Chapter 13
Chapter 13
mutanen Gidanmu akan halin dana ke ciki, Cikin sauri suka shigo dakin, Dukkansu sun firgita da halin da suka tsince ni a ciki, na yi kokari da taimakon Abasu kala na cire doguwar rigan dake jikina, Cire rigan keda wuya sai naji mutanen da suka shigo dakin suna salati suna salallami , Ban san akan me suke salatin ba amma tunanina yabani kodai suna mamakin yadda akayi har naji wannan babban rauni ne, "Shuraihu wayannan tabon da suke bayanka na menene, yaya akayi har kaji wayannan tabobin??" Na tsinkayi muryan mahaifiyana tana tambayana , Salati nayi kafin mahangar tunanina ya hango mani ta yadda akayi har na samu wayannan tabon, Alokacin da tsoho zaikid yake koya mani fada yakan ji mani rauni a jikina, "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" na fada a fili Mafarki na neman ya zama gaskiya akaina Abun daya faru dani a mafarki na farka na ganshi a jikina, Anya kuwa wannan mafarkine, tun da nake a rayuwata ban taba jin wani labari makamanciyar nawa ba, wai ace kayi mafarki kaji rauni, kuma ka farka ka ganka dauke da raunin, Anya mafarkine nayi kuwa,???? . Tambaya Mafarkine ko Gaske . Rayuwa haka take wakana yau lafiya gobe akasinta, dazu-dazu lafiya yanzu-yanzu rashinta Allah ka baiwa dukkan musulmi marasa lafiya masu lafiya kuwa Allah ka kara masu ,,,, Its 99% awakening from three 3 days sickness BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 12 . ........ Bayan Wata Uku * "Shuraih!! Shuraih!!! Ka tashi dare yayi fa" Na tsinkayi muryan abokina Abdulhamid a cikin kunnuwana, Na mike cikin magagin bacci nace "karfe nawa yanzu" "Goma da rabi ne yanzu" Ya bani amsa Da saauri na mike tsaye, cikin kankanin lokaci na wartsake daga magagin baccin dake dibana, Na zuri takalmina na fice daga dakin Abdulhamid ya bini da gudu yana mai kiran sunana, "Shuraih ka tsaya mana baka ga garin akwai hadari bane, kuma kafin ka kai gida ruwa ya tsinke," Na danyi nazari kadan kafin na jijjiga kaina nace "Ai gwara ruwan ya tareni a hanya akan na tsaya har shabiyun dare yai mun anan angwan naku" "Toh Allah ya kiyaye hanya" "Ameen " nace sannan na cigaba da tafiyana , Darene mai dauke nannauyan hadari wanda akowani lokaci ruwan dake tattare dashi na iya zubowa, in banda hayaniyan mutani, da karan wucewan iska, babu abunda kake ji a angwan, Karar aradu ne ya ziyarci kunnuwana wanda hakan ya sanya na kwararo addu'o'i , Ina tafiyanne sauri sauri gudu gudu, na matsu na ganni a kofan gidanmu, sabida bana son wannan ruwa ya riskeni akan hanya, duba ga yadda naga ban dade da dawowa daga asibiti ba, ' Tunanin abubuwan da suka faru a baya ne suka fara dawo min cikin kwalkwata tamkar a majigi (video), nayi murmushi a sa'an da hoton surar haseena suka baiyana cikin kwalkwata, Yau watanni uku kenan, tun bayan lokacin dana hadu da haseena a cikin wata rayuwa wadda na kira da mafarki, hakan ya janyo mani abubuwa da yawa, ciki kuwa har da daukana da akai a matsayin mahaukaci, sakamakon labarin dana sanar ma iyayena, Wannan yasa suka tarkatani sukai asibitin kwalkwalwa dani, watanni na uku acan ina karban magani da Allurai, babu yadda banyi ba dun na ganar da iyayena cewa ina cikin hankalina amma abu ya faskara, , A shekaran jiya ne aka sallamoni daga asibitin kwalkwalwa, Na saki murmushin kuna lokacin dana tuna wanda ya makala mani hauka, "Shuraih anya kana cikin hankalinka kuwa, taya za'a yi wannan abu ya faru a rayuwan zaahiri,sai kace wani wasan kwaikwayo (film)" Na tuna lokacin da mujahid ke fadin haka a gaban iyayena yayin dana basu labarin duk abunda ya faru dani da yadda akayi har naji ciwo a dantsena "Da gaske nake wallahi babu karya a cikin labarin dana baku" nafada ina kokarin baiyana masu gaskiyana "Baba ya kamata mukaisa asibitin kwalkwalwa su dubasa bana tunanin yana cikin hayyacinsa" Mujahid ya fadi yana duban mahaifina "Toh naji amma kafinnan bari mudan fara dana gargajiya tukun,ko ya kuka gani" mahaifina ya fadi yana dubansu , In gajarce maku sanda aka gaiyato malamai sunkai Goma sukai saukan qur'ani a gidanmu, maganin gargajiya kuwa babu iriyar wacce ba'a dankara mani ba, tun ina bi a hankali inayi masu bayanin cewa nifa lafiyana kalau, har takai sun tunzurani wata rana na kama wani mai magani da aka kawosa wai ya bani magani na lakada masa dukan tsiya, , Toh a sannan ne aka wuce dani asibitin kwalkwalwa, ko kuma ince asibitin mahaukata ,,, Barkewan da ruwaan saman yayi tamkar da bakin kwarya shi ya sanya na fara gudu, ina neman mafaka, cikin wani lungu nake wanda ma ban gama sanin hanyan ba, , Gani da nayi ruwan na neman ya kara karfi bisa kan na da, ya sa na fara tikan gudu, banyi nisa da gudun ba Ruwan saman ya fara saukowa da karfi, , Nayi tunanin muddin na cigaba da tafiya cikin ruwannan zan iya kamuwa da mura, ko zazzabi Sai a sannan nayi dana sanin zuwana angwan Tofa wajen Abdulhamid, , Na fara waige waige ko zanga wani mafaka don in samu in fake har sai an iddar da ruwan , sannan inyi tafiyata , Wani Zaure na hango daga nisa kadan da ni, Batare da na tsaya yanke wani shawara ba na afka cikin zauren da gudu, Shakka babu da nasan abun da zai biyo bayan shigana cikin zauren da banyi, kwadayin shiga ba Shakka babu da nasan cewa shiga na cikin zauren zai tono wani babban rauni a zuciyata ya kuma sake bude wani sabon babin Rayuwan mafarki a rayuwata, da banyi gangancin shiga ba , Ina tsaye a cikin zauren yayin da ruwa keta kwarowa a waje,sautin karan zuban ruwa a rufin gidajen jama'a shi kadai ne abun da jama'a ke iya saurara, , Zauren yana hadene da Gida saide kofan gidan a kulle yake ta ciki saboda yadda naga babu kwado a jikin kofan, , Na dau lokaci a tsaye a cikin zauren, yanzu kam an dan sarara da ruwan, sai de dan yayyafi da ake yi, wannan yasa na fara himman wucewa gida, Har na yuunkura da niyyar in mike daga tsugunon danayi, sai naji ana kiciniyar bude kofan Gidan , Na tattara hankalina gaba daya ga kofan don ganin wanda zai fito, Duk da darene amma ina ganin komai shar shar da taimakon hasken farin watan daya ke sararin sama , Kofan gidan ya bbude a lokaci daya, dishi dishin mutum idanuwana suka fara hangowa saide ban iya banbance namiji ne ko mace ba, Mutum din ya nufoni wannan karon kuwa na gane cewa macece, duba da yadda naga tana tafiya, da kuma yanayin surar jikinta, Sai da tazo daf dani sannan Numfashina ya tsaya cak, kwalkwata ta tafi hutun rabin lokaci Zuciyata ta dawo bugawa sau hudu a second daya,miyaun bakina ya kafe, da kyar na samu na sassaita kaina, Cikin dakewa na lalubo harshena na furta "BUDURWAN SIRRI" a rude na furta kalman , Tana tsaye a gabana, kamar yadda nasanta komai nata nanan, babu wani canji daya ziyarceta, Kayan dake jikinta sun jike da ruwa kuma bata sanye da hijab, hakan ya taimaka wajen baiyano da kiran jikinta, , Wani kallo
Table of Contents