Chapter 1
Chapter 1
BUDURWAN SIRRI Littafin Shuraih Usman l Page 1 . Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin na batare da iznin wannan shafi ba . Na fito daga gida ina sauri zan karasa wajen wani abokina domin na karbi wayata , nan na tsaya a bakin hanya ina neman lift, ban dade da tsayawa ba kuwa na samu wani dan anguwarmu yazo wucewa na tsayar da shi . "Abasu kala, dan Allah kabani wayana mana ya kanamin irin haka ne kaifa kasan in babu wannan waya toh fa abubuwa da yawa zasu rikirkice domin kuwa akwai document dina da yawa aciki . Kuma mutae da yawa suna jirana" Na fada a lokacin dana ke tsaye a shagon su umar shagon hada takalmane wanda wani dan cirani yazo ya bude cikin ikon Allah sai kuwa jama'a sukai ta saka yaransu cikin wannan shagon har takai yanzu wannan shago ta shahara wajen hada takalma . Umar wanda fuskarsa ya baci da dusar takalmi ya dubeni yace cikin muryar wasa " 99% wallahi wayanka tana gida , kuma yanzu dai kaga ina gugan takalma ne , babu yadda zanyi na saki gugan nan na je gida yanzu" . Kwafa kawai nayi cikin bacin rai na fice daga shagon sannan nayi natafiyata , don kuwa ba karamin haushi yabani ba, Nan na tuna yadda ya dauki wayar ina barci da safe , inda idanuwana biyu ne a lokacin toh da babu abunda zaisa na barshi ya dauki wayar . Gida na nufa cikin takaici da jimamin wannan abu da umar yayi mani, kamar daga sama sai naji wata zazzakan murya tana kiran sunana "Shuraih shuraih!! Shuraih!!!" . Cikin sauri na juyo don naga wacce take kirana amma cikin mamaki da zunzurutun al'ajabi sai banga kowa ba hakan ba karamin kidimani yayi ba amma sai na dauka tamkar kunnena ke yaudarana . Hakan na cigaba da tafiya ina isowa gida na wuce zuwa daki na , ina shiga naje na kwanta don kuwa yanzu lokacin hutu ne babu abun da nakeyi agida hakan yasa na ke dan rubutu da gajerun labarai na littatafan hausa na ringa post na su a social media, . Toh gashi dan iskannan ya dauke wayar kuma ya hanani,sai yawo da hankali yake yimini,kwanciya nayi bisa wata lallausar kujera dake girke a dakina, nan na kumshe idanuwa na domin kuwa barci nake bukata da nayi . . . . . . . . "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UNN" Na fada alokacin dana farka na tsinci kaina cikin dokar daji babu gida baya babu gida gaba, . Na mike tsaye cikin tu'ajjibin wannan lamari ina mai tsananin mamaki da Al'ajabi don a tunani na ma mutuwa nayi, . Toh amma da mutuwa nayi ai dole, naga mala'iku hakan ya tabbatar mani. Ba mutuwa nayi ba , . Tayaya ni da na kwanta acikin dakina bisa kan shimfidata sannan na farka na ganni cikin dokar daji ai dole wannan abu ya rikita ni, . Babu abunda ya sake rikitani game da wannan daji face gani danayi wannan dajin sam bai yi kama da irin dajin dana saba gani ba, Don kuwa yanayin irin wannan daji a talabijin na saba gani cikin finanan kasashen waje . Ni shuraihu inkiya 99% sai dana firgita ainun da yanayin wannan daji na nemi waje na zauna ina ta tunani kala kala acikin zuciyata, can sai nayi karfin hali na tashi na tunkari gabas donni a tunanina, wai kodai barayi suka shigo gidanmu suka kamani suka zo suka ajjiye anan, . Sai wata zuciyar tace dani yo imma barayinne suka kama ni mene ne dalilin da yasanya suka kawoni wannan waje, nan dai na cigaba da tafiya ina ganin ababen mamaki, dogayen bishiyoyine suka cika wannan daji bishiyoyin kuma zaka gansu sai kamshi suke tamkar itatunan sandal, . Su kansu ganyayen wannan bishiyoyin korayene ababen sha'awa, sannan kasan wannan daji wasu irin ciyayi ne wayanda ban taba ganinsu ba , su wayannan ciyayi sun kasance jajaye, kuma koda na taka su sun durkushe take zasu sake dagowa . Koda na kara gaba sai na hadu da wani abun mamaki wanda yai matukar tayarmun da hankali Ba komaine na gani ba illa wata korama, wadda ruwanta yake zubowa daga saman wani katon dutse , shi wannan korama ruwansa garai garai ne dun kuwa koda na matso kusa da ruwan sai na ga hoton fuskata ya bayyana acikin ruwan tamkar an dauki hotona ne aka manna ajikin ruwan . Tsaban tashin hankalin dana tsinci akaina aciki a wannan lokacin yasa na kurma ihu, domin kuwa dauka nayi ko mafarki nake hakan yasa na cizi hannuna, a bisa mamaki sai naji zafi ya ziyarci hannanuna hakan ya tabbatar mani da cewa ba mafarki nake ba . Irin wannan koramar sam babu shi a kasar hausa, kuma na riga dana san a irin garuruwan da ake samun wayannan koramun, don kuwa na kanga hotunansu a jikin gorunan swan water da talabijin . Motsi naji daga bayana hakan ya tabbatar mani da a akwai wani halitta a bayana koda na waiga sai naga daga cikin wani surkukin ciyayi mitsin yake fitowa, nadai takure na matse sannan nayi na maza na daure don ganin mene ne ya ke fitowan . Abubuwan dana ga suna fitowa daga cikin wannan surkuki su suka saka naji cikina ya tsure, idan da ba dun ina da karfin haliba toh da babu abunda zai hana ban saki gudawa a wandona ba, amma duk da haka sai dana tsiyayo fitsari wanda ni ban ma san na tsiyayo ba . . Kai friends ku taimaka ina cikin firgici Shin ko kunsan mena gani alokacin toh ku jirani sati mai zuwa a cigaban wannan labari wanda zai runga zuwa maku duk sati Ranar Asabar da safe tare dani Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% . Wannan kirkirarren labarine daga 99% Ku tsumayeni a page 2 Daga:- hausaebooks wepsite Da keffians News Teller BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 2 . Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin na batare da iznin wannan shafi ba . Ba komai nagani ba face namun daji danginsu su Alfadari, Giwa, barewa,Zaki,maciji,damisa,kura kai duk dai wani dabba da kuka san yana rayuwa acikin daji, cikin gungunsu suka nufo ni ai koda ganin haka sai na juya da nufin na fada cikin wannan kogi dayake gabana . Amma me zan gani wasu kyawawan kananan kifaye na gani masu zakwa zakwan hakora lokaci lokaci zakaga suna kikkirta hakwaransu, abun yabani mamaki wai ace kifaye da hakwara amma sai na tuna wani american film din dana kalla mai suna PIRANHA . Koda naga haka sai nayi wani gefe da gudu don na tsere ma wayannan dabbobi da suka biyo ni da mugun nufi, gudu nake iya karfina don na ceci rayuwata daga hannanun wayannan dabbobin sai dana kai wajen mintin arba'in ina tsala gudu acikin wannan jeji amma wayannan dabbobin sai bina suke duk inda na shige, abunda zai baka mamaki da wayannan dabbobin shine . Su ba gudu suke ba don kuwa tafiya suke amma yadda kasan suna gudu
Table of Contents