Chapter 7
Chapter 7
itace aka sana'anta shi, bakin bukkar muka tsaya sannan haseena tai sallama, wata tsakurarriyar muryace ta amsa sallamar, daga bisani sai wani dattijon Aljani ya fito daga bukkar yana sanye da dogon yar shara har kasa sam sam fuskarsa bata nuna alamar tsufa ba ,zai yin kama da saurayi mai jini a jika Har kasa ya zube yayi gaisuwa wajen haseena ta durkusa ta dagoshi tace "baba zaikid nasan dai basai na maka bayanin abunda ya kawoni wajenka ba, amma duk da haka zan sake maimaitawa, wannan shine Mijin nawa In Allah ya yarda ina so a cire masa dukkan wani tsoro na jinsun mu kuma ka koya masa dukkan wasu dabaru da salon yaki, nan da wata daya zan dawo na daukeshi" Murmushi tsoho zaikid yayi "an gama ranki shi dade" Ni dai na cika da mamaki ainun jin cewa wai ni za a cire ma tsoro sannan kuma wai za a koya min yaki da dabarun fada Haseena ta dubeni a lokacin da fuskarta ....... Kwana biyu kun jini shiru Bani da lafiya ne shi isa BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 7 . Haseena ta dubeni a lokacin da yanayin fuskarta ya sauya , ta kankame hannuna sosai tace" shuraih muddin muna son mu rayu har abada amatsayin mata da miji toh dolene ka koyi wasu abubuwa na yaki, da kuma ka kuma cire tsoro a zuciyarka, ina matukar sonka irin son da baki ba zai iya fasaltashi ba, hannu ba zai iya rubutashi ba ko na dakika daya bana son rabuwa dakai, amma dole na na barka anan domin ka koyi yadda zaka kare kanka daga sharrin Salman" . Har na budi baki zanyi magana sai ta sanya yatsanta a akan lebena alamar nayi shiru ba musu nayi shirun duk da irin tarin tambayoyin dana ke shirin jefamata Ta dan ja baya kadan sannan ta soma tafiya har tayi nisa idanunawana suna kanta ta juyo muka hada idanu ta sakarmin murmushi daga haka ta cigaba da tafiyarta har ta bacemin da gani ina nan tsaye a gun . Tsono zaikid ya dubeni da kyau yace "yaro shin meye sunanka" "Shuraih" na bashi amsa batare dana kallesa ba haryanzu idanuwana na kan hanyar da haseena ta bi Tsoho zaikid ya sha gabana sannan ya turbune fuska yace "shuraih kake ko wa to bari kaji Abunda kazo yi nan shi za kamai da hankalinka gareshi , domin kuwa in kai wasa toh kana ji kana gani ta rabu da kai kenan" Sosai hankalina ya tashi da maganganun wannan tsohon Batare daya jira amsana ba ya juya ya shige cikin bukkarsa yana cemin" ka dai shirya don kuwa daga gobe zamu fara atisaye " .... Har magriba ta gabato banga alamar tsohon nan zai fito ba hakan ya sani ta shi na kwankwasa kofan bukkar daga ciki muryan tsohon naji yace "ya akayi ne" "Yun wa nake ji ,kuma gashi dare ya fara yi baka bani makwanci ba" na fada Sautin dariyarsa naji alamar dariya yakeyi "In tambayeka mana" ya fada "Ina jinka "na bashi amsa "A rana sau nawa kake cin abunci" "Sau uku" "Toh daga yau ka sanya a ranka kuma a jikinka baza ka sake cin abinci ba sai bayan kwana daya,kuma ka sani baka da abunci sai yayan itace" Sosai na girgiza da jin batun tsohonnan "To shi kuma makwanci fa" "A nan zaka runga kwana kuma ka tabbata asubar fari ka farka yanzu dai ga ruwa kayi alwala kai sallah," ya jefo min wani batta na ruwa Na karba nai alwala nai sallah daga nan na zube wajen durkushe duk da yanayin wajen yana da kyau kuma ko kadan babu kwari ko wasu muggan dabbobi masu cutarwa a cikin dajin domin kuwa tunda muka shigo dajin kawo izuwa yanzu bamuyi gamo da wani abu mai rai ba . Haka na kwanta akasa kan ciyayin dajin masu tsananin laushi duk da ya kasance ina rawar dari saboda sanyi da nake ji, bai hana bacci daukata Ba . A fiirgice na farka sakamakon jin an kwara min ruwa da nayi waige waige na fara yi don ganin mahalukin daya kwara min ruwa dan tsakurkurin tsohon ne dai a gabana ya bata rai yana rike da wasu mayan mangala guda biyu Ya ce"shin jiya ban sanar dakai cewa asuban farko taimaka a farke ba, shine ka shagala har asuba ta biyu baka tashi ba" Bai jira cewana ba ya jefo mani mangalolin nan masu dan karen nauyi da kyar na iya cafe guda daga cikinsu Yacigaba "maza maza ka tashi ka tafi wancan kogin yai nuni da hannunsa zuwa wani gefe dabam, ka debo ruwa ka runga zubawa anan ya nuna mani wata katuwar rijiya wadda tun zuwana wajen ban lura da ita ba . A kasale na tashi na rarumi mangalalolin na nufi inda ya nuna mani nayi tafiya mai dan karen nisa kafin na iso bakin koramar na zauna kan daya daga cikin mangalolin nan ina hutawa bayan nagama hutun ne na cika mangala daya da ruwa sannan na kinkimeta da kyar da sidin goshi na dorata akaina irin nauyin danaji akaina yafi kama da na Mota ko wani katon dutse a daddafe da kuma ikon Allah har nakai bakin rijiyar na zuba ruwan na sake komawa rafin kai in takaice maku sai wajejen la'asar na idda kai ashirin din daya ce na zuba, na samu waje na baje a kasa ina numfashi sama sama alamar na jikkata naji karar budewan bukkar tsohon ya zo ya tsaya daidai gabana sannan ya bushe da dariya yace "kai amma bil'adama da ragwanta suke yanzu wai dan wannan aikin shine har da numfarfashi sai kace wanda yai aikin azo a gani, maza ka mike tsaye" A daddafe na mike tsaye don kuwa tun da nake a rayuwata ban taba yin wani aiki mai wahala daya kai wannan ba . Yanzu kam da sauki tunda dai na dan rage nishin da nake tsoho zaikid ya shige cikin bukkarsa yadan dau lokaci kafin ya fito rike da sanduna guda biyu, sandunan dogayene sosai don kuwa sunyi tsayina biyu Ya jefo mani guda daya duk yanda naso na cafe ta amma na gagara saboda irin saurin zuwan da tayi sai gashi sandan ta wuce ni tamkar walkiya , ta sauka nisa dani tsoho zaikid yayi murmushi " Maza kaje ka daukota" Ba musu na nufi wajen da sandar take ina zuwa na sanya hannuna da nufin na rabata da kasa amma sai wani nauyi ya ziyarci hannuna ji nai tamkar na ina kokarin daga katon dutsene na daddage na tara karfina har ina nishi na daga sandan daga kasa na kafata tsaye , sai nishi nake haka na fara jan sandan a kasa har na kawota wajen tsoho zaikid, "Da alama wannan tayi ma nauyi toh bani ita ka amshi tawa" Ya karfi wannan daya bani ya kuma mika mani nashi da sauri na karfa don dama ni nasan kuskure yayi wanda ya kamata ya bani shike hannunsa , ai mugun nauyin danaji shi yasa na saki sandar ta fadi a kasa don kuwa hartafi waccan dinma nauyi tsoho zaikid yai kasake yana kallona kafin yace "muddin zaka runga yimasu irin wannan daukan toh baza ka taba iya
Table of Contents