Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Budurwar Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,187 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rike koda daya daga cikinsu ba" "Yaya kake so na dauka toh" "Kasanya a ranka cewa zaka iya , sannan kana nan ne kawai don BUDURWAN SIRRI, haka kuma ka cire tunanin duniyarku daga ranka ka dauka tamkar a gidanka kake, sannan ka tausasa zuciyarka, a natse zaka ji mamaki ainun don kuwa ba wannan sandan ba hatta wancan tsaunin zaka iya yin gamo a dora maka shi" Nai kasake ina kallonsa yayin da na kalli tsaunin daya ke nuna mani a zuciyana nace "toh ko nine ILYA DAN MAI KARFI sai haka" . Na nufi sandan nayi tamkar yadda yafada na rufe idanuwana na shafi sandan da hannuna na kama na daga cikin matukar mamaki sai naji tamkar na dau fallen takarda don kuwa ko kadan sandan bata da nauyi yanzu na juya na dube shi yai mani murmushi yace "shin yanzu ka yarda da magana ta" "Shakka babu na yarda" Daga nan ya fuskanceni yace "daga yau zamu fara darasin mu na koyan fada , da kuma yadda zaka kare kanka, . Ya koyar dani abubuwa da dama a wannan rana don kuwa in ba sallah ba babu abunda yake tsaida mu, da shike ina da saurin daukan abubuwa , har magariba tayi ya ce mani "je kai sallah ka kwanta kuma gobe ka tabbatar kafin safiya ka gama diba ruwanka nai godiya sannan nai wucewata izuwa inda na kwanta jiya ******* Kwanaki suna ta wucewa tamkar yadda takarda ke zukar ruwan biro yau saura kwana daya wata daya ta cika, A cikin wayannan kwanakin na koyi a bubuwa da dama, dun kuwa ji nake babu wanda ba zan iya tunkara ba yanzu batun tsoro kuwa babu ita , Tunda kuwa ni da kaina nake fada da manyan zakuna da kadoji kuma na kai su kar . Shi kansa tsoho zaikid yana mamaki ainun da saurin daukan fada na, kaman kullum yauma muna filin koyon fadanmu ni da tsoho zaikid sai fafatawa muke in ka ganmu a lokacin sai ka rantse wasu a bokan gaba ne domin kuwa kowannenmu burinsa shine yaga ya cutar da dan uwansa, ni dai na dage sai kare hare haren tsoho zaikid nake wanda shi kuma ya kufula ainun ganin sam bana kawo hari, sai da muka shafe wasu sa'o'I kafin ya samu nasarar buguna da sanda akafa nan take kafana ta gurde amma saboda juriya irin nawa sai na dake na kama kafar na murda ta sai ta dawo dai,a lokacinne na fusata na fara kaimai hari ba kakkautawa kan kace kwabo sai ga tsoho zaikid a kasa wanwar sakamakon bugunsa da nayi da sanda akansa . A gigice na nufeshi na tallabo kansa ina mai bashi hakuri yayi murmushi sannan yace "lallai na yarda yanzu kam ka kawo karfi ina son ka shiryaa don kuwa gobe BUDURWaN SIRRI zata zo ta dauke ka" Na gyada mai kai ina susa keyana ******* Washe gari tunda sassafe na iddar da debo ruwana don kuwa yanzu ji naake tamkar zan iya diba kai dubu ma, Nai sallah sannan na taho kofan bukkan tsoho zaikid na tsaya ina nan tsaye a wajen har gari ya waye, Tsoho zaikid ya fito daga bukkar hannunsa rike da sanda guda, na dubesa da mamaki don kuwa a kullum da sanduna biyu yake fitowa ya zauna kusa dani yace "shuraih ka tashi lafiya" "Lafiya lau" Daga haka ban sake magana ba Kaman a mafarki sai naji muryan haseena tana gaida tsoho zaikid na dago kai na dubeta da mamaki don kuwa shi kansa zaikid bai san lokacin da ta zo ba iyaka dai jin muryanta yai har kasa ya rissina ya gaiisheta sannan ya nuna ni da hannu yace "ranki shi dade yanzu matsoraci kuma ragon bakon ki ya juya izuwa jarumin saudauki wanda sam baya jin tsoron komai gaba dayan tsoronsa sun juya izuwa naciya da juriya" Tai murmushi wanda ya sake fitta kyawunta ta matso kusa dani ta kama hannuna da mamaki sai naga hawaye akan idanunta "Shuraih kayi hakri nasan cewa na cuci rayuwarka na sanyaka a kunci sakamakon son zuciya da sonkaina, kana zaman zamanka a duniyarku na daukoka na kawo ka nan gashi yau a kaina ka...." Na yi sauri na dora hannuna na rufe mata baki sannan nace "yana daga cikin rukunan imani yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, wannan mukaddari ne bayin ki bane kuma ki sani muddin ina numfashi a doron kasa ba makawa sai na aureki bana tsoron mutum bare Aljan, ni kawai abunda nake bukata dake yanzu shine mu tafi izuwa filin wannan gasa domin na nuna ma salman cewa DAN ADAM HATSABIBI NE, Babu abunda baya sarrafawa komai girmanta koya takai da cutarwa" ********* Zaune naake bisa wata lallausan kujera yayinda haseena take fuskanta ta Kura mani idanu tayi bata ko kiftawa nim dai idanuwana akan nata suke, cikin kwayan idanunta babu digon baki sai wani digon jaja ja, haka nan naji ina matukar farin ciki tun ma bamuyi gasan ba Tace "shurai nasan cewa kana da tarin tambayoyin da kake son kai mani musamman ma akan wannan suna daka ji ana kirana wato BUDURWAN SIRRI, toh yau zan baka amsar dukkan tambayoyinka . Toh fa Nasan ku kanku kuna son jin labarin budurwan sirri kui kasake da kunnuwanku BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 8 . "shurai nasan cewa kana da tarin tambayoyin da kake son kai mani musamman ma akan wannan suna daka ji ana kirana wato BUDURWAN SIRRI, toh yau zan baka amsar dukkan tambayoyinka" Nai murmushi "ni tambayata guda ce itace wannan suna dana ji ana kiran ki da ita BUDURWAN SIRRI, shin meye ma'anarta" , Haseena tai murmushi sa'annan tace "kaman yadda na baka labari a baya cewa mahaifina acan duniyarku yai aure kuma bil adama ya aura, nasan cewa kana mamaki inda har Aljani ya auri Bil'adama toh kama daina don kuwa jinsi ne kadai ba daya ba, domin kuwa a zamanin da Aljanu da yawa sun auri bil'adama haka suma Bil'adama da dama sun auri Aljanu sannan suka hayayyafa, Hakance ta kasance da mahaifina bayan an haifeni na kasance kyakkyawa wacce babu kamarta a duk fadin wannan duniya tamu , hakan yasa yayan saraku da Attajirai sukai ca akaina kowannensu yana so aureni ni kuma duk cikinsu babu wanda ya kwanta min arai hakan ce tasanya na ki amince masu, A kudancin duniyarmu a akwai wata babbar birni na Aljanu ana kiranta da BULZUM sai de su Aljanun sun kasance kafirai ne kuma matsafa, sarkin birnin azzalumine sunansa RAVA yana da 'da daya tilo daya haifa mai suna bishmalu, sarki rava yana son bishmalu sosai hakan ce tasa duk wata bukata da bishmalu ya nema duk wahalarta duk tsaurinta sai sarki rava ya biya masa ita wannan tasa shima bishmalu yake son mahaifin nasa sosai, Bansan tayadda akayi har bishmalu yaga fuskata ba, sai ganin dan aiken sarki rava mukayi yazo har fada da mummunar wasika wasikan da ta zama sanadiyan mutuwan rabin Aljanun wannan gari namu, "tana zuwa daidai nan ta fashe da kuka Banyi yunkurin hanata kukan ba cikin sheshsheka ta cigaba "mahaifina ya karbi wasikan ya bude shakka babu daya san abunda yake cikin wasikan nan toh da bazai bude ba, yana budewa

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});