Chapter 14
Chapter 14
ta makamin mai taken daga ina kake????? ,,,, Kai fans anya ba mafarkin na sake yi ba BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 13 . "Malam daga ina ??" Ta harbeni da tammbaya fuskarta na nuna alamun bata taba ganina ba, , Karin mamaki ne ya mamayeni a sa'ilin data jefo mani wannan tambayar, , Maimakon na bata amsar tambayarta Sai natsaya ina kallonta kawai, kafin daga bisani na furta "Haseena shin baki gane ni ba"? , "To ta yaya kuwa za'ayi na gane ka, wai shin ma a ina na sanka, da har zan ganeka, naji ma har sunana ka sani?a ina kasan sunana" Bakinta kawai nake kallo yayinda take maganar sam na manta da duk wani kalubale na rayuwa dayake shirin tunkarata a sanadin wannan yarinyar, na manta irin tarin wahalan da nasha don kawai naga na mallaki budurwan sirri, , Karar tafin hannunta sune suka dawo dani cikin hayyacina , Kamar wanda ya farka daga barci, na girgiza kai ina mai cewa "Sam haseena bai kamata ace kin manta da wanda yake shirin sadaukar da rayuwarsa akan ki ba,kece..." Magana ta ya katse a lokacin da gaba dayan cikin zauren ya gauraye da hasken wutan NEPA, Kunnuwana suka daukomani muryan yara suna cewa NEPA, Minal jinnati wannas, abun danake furtawa cikin zuciyata kenan, kafin na furta "tabarakallahu ahsanul khaliqeen" , Duk ganin dana kewa haseena ban taba yi mata kallo irin na yau ba, ayau ne nasan cewa haseena tauraruwar matace, Na lura da yadda jikinta yayi sanyi ba kaman da ba, lokaci daya dukkan wani tsiwanta suka lafa, ita kanta ta zargu da irin kallon dana ke mata, Daga kai tayi sama, alaman tana son ta tuno da wani abu, Ihu mai karfi ta saki sa'annan ta sulale a kasa sumammiya, , Hankalina ya tashi da sauri na fadi a kasa kusa da ita ina mai tallabo kanta hade da kiran sunanta Da karfi nake kiran sunan nata, Karar bangaje kofa naji daga bayana da sauri na duba gefen da naji karar , Wata tsohuwace naga ta nufoni da gudunta, kallo daya nai wa tsohuwar na ga suna dan kaman ceceniya da haseena Tsohuwar wacce ban san ko wacece ita ba tana isowa ta kama hannun haseena kodubana batai ba, ta tallafo wuyanta da kafafunta ta daga ta sama cak, tayi cikin gidan da ita, , Tarin mamakinn da wannan al'amari ya bani shi ya sanya na fara jin jiri na dibana, don babu ta yadda za'ayi yar fingilar tsohuwar nan ta iya ciccibar budurwar mace kamar haseena, Na tabbata ko kosasshen akuya wannan tsohuwar ba zata iya dauka ba amma sai gashi ta ciccibi budurwa . Na yunkura da nufin na tashi nima nabi bayan tsohuwar cikin gidan, Toh alokacinne wani babban al'amari ya afku al'amarin daya sanya ni farinciki gaya, , Yun kura wata keda wuya na dumfari kofar shiga cikin gidan, Batare da wani shakku ko fargaba ba na bangaje kofan da kafata sannan na antaya ciki, 'Lahaula wala kuwwata illa billahil azizul hakeem" Na fada a bayyane yayin da idanuwana sukai arba da abunda ya kusan zautani, Shakka babu yanzu kam na yadda cewa Rayuwata a cikin mafarki gaskiyane, labarin budurwan sirri ma gaskiyane, sai de kuma kar ya kasance shima wannan karon mafarkin nakeyi, Tsintar kaina nayi cikin dajin da aka koya mani fada, a gaban bukkar tsoho zaikid, Nadai daure na isa gaban bukkan koda na tabbata bukkarne sai na nufi cikinta sai de tun kafin na kai ga shiga, naga ana kokarin futowa daaga cikin bukkar Tsoho zaikid ne ya fito fuskarsa tana mai yimani murmushi, abayan tsoho zaikid wannan tsohuwarce data dauki haseena Na saki baki cikin firgici ina kallonsu, anan take na fara tunanin shikenan na sake jefa kaina gidan jiya, "Dan saurayi Shuraihu! Taho ka zauna ba mafarki kake ba " Muryan tsoho zaikid ne ya ankarar dani daga dogon tunanin da na fada Ba musu kuwa na zo na zauna agabansu yadda kasan wani mai daukan darasi, su kuma suna zaune akan wata itace, Tsohuwar nan ta bude baki ta fara magana "Yaro hakika mun yarda da soyayyarka ga haseena, duk munga irin halin daka shiga sakamakon ta, shakka babu ka cancanci auran budurwan sirri," Tacigaba bayan taja gauron numfashi "Kai sani cewa Haseena ita kadai ce ta tsira da rayuwarta a yayin da ka dasa makaminnan, a garin bulzum ita kanta haseena abu daya ne ya taimaketa, Ta kasance a cikin kwayoyin halittar jikinta , rabin kwayoyin halittar na Aljanu ne rabi kuma na Bil'adama ne, Toh a yayin da wannan makami ya fashe, sai ya kasance kwayoyin jikinta na Aljanu sun mutu, da shike ALlah yasa tana da sauran kwana sai kwayoyin bil'adama suka maye gurbin wajen kwayoyin halittan, Yanzu kam haseena ta zamo bil'adama sak irinka Hakan ne ma yasa Zaikid ya dauketa daga duniyar nan ya kaita duniyarku ta bil'adama domin ta samu kyakyawawan kulawa," , Bakina bude nake dubansu na kasa bambance shin farin ciki zanyi na kasancewar haseena a matsayin bil'adama ko kuma bakin ciki zanyi na komo wata duniyar da babu Bil'adama, , Tsoho zaikid yayi murmushi a karo na farko yace "ina sane na sanar dakai cewa haseena ta halaka, na kuma koma da kai izuwa duniyarku, saide yanzu da kwai matsala daya" "Wata matsala kenan" Na tambaya Tsoho zaikid yace "matsalar shine haseena ta manta dukkan wani abun daya faru da ita lokacin da take duniyar nan, shi yasa ma da kuka hadu kaga bata shaida ka ba" , "Amma mai yasata faduwa dazunnan" Na tambaya ina kallon tsohuwar nan "Dogon tunani ko kuma son tunano abun daya faru lokkacin daya wuce" , "Ban fahimta ba" "Aduk lokacin da haseena tayi yunkurin tunano rayuwarta na baya toh hakane zai runga afkuwa da ita, zata iya Suma, izan kuma abun ya yawaita zai iya shafan lafiyanta, sai ka kiyayi yi mata duk wani abun da zai sanya tayi kokarin tunano rayuwarta na baya" Tsoho zaikid ya bani amsa Tsohuwar nan ta dubeni da kyau tace "Nasan kana tunanin koni wacece? Toh nice kakar haseena, dun kuwa ni na haifi mahaifiyarta Kafin Nuridden ya aureta alokacin mahaifinta ya rasu, kuma ni bansan cewa nuriddeen Aljani bane, har ya auri yata, suka samu karuwa da juna biyu, saide a yayin haihuwar yata ta koma ga mahaliccinta, Tun daga wannan lokaci ban sake ganin nuriddeen ba bare har na gana da haseena, sai a kwanakin baya wannan aljanin ya kawota wajena ina ganinta na ga fuskar yata a tattare da ita , shine yayi mani bayanin dukkan abun da ya faru " Ta karisa zancen tana mai duban tsoho zaikid 'Baba yanzu a ina haseenan take" 'Tana cikin bukkata" , Na mike tsaye na dumfari bukkar wacce tun dana fara zuwa Dajin har wa yau ban taba shiga ciki ba , Batarre da fargabar komai ba na tura kai cikin bukkar Yadda nai tsammani hakan take babu komai cikin bukkar sai wata tabarmar karau, sai wasu tarin tarkace a wani saqo, Idanuwana suka kai ga inda haseena take kwance a saman tabarmar karau dinnan tana barci , Kallonta nake bana ko kiftawa har na kariso inda take nakai hannu da zummar na taba saman goshinta cikin mamaki
Table of Contents