Chapter 3
Chapter 3
sai naga tama fi kyawu bisa kan da, . Koda taga halinda na shiga adalilin wannan murmushinn da tayi sai ta kyalkyale da dariya, ai saboda dadin sautin wannan dariya nata ban san lokacin dana sulale a kasa sumamme ba, Iya abin da masarrafin kwalkwata ya iya dauka shine daukewar dariyar wannan budurwa daga nan kuma ban sake sanin meke faruwa ba *** . A hankali nafara bude idanuwana, mutane ne nafara ganinsu dishi dishi akaina, na mike na zauna sai a sannan ne kwalkwalwata ta dawo aiki hankalina ya dawo jikina . Na dubi mutanen da suke gefena suna yimini sannu, sai naga ashe ma yan mata ne kyawawa, sanye da fararen dogayen kaya, sai a sannan na lura da dakin danake ciki . Karamin dakine an kawata shi da kayan ado na mutanen da, zaune nake a kan wani luntsumemen katifa, wadda yake bisa wani katakon gado, na budi baki na ce wa yan matannan "su waye ku, a ina nake sannan waya kauni nan?" Wata daga cikinsu tace ainan kana gaban birnin sin ne cikin garin LAJUJ . "Ina ne kuma garin lajuj, na tambayesu" na tambayesu cikin mamaki Wacce ta bani amsa da farko ta sake cewa "ai garin lajuj garine na Aljanu don kowa daka gani anan garin aljanine, mutum dayace kawai ba aljana ba, amma itama ba mutum ba ce, kuma itace ta kawoka wannan birni namu, " . Cikin rudewa na mike a firgice ina neman hanyar gudu don kuwa na riga dana gama firgita da maganarsu, Na nufi kofar fita daga dakin cikin gudu na kama mabudin kofan na murda take kofan ya bude . Ban jira komai ba na nausa a guje, wata doguwar hanya na gani ta mike santa wannan hanyar na zura a guje, ko waigowa baya bana yi, ban dade da fara bin hanyarba sai na hangi wata kofa karshen hanyar, wannan kofa abude take, . Turus naja na tsaya a yayin dana shige cikin wannnan daki da yake da wannan kofa, . Zaune take akan wata luntsumemiyar kujera haryanzu wannan murmushin nata yana nan a fuskarta, Ta dubeni tai mani nuni da wani kujera tace na zauna . Babu musu naje na zauna akan wannan luntsumemen kujera wanda saboda tsabar laushinsa sai danayi tsammanin ko bulalliyar kujerace, . Zamana keda wuya sai na cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta wadda banki nayi shekaru talatin ina zaune ina kallo ba, karar budewan kofar dakin shine yaja hankalina inda na maida dubana ga wajen . Daya daga cikin matannan ne ta shigo tana dauke da wani faranti a hannunta mai dauke da akushi sai wani tambulan na zinare, tazo ta ajjiye a gabana . Tana ajjiyewa tayi ficewarta kyakkyawar budurwan ta dubeni tace "ga abunci nan kaci in kama sai muyi magana, " Ba musu na bude akushin wanda yake rufe sai nayi arba da dafaffiyar kaza, sai a sannan ne ma cikina ya fara kuka na tuna cewa wunin ranar ban ci komai ba , kuma banji yunwa ba sai yanzu . Toh dama ina cikin wannan hali ina zanji yunwa, cikin kankanin lokaci na gama da wannan kaza banbar komai a cikin akushin ba sai kasusuwa, nan na kora wani lemu mai tsananin zakin gaske sannan nayi hamdala ga Allah . Koda ta fahimci na iddar da abuncin sai ta fara magana da daddadan sautin muryanta wanda kan iya zauta mutum, "shuraih ka sani cewa ni sunana haseena tun ranar dana fara ganinka shekaru biyar baya naji zuciyata ta kamu da tsananin sonka, naji babu wanda nake so aduniya sama da kai, Tun a wancan lokacin na so na sanar dakai irin zunzurutun son dana ke maka Amma naji tsoron Abu daya, Wato naji tsoron SALMAN" Haseena tayi shiru ga barin magana llokacin data sadda kanta kasa, . Na tsinci kaina acikin wani irin Ni'ima wanda tunda nazo wannan duniya ban taba tsintar kaina a ciki ba, wai ni take so tabbas abun da Al'ajabi Cikin dakewa irin ta maza na dubeta bakina sai rawa takeyi nace HAS-sss Ena ta dago da kanta ta dubeni fuskarta na murmushi a gareni in ka ganta tamkar wata ran daren goma sha biyu . Nan da nan naji na samu kaina ina mai cemata "lallai babu mutumin da zaiyi arba dake baiji cewa yana sonki ba, tun dana fara ganinki nima zuciyata take bugawa ban taba gani ko jin labarin wata mai kyau irin nakinnan ba,, I na sssoosssonki Haseena" . Tayi murmushi sa'annan ta kama hannuna ta mike tsaye tace zo muje na gabatar dakai a wajen mahaifana, naji abun banbarakwai amma na dake nace mata masoyiya kafin muje mai yasa ba za kidan bani labarin wannan birni naku ba mai matukan ban Al'ajabi . Haseena ta dubeni da wani kayataccen kallo sa'annan Tace "habibina mai zai hana" Muka koma muka zauna akan luntsuma luntsuman kujerun dake makare a cikin dakin . Haseena ta dubeni tace "shuraih sunan wannan birni namu LAJUJ kuma wannan birni bayana kan Duniyarku bace ta mutane Wannan birni na Lajuj birnin Aljanu ne amma mun kasance musulmai kamar kai, mahaifina sunansa Nasaruddin kuma shine sarkin wannan gari namu..... ..Rayuwa haka take wakana yau lafiya gobe akasinta, dazu-dazu lafiya yanzu-yanzu rashinta Allah ka baiwa dukkan musulmi marasa lafiya masu lafiya kuwa Allah ka kara masu ,,,, Its 99% awakening from three 3 days sickness Yo sai mun Hadu MAKO mai zuwa Daga - www.facebook.com/hausaebooks . Marubuci:- Shuraih Usman Typing:- Shuraih 99% Hakkin mallaka (m) hausaebooks page BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 4 . Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin nan batare da iznin wannan shafi ba . Haseena ta dubeni tace "shuraih sunan wannan birni namu LAJUJ kuma wannan birni bayana kan Duniyarku bace ta mutane Wannan birni na Lajuj birnin Aljanu ne amma mun kasance musulmai kamar kai, mahaifina sunansa Nasaruddin kuma shine sarkin wannan garin namu, . Mahaifina ya kasance jinsin aljanu ne , amma kuma daya tashi aure sai ya tafi naku duniyar ya auro jinsin bil'adama wacce ta kasance itace mahaifiyata, sai da mahaifi na ya yai shekaru biyu a duniyar mutane sannan Allah ya baiwa mahaifiyata haihuwa, amma cikin rashin sa'a data haifeni sai ta koma ga mahaliccinta . Mahaifina yayi kuka sosai akan rashinta, domin kuwa a kullum da dare baya samun bacci sai tunaninta yake sakamakon irin zunzurutun shakuwan dake tsakaninsu, da kuma matsanancin soyayyar da suke wa junansu . Tun daga wannan lokaci gaba dayan son da mahaifina yake yi wa mahaifiyata sai ya dawo kaina, ya dauko ni muka dawo wannan duniyar, amma lokaci lokaci yakan daukeni muje duniyar mutane na dan wani lokaci sannan mu dawo wannan duniyar . Abum Al'ajabin daya kasance dani shine ni ba Aljana bace haka nan ni ba mutum bace, kuma ni Aljana ce Ni mutum ce,.." Har zan yi magana sai ta daga mani hannu alamar nayi shiru, ta dora da "tsananin kyawuna ne ya sanya aljanu da yawa ke muradin suga sun aureni, amma sam mahaifina ni baya son na auri Aljan , , Daga cikin masu son su aureni akwai Salman salman shine sarkin yakin wannan birni namu
Table of Contents