Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Budurwar Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,182 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wanda tunanina ya bani cewa bayi ne, kama yadda na zata dun haka yake dun kuwaina budewa na shiga na samu ruwa cikin wata randa na zinare batare da bata lokaci ba nayi wanka da wannan ruwan sai de abun daya daure shine a duk lokacin dana debi wannan ruwa sai naga ya karu Har na iddar da wankan na fito daga bandakin na nufi kan gadona domin na saka kayan dana cire ajje , Amma kayan sai sukace daukanmu inda ka ajje, na neme su sama da kasa na rasa, can na bayan na gaji da nema sai na dawo kan gadon na zauna nayi tagumi, wani haske naga dan kashe mani idanu, na kai dubana ga wajenda hasken ke fitowa sai naga ashe ma a gefena ne, nakai hannu don ganin menene wannan yake wannan haske, cikin mamaki sai gani nayi hannuna ya tabo wasu lallausan abu duk da ban ko menene ba sai na daga abun sama toh anan ne aka samu mishkila abun ya kubuce daga hannuna ya fadi a kasa ai yana faduwa sai naga ashe ma kayane riga da wando irin na sarautar mutanen garin Cikin tu'ajjibi na dauki kayan na sanyasu a jikina sannan na nufi wajen madubin dayake dakin nayi mamaki ainun alokacin dana irin zunzurutun kyan danayi, kai alokacin sai dana koda kaina nace ashema ni kyakkyawane haka, , Karar Kofan dakin ne ya katse ni, lokacin da ake kwankwasawa, na nufi kofan nabude su ukune kamar yadda na fara ganinsu, har yanzu babu wani sauyi atare da su, yan matan jiya ne daya daga cikinsu ta dubeni tace "ran ka ya dade gimbiyace ta turomu mu tafi dakai wajenta don kuyi kalaci" "Wacece kuma gimbiya" na tambaya "Wacce ta kawo ka nan garin" "Wai HASEENA ki ke nufi" Na lura da cewa wannan kalma danayi na karshe yasa dukkansu sun tsorata duk da bansan dalilinsu na tsoratan ba, "Eh itace , amma yallabai kasani duk fadin kasarnan babu wadda yake kiran ta da sunanta hatta mahaifinta ma, " "Saboda me ba'a kiranta da sunanta" "Wannan kuma wani sirrine na gidan sarauta" Na jinjina kai sannan nace masu "Toh muje " Suka juya suka fara tafiya ni kuma na take masu baa . Mun danyi tafiya mai dan nisa sa wacce takaimu izuwa wani kayataccen lambu wanda ya yalwatu da yayan itatuwa, su kansu bishiyoyin dake cikin lambun ababen sha'awane, domin kuwa bishiyoyin dukkansu yana yinsu daya ne, tsayinsu da komai na su, Furannin lambun kuwa sun kasance a duk bayan dakika daya suna dunkule wa waje guda, Muka nufi wani waje daban a inda muka bi ta kan gada, wannan gadan de an kerashi ne da zallar itace da igiyoyi aduk lokacin da muka taka gadan sai kaji wani kara na tashi . Tun daga nisa na hango kyakkyawar fuskarnan nata sai sheki yakeyi, farace kyakkyawa gata da dirarriyar jiki domin kuwa shape dinta na kwalbar cokacola ne, Ta mallaki tsastsaikan fuska wadda ke dauke da dara daran idanu, wayanda jure kallonsu, dan mitstsin bakinta wanda idan ka lura da kyau alokacin data ke magana zakaga tamkar baya so ya bude, . Ayau tana sanye ne da irin kayan duniyanmu kuma irin na kasarmu, riga Atamfa da sikert, abun ya bani mamaki ainun, ni danake zaton babu irin wannan kaya a wannan garin, sai de dana tuna da abu guda sai nama dena mamaki . Ayau tafi kowanne lokaci kyau fuskarta sai sakin tausasan murmushi yake a gareni, ai ban san lokacin dana kura mata idanu ko kiftawa bana yi ba, Muka kariso wajen yan matan nan sukayi saurin russunawa akasa zasuyi magana kenan ta dakatar da su ta hanyar daga masu hannu sannan ta sallamesu, sukai tafiyarsu . Ta dubeni tai wani murmushi wanda yake zuzuta wutar kaunarta a zzuciyata, "ka kwana lafiya" "Lafiya lau" Ta riko hannuna , awannan lokacinma sai da naji shocking ya ziyarci kwakwalwata, har nayi dan kara karami, ta jani muka karisa gindin wata bishiya, inda naga an shimfide gaba dayan wajen da wani babbar tabarma, a tsakiyar ta barmar ga abubuwan ci da sha nan birjik, Takalmi na cire alokacin da nake shirin hawan tabarmar, Wani laushine ya ziyarci tafin kafafuwana ,ko kadan wannan baiyi kama da tabarmar dana sani ba mai uban gurza-gurza Haseena ta zaunar dani itama ta zauna kusa dani yanda muna iya jin numfashin juna "Shuraih tun da nake a duniya ban taba ganin dan Adam lokaci daya naji sonsa ba saikai, hakan nema yasa yau dinnan zan fada maka sirrin dake tattare dani ina sonka shuraih so ,kuma ina muradin zama abokiyyar zamarka na duniya da lahira, Jina nake tamkar wanda akaiwa kyautar Aljanna domin kuwa a wannan lokaci na tabbata babu wanda yakaini farin ciki "Haseena kiyi sani cewa nima ina sonki , kuma babu abunda bazan ma don na mallakeki, nasan cewa kina shakkun wannan gasa ta fidda gwani ne, toh ki sani muddin akan ki ne sai de na mutu awannan gasa don kuwa bazan bari wani daban ya sameki ba, ki kudurta a zuciyanki nine mijinki" Hannu ta saka ta dauki wani tuffa ta mai gaza daya, har zata kai na biyu sai nayi sauri na karbi tuffan daga hannunta ina mai yimata wani irin murmushi na zolaya, sannan nima na gaza daidai wajen da ta gaza Anan muka luluka izuwa duniyar soyayya domin kuwa hira muka shiga yi sosai yadda take bani labarin garinsu, sosai naji dadin wannan lokaci . Muna tsaka da hiran ne wani lokacin izan ta fadi abun dariya sai mu dara , wata kakkausar murya ce ta katse mu da fadin "BUDURWAN SIRRI bata bil'adama bace, . Dukkanmu muka juya don ganin mamallakin wannan murya,,,,,, . www.facebook.com/hausaebooks BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks page @shuraih 99% Page 6 . Gabjejen katone mai kirar mutanen farko yana da tsayi wanda na tabbata yayi ni Uku a tsayi don sai dana daga wuyana sannan nai nasarar ganin Fuskarsa a turbune fuskar yake babu alaman murmushi ko kadan a tare da shi, kwayan idanunsa jane, gashin kasumba ya rufe mai baki yayin da ya hade da gashin gemunsa wanda ya zura ma wani zobe ya kulle . Yana sanye da riga falmara mara hannu hakan yasa na samu nasarar ganin kwanjinshi, gaba daya jikinsa a mummurde yake, ga jijiyoyin jikinsa sun tashi sunyi burdum burdum kai kace igiyace . Hannunsa na dama yana rike da gashin gemunsa wanda ya rike daidai wajen da ya zura zoben yana dan liliyawa ,fuskarsa na yatsinewa wanda shi a zatonsa murmushi yake, Shi ba mummuna ba haka kuma shi ba kyakyawa ba, amma kallo daya kadai nai masa na gane cewa wannan dakare ne, domin kuwa akuibin cinyoyinsa hagu da dama akwai wasu takubba manya manya cikin kufensu , wayanda na tabbata in aka ce na daga daya cikinsu bazan iyaba . Cikin firgita da tsoro na saki baki galala ina kallonshi har ya kariso garemu, Abun daya daure mani kai shine sam babu alamun firgici a fuskar haseena A zuciyata nace yo ta ina zata firgita bayan itama yar uwarsu ce, na sake maimaita wannan suna da naji ya kira haseena da shi a cikin zuciyata BUDURWAN SIRRI . Yana tafiya takubban dake

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});