Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Budurwar Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,173 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mayaudariya kake yimin, gani kake tamkar yaudaranka nayi Kasani cewa tunda nake a doron duniya babu wani namijin dana taba jin sonsa in banda kai, Alokacin dana fara ganinka, sai da zuciyata ta buga, ina matukar farin ciki da nishadi aduk lokacin dana ke tare da kai, duk da nasan na bata maka amma kayi hakuri ina sonka so na gaskiya Allah yabaka sa'a a wannan tafiya da zakayi yakuma dawo dakai gareni lafiya" Tsaban dadin danaji ya ziyarci zuciyana yasa na kurma ihu, ina fadin alhamdulillah, A haka har na iso bakin bukkar tsoho zaikid, Na sameshi a zaune kan wasu itatukan da muka sassaka a tare a matsayin kujeran zama, , Sam baiyi mamaki da ganina ba sai ma gani nake tamkar ya san da zuwana, Nayi masa sallama ya amsa cikin tausasa murya Cikin farin ciki na dubeshi nace "baba " sunan dana ke kiransa da shi kenan "So nake ka maidani garinsu haseena " Ina fadin haka sai naga kwalla ta gangaro daga fuskan tsohon ganin hakan ya rikita ni ainun Na matso ina mai tambayarsa" me ya faru ne baba" , "Haseena,nasaruddin da dukkan ilahirin Aljanun da suke birnin lajuj sun HALAKA" Abunda bakin tsohon ya furta kenan , Kirjina ya buga dumm gabana ya fadi Na dubeshi cikin rashin fahimtar inda zancensa ya nufa nace "kaman yaya sun halaka baba, nifa ban gane zancenkannan ba" , "Shuraih su Nasaruddin sunyi kuskure babba, wajen amfani da wannan makamin don hallaka birnin Bulzum, tabbas da sun san illan da makamin zaiyi masu toh da basu kwatanta amfani da shi ba gashi yanzu dukkansu sun hallaka birninsu ruwa ya mamayeshi" Tsoho zaikid ya fada yana mai tashi tsaye kafin ya cigaba "A ka'idan wannan makamin guda daya ake sana'antawa, in angama amfani da shi sai a sake sana'anta wani, Amma su nasaruddin sun sana'anta guda uku daga cikin ukunne suka baka daya kaje ka tayar a birnin bulzum abunda basu sani ba shine, muddin aka tayar da makamin ya gama aikinsa sai hayakinsa ya bazu a duniya a duk inda yaci karo da irin makamin sai ya tayar da shi, toh hakanne ya faru bayan ka tayar da daya a birnin Bulzum daya gama hallaka mutanen birnin sai hayakinsa yabi iska ya je har birnin lujaj ya kuma ci karo da irin makamin hakanne yasa ya taada su, toh kaji kuskuren da su nasarudden sukayi, sai ka shirya na mayar dakai duniyarku" Ya karashe maganar yana mai nufan bukkansa , Daskare nake a tsaye tamkar gunki, numfashina ya tsaya cak, inbanda bugun da zuciyata take sai ka rantse gunki ne ni , Tsaban rudewa ne ko tsaban firgici, BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 11 . , Dukkan wani na'uran sadarwa na jikina ya dena aiki, ahankali a hankali, kwalkwata tafara kawo wuta, Tunanina ya fara dawowa, "INna lillahi wa inna ilaihir raji'unn" shine kalman da bakina keta faman furtawa, Na durkushe a kasa, yayinda kaina ke tsananin sara min, "Haseena! Haseena!!" Sunan da nake ambato kenan har na bingire a wajen a sume, ********* "Shuraih ina sonka ba zan taba Rabuwa dakai ba, me rabani da kai sai mutu...." Nayi sauri na sanya tafin hannuna na rufe mata baki "Ina fatan ko a Rayuwana bayan mutuwa na kasance dake, haseena" , Haseena kwance akan kafadana yayinda ni kuma nake shafa gashin kanta, Ta janye jikinta daga nawa sannan ta mike tsaye, ahankali ta fara tafiya tana miko mani hannu alaman na riketa, cikin zafin nama na mike na nufeta da dukkan kuzarina domin na riqe hannunta, Murmushi kawai take mani tana tafiya da baya, fuskarta na dubana, Hankalina bai sake tashi ba sai a lokacin da na hangi a bun dake gabanta, Wawakeken Rami ne, a gaban haseena wanda muddin ta kara gaba kadan toh zata fada, , Na sake kara karfin guduna domin na cimmata na rike mata hannu don kada ta fada cikin Ramin, Amma sai naji kaman ana rikeni ta baya gudu nake sosai amma gani nake tamkar ina gudu ne a cikin Kogi, , kamu daya kacal ya rage na cafke hannun haseena, hakan yasa na daka salle nayi sufa , Alokacin ne kafarta daya ta fada cikin ramin nayi nasara hannuna ya taba nata kafin gaba dayan jikinta su dulmuya cikin wawakeken Ramin , "Haseena!haseena" Firgigit na farka , ina mai sake kiran sunan nata a fili "haseena" "Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun" na fada a fili yayinda nayi arba da abun da ya kusan zauta ni, Kwance nake a kan tangamemen lallausan kujeran dake girke a cikin daki . Dube dube da kalle kallen dakin dana tsinci kaina a ciki nake, . Kamar yadda dakin yake a baya kuma yadda na barsa, babu abunda ya canja Ina kwance akan dogon kujeran dake girke a cikin dakin, Dakina ne dana kwanta kwanakin baya, na farka na ganni a cikin dokar daji, , Karin tarin mamakina bai karu ba saida na kai dubana ga kayan dake sanye a jikina, kayan dana kwanta da su ne, a lokacin da na fito wajen Abasu kala don ya bani wayata, , Tunanika da yawa suka antayo mani a lokaci daya, anya ba mafarki nayi ba kuwa, kai tabbas wannan mafarkine , yo Im ba mafarki ba dama nasan babu ta yadda za'ayi wannan abu yafaru da gaske, ace wai daga kwanciyata a dakina na farka na tsinci kaina cikin dokan daji, . Nayi murmushi sannan nayi hamdala, yayin da dukkan tunanina ya raja'a akan dukkan wani labarin BUDURWAN SIRRI mafarki ne, addu'a na fara karaantawa lokacin dana mike na nufi kofan fita daga dakin , Na kama mabudin kofan na murza na yunkura da nufin na janyo kofan, Jinayi an turo kofan da karfi, hakan yasa na dan ja baya don ganin mahalukin dayake shirin shigowa cikin dakin, , Tunanina ya hasko min Ganina na farko da haseena acikin mafarkina dana yi, bansan lokacin da lebbana suka saki tausasan murmushi ba, , Abasu kala ne ya shigo cikin dakin, Yana sanye da bakar riga, wanda ake kira da jagaban, sai blue din jeans wandda aka yayyanka wani sashe na jikinta , da sunan Crazy, sabon style , "99%" ya fada yayin daya bani hannu muka tafa Cikin dariyan shekiyanci ya miko mani wayana, na sanya hannu zan karfa kenan sai naga ya zabura yayi baya, Walwala da annurin da fuskarsa ke dauke da ita ta juye izuwa tsoro da tsaban firgici Yayi nuni da hannunsa izuwa jikina yana cemin"99 menene haka ya ji maka rauni a dantse, dubi yadda jini ya bata maka riga" Nima cikin mamakin maganarsa na dubi dantsen haguna saide banga komai ba, Na sake juyo da dubana ga dantsen damana toh a sannan ne hankalina ya tashi, sakamakon abunda idanuna yaci karo da shi , In har ban manta ba, wannan rauni anyi mani shine a garin Bulzum, kuma wannan al'amari ya farune cikin mafarki, Toh wai dama in har abu ya faru dakai a mafarki, kuma ka farka wannan abu zai kasance a jikinka?? Na tambayi kaina Tambayar da bansan amsarta ba, , Na kai hannuna na taba wajen, Ihu mai karfi na saki sakamakon wani radadi daya ziyarci hannun , Karar ihun ne ya ankarar da

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});