Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Budurwar Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 634 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai gani nayi ta bude idanunta, Da sauri na kauda hannuna , ta mike zaune tana dubana sama da kasa tace "Wanene kai ? Yanzu a ina nake" "Zaki iya kirana da masoyi yake abar qaunata," "Masoyi!" Ta nanata sunan a bakinta "Amma ina ji tamkar na taba ganin ka a wani waje daban" , Ta fadi tana kallona Nayi murmushi nace "eh tabbas kin sanni domin kuwa mun sha haduwa dake cikin mafarki a matsayin Masoya, masu begen juna, bazan taba mantawa da ranar da kika furta cewa kina Sona ba, " , A dan firgice ta zazzaro idanuwa tace "da gaske ni na fadi hakan" ' "Eh kin fadi haka kuma har ma kika bani zobe a matsayin Alkawarin aure a tsakaninmu, tun daga lokacin danai arba dake a cikin mafarkina rayuwata ta sauya, a kullum bana da buri sai na in sake yin mafarkinki, nakan raba dare ina mai tunano da kyakkyawann fuskarki , abun dayafi jamin hankali dangane dake shine murmushinki, aduk lokacin dana tunaki sai inji farin ciki ya baibayeni, duk irin kuncin dana ke ciki da zarar na tunaki sai ya yaye, Akullum addu'ata shine ubangiji ya bayyana min ke a zahiri, da shike Allah maji roqon bawansane, sai gashi Allah ya hadamu," Haseena tayi shiru tana kallona ga dukkan alamu kalamaina sun ratsa jikinta, Cikin sanyin jiki ta kwantar da kanta kas "Haseena" na kira sunanta Ta dago kai a hankali batare data amsa ba "Ina sonki, ina kaunarki, shin kina Sona" Bakintane ya fara kokarin motsi alamar tana son furta wani abun sai kuma ta fasa , Ta mike tsaye tsam ta fara tafiya cikin sanyin jiki , har ta isa bakin kofan bukkar sannan ta juyo muka hada idanuwa da ita Duk da bana iya jure kallon cikin kwayan idon haseena, a wannan lokaci sai na tsinci kaina ina mai kallonta batare da kiftawa , , Murmushi tayi yayin da gefen kumatunta suka lotse wushiryarta suka fito, hakan yayi matukar kara fidda kyawunta, daga nan sai ta fice daga bukkar a guje , Koda naga haka sai nima na tashi na fice daga cikin bukkar........ ALHAMDULILLAH Anan na kawo karshen Littafin BUDURWAN SIRRI Sai kun jini cikin sabon littafi , Duk wani kuskure dana tafka Allah ya yafeni Gefen ADABI kuwa, Ashirye nake don karbar gyararraki, shakka babu ni kaina nasan da kwai kurakurai da dama dana tafka, A kullum burina shine na ga na kware wajen rubutun hausa na adabi, DAlibi nake ba gwani ba , Dan koyo nake ba dan iya ba Wannan shine takena , (c) Shuraih 99% 2018 BUDURWAN SIRRI Publisher : (c) Shuraih 99% Author : Shuraih Usman Year : 2018 . Wannan littafin na BUDURWAN SIRRI an fara kasuwancinsa Okadabooks akan #300 , Wayanda suke son karantawa sai su duba facebook ko kuma su duba shafin Shuraih 99% , Masu neman Ebook sai suyi marmaza su garzaya shafinmu na ebook mai taken Hausaebooks.cf . Nagode wa Allah mai kowa mai komai daya bani dama na kammala littafinnan , Matukar godiya da jinjina ga ahalin ; _____ PAGE _____ Shuraih 99% Triple Abubakar Hausa Books Littattafan Hausa Dandalin Abduluk hausa books Zauran Labarai Home of Littafan Yaki And Hausa Novels Hikayoyin Yaki Hausa ebooks - pdf,txt and doc _______ GROUP _______ KINGBOY ISAH HAUSA NOVELS FILIN LITTAFAN HAUSA NEW TSANGAYAR MARUBUTA "TASKAR GIDAN LITTAFI" HAUSA BOOKS HAUSA NOVELS Chakwakiyar Soyayya Hausawa DA Pulani Donated By www.Hausazone.Com KUZO MUYI NISHADI Samee khairah novels group DANDALIN HAUSA NOVEL DUNIYAR MAKARANTA LITTATAFAN HAUS 360 Hausa Novel Books FEENAT JA'AFAR NOVEL'S HAUSA BOOKS NOVELS Just Hausa Novels kingarticle novels of abdul$bafferh Zumunci Hausa NoveLs [ÝäzèèÐ] HAUSA NOVELS ONLY *FATIMA ZARAH NOVEL GRP(HAUSA)* Hausa Novels by ASK (GREAT HAUSA NOVELS BOOKS) SOYAYYA RAYUWA CE ZAINAB MUHAMMAD AND NUHU ALIYU GUSAU NOVEL GROUP Nagode sosai da yadda kuka nuna kulawarku gareni da kuma bibiyar littafin budurwan sirri Allah ya barmu tare Nine dai nakunnan shuraih Usman inkiya 99%

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});