Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Aljana Ce Ko Mutum Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mallam, tashiga tasamu nawwara ta tashi amma jikinta yana mata kamar ciwo ciwo, da taimakon matar nan tayi wanka da ruwan magani sai taji jikin nata ya mata dadi, ta fito wanka matar ta kawo mata kaya tare da abinci, bayan tagama ne , mallam yace tafito tasamesu a falo, bayan ta zauna suka kara hada ido da nawwar taga ita yake kallo sai taji ta tsane wannan nawwar din don tak'in jinin kallo , shiko zuciyarshi sai har bawa takeyi, kamar zata fashe, don ya hango tsagwaron kiyayyar sa a idanun nawwara, mallam yayi gyaran murya yace sameeratu, nasan baki San Ina ne nan ba , kuma baki san suwaye muba, wato kin dade baki da lfyane tsawon shekaru bakwai dasu ka wuce, tayi saurin zabura tace shekaru bakwai fa kace ? wannan wani irin ciwo ne dake damuna har natsawon shekara bakwai ban sani ba? mallam yace kar ki damu a sannu zaki san komai. yaci gaba da cewa zaki iya tuna yaushe rabonki da gida? tayi shiru tare dayin tunani, sai tatuna abunda yafaru lokacin daza taje sallah gdan baba rabi sai ga wani guguwar isaka yatasu, tayi saurin cewa wallahi jiya ne danabar shagon dinkin mu zanje gdan baba rabi sallah sai ga wani guguwan iska yataso. abunda kawai zan iya tunawa kenan, mallam yace yauwa, toh ba jiyabane yanxu kusan shekaru bakwai kenan da faruwan wannan al'amarin, ta dafe kirjinta tace nashiga uku mallam, toh yanxu ina iyayena? badai tsawon shekaru bakwai bana tare dasu ba! , wayyo Allah abbana, wai meya sameni hakane? Kai malam ya d'aga mata alamar bata tareda iyayenta" toh yanxu nan wani gari ne! yace maiduguri, idanu tazaro, sai kuma tasaki kuka, to waye yakawoni maiduguri! mallam yace labarine mai tsawo kuma cike da al'ajabi da tausayi: yanxu dai kibari idan kin huta zakiji komai in Allah ya yarda" kuka kawai take tana cewa dan Allah sukaita wajan iyayenta taga awani hali suke" mallam yace ya isa haka nawwara kiyi hakuri insha Allah zamu sada ki da iyayenki, tace to ngd' nawwar da awwal tabasu tausayi sosai," mallam yace tashi kije ki kwanta abunki kar kisaka damuwa aranki kinji, kai tad'aga masa tana sharar kwalla. bayan tashiga ciki mallam isma'il ya kalli mallam da su nawwar yace yakamata mukai yarinyar nan wajan iyayenta, awwal yace haka ne kam sai muje gobe ko? tunda kano ne wajan bazai yi mana wuyan ganewa ba, hakane Allah ya kai mana rai. yaune ranar dasu mallam isma'il da su awwal zasu kano da nawwara, tafiya suke cikin mota kowa da abunda yake sakawa azuciyar sa har suka isa kano. *KANO* Alhaji idrisa ne kwance Afalonsa yana tunanin rayuwa" hajiya maimuna takawo masa ruwan sha da abinci, zama tayi kusadashi, tace mallam haryanxu bazaka daina yawan tunanin nan ba! yace haba maimuna' ai tunani ya zamemin dole yau ace shekara bakwai babu nawwara babu alamar ta" yau koda gawarta nagani daya fiyemin kwanciyar hankali , bamu san awani hali take ciki ba , hakane Alhaji, haka Allah y kaddaro mana muciga ba dayin addu'a, insha allahu zamu sami mafita , suna cikin magana ne wani yaro yazo yace ana sallama da Alhaji wai baki Daga maiduguri, yace to kace su shigo. *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN *Nusnim* *pyar* kuyi hakuri da wannan banajin DADI ne [1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* *By* *Nusnim* 5⃣6⃣➡6⃣0⃣ yace to kace su shigo, dan Aiken ya koma yace wasu mallam isma'il ance su shiga, nawwara tana cikin mota zaune da badan su mallam sun dakatar da itaba da tuni ta falla da gudu ta shige gdan, sai tsaki take ta ja, shiko nawwar kallon ta kawai yakeyi, yadda ta hade giran sama data kasa" azuciyarsa yace wannan yarinya za ayi daru da ita. muryan mallam ne ta katse masa tunanin sa, mllam yace sameeratu fito kimana jagora cikin gdannaku, kamar ko jira take amata magana, cikin murna ta fito waje tana washe hakora" tace to mallam, yace to bismilla mujenku, itace agaba tana tafiya cikin nutsuwa. suna karasowa tsakar gdan sukaci karo da zainab tana wanke wanke, karaf sukayi ido hudu da sameeratu, zainab ta saki kwanon hannun ta, ta arce cikin gidan da gudu tana ummu ummu ummu, gatanan gatanan, yayin data fada jikin Hjy maimuna, tace ke lafiyarki kuwa, alhajine yace zainab wakika gani kike gudu haka"" sai haki kike. ji yayi ance abba nice kunnuwan shi ce ta jiyo mishi muryar da bazai taba mantawa dashi ba, muryarda a kullum yake mafarki da tunanin Allah yasake had'a fuskokinsu kafin mutuwarsa" atare suka d'ago idanu cikin sauri shida hjy maimuna, suka zubasu ga kofa, nawwara ce tsaye tana hawayen farin ciki. Alhaji idrisa da hjy maimuna sukayi zumbur suka mike tsaye, kowanne bakinsa na rawa sun kasa furta kalma d'aya" dakyar kamar had'in baki sukace sameeratu kece kuwa, karasowa tayi falon da gudu ta rungume iyayen nata , tana kukan murna, abba umma nice nawwaran Ku, ban mutu ba inanan. su nawwar dake gefe sun basu tausayi, har sai da kwalla ya fito musu, nawwara tace zainab nice fa sis dinki wacce kuke kwana daki daya, da gudu zainab ta rungume nawwara, sister nah ina kika je nayi kukan rashinki na tsawon shekaru, amma kin dawo kenan baza ki koma ba ko?, nawwara ta share mata hawaye. tace karki damu sister zee na dawo kenan insha Allahu bazan sake tafiya na barki ba, Allah sarki dama yan magana sun ce sabo turkin wawa,sai alokacin Alhaji idrisa ya kalli bakin kofa inda su mallam isma'il ke tsaye cikin tausayi. ya karasa wajan su tareda mik'a musu hannu sukayi musabaha, sannan ya nuna musu waje suka zauna, aka gaggaisa, mallam isma'il ne yafara magana, yace Alhaji mu baki ne daga maiduguri, munxo ne don mu sadaka da yarka sameeratun nawwara, sannan kuma mufayyace maka abubuwan da muka sani, Alhaji yace ikon Allah ashe duk shekarunnan da suka shude sameeratu tana maiduguri bamu sani ba. mallam yace a'a bata maiduguri tana duniyar aljanu har natsahon shekara bakwai nawwara tazaro ido waje tareda dafe kirji tace duniyar aljanu kuma? mallam yace eh, Alhaji ya jinjina kai, yace lallai kam nayarda, sbd na tafka babban kuskurenda ko makiyina bazan masa fatar shiga halin dana shiga ba, nan dai mallam ya kwashe labarin bacewar nawwara har izuwa lokacin da aka ganta, babu abinda Hjy maimuna alhaji idrisa da ita kanta nawwaran keyi sai kuka, nawwara tana cewa yanxu nice nayi tarayya da aljanu, abbanta yace nawwara kiyafe min, duk ni naja miki na rashin d'aukar shawara da maganar malaman islamiyyarku. a'a abba ni baka min komai ba kaddara ce kawai tafado mana, Allah ya yafemu baki d'aya" ta d'aga ido tayiwa su mallam godiya, mallam yace ba sai kin mana godiya ba, kiyawa Allah godiya sannan kuma ki gode masu awwal abisa sadaukar da ransu da sukayi sbd ceto taki rayuwar, sannan kuma ameenatu bin saifulla duk da wannan tariga ta koma duniyar su. nawwara takalli su nawwar tace yaya awwal yaya nawwar , ina matukar godiya akan tsamoni da kukayi daga aljana zuwa mutum, Allah ubangiji yasaka muku da mafificin alkhari, yabaku abokanan rayuwa na har abada, yasa aljanna fiddausi ce makomar ku" kowa yace

Table of Contents

Chapters

14 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});