Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Aljana Ce Ko Mutum Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

illa abunda nasani shine!!! sunana sameeratun nawwara, nakasan ce aduniyar aljanu' nataso naganni a fadar sarki *GULMIYANU* tare da ya'yan shi biyu mace da na miji *Ambar* da *kiyara* ambar ne yake son aure na, ni kuma bani sonshi adalilin hakan ne nake fuskantar mummunar azaba" ban san su waye iyayena ba, kawai nata so naganni awajan kanwar sarki" *gulmiyanu* wato me suna *gimbiya *sameeratu* duk fadin duniyar aljanu ana jin maganar *gimbiya samiratu* sbd ita take mulki alokacin, amma yanxu ta mutu kuma bil adama su sukayi ajalinta, wanda ban san dalili ba" nayi nayi binciki afada min ni wacece amma haryanxu ban samu amsata ba"haka rayuwata taci gaba da gudana. Akwai watarana da bazan taba mantawa ba ina zaune bakin ruwa ina wasa da tsuntsaye domin suke debe min damuwar dake zuciyata!! sai naji abayana ana min magana juyawan dazanyi, naga wata kyakkyawar matashiya kuma bafulatana" dauke da kwaryan nono tana min murmushi, tace nawwara ko zan iya zama kusa dake? na daga mata kaina tare dayin murmushi, kafin tazauna sai naji tace *bismillahi*sannan tazauna na kara kallonta, itama ta kalle ni, sai naji ta ambato sunana, tace nawwara, nasan baki sanni ba kuma baki taba ganina ba" amma ni nasanki, nasan asalinki, nasan labarinki me dauke da tausayi. kullum in zan wuce ta bakin ruwannan ina ganinki kina cikin damuwa, abun na damuna" shiyasa nace bari yau nazo nafada miki asalin wacece ke, kuma suwaye iyayenki, kuma infada miki" awani jinsi kika fito , *jinsin aljan* ko *mutum* dannasan shine abinda kikafi damuwa akai" cikin murnata na rungumeta ina cewa nagode yar uwata, tace bakomai, yar fulani taci gaba da cewa amma inaso kimin alkwarin bazaki fada ma kowa idan nafada miki asalinki ba" sbd idan akaji sai ankasheni. kuma addinina dana su ba daya bane, ni musulma ce sunana *Ameena Bintu saifullah* , taci gaba da cewa nawwara ke diya ce ga abdullahi da asma'u, kin kasan ce ajinsin _____ sameeratun nawara tayi ajiyar zuciya, awwal yace kinyi shiru baki karasa ba,ta dago idonta wanda yayi jajir ta kallesu, nawwar ya rikice yace lafiya nawwara" cikin murya mai rauni tace Aminatu bintu saifullah bata karasa fada min ba, naji tasaki wani uban ihu tafadi kasa, juya wan dazanyi naga *kiyara* ce da wasu kartan maza, su suka aikata ma ameena haka, ashe sunji abunda ameena zata fadamin shiyasa suka mata haka" nashiga rokon kiyara dasu bar azabtar da ameena amma ina, tun ameena tana cewa nawwara ki taimakeni nawwara kitaimake ni, nayi nayi iya kokarina" intaimaki ameena amma ina sun bace da ita!!! nawwar da awwal wanda hawaye yagama wanke musu fuska nawwar yace yanxu ina suka kai ameena bintu saifullah? tana raye ko bata raye? tace tana raye amma tana cikin wani ma ajiyan mu da ake kulle me lefi, tana shan azaba kala kala, banta6a mantawa lokacin dana yima ambar wayau ta sigar soyayya daya kaini wajan ameena dana ganta, da kyar ya amince" da mukaje naga duk ta canxa kamanni sbd azaba, kalmar data fadamin shine, tace nawwara kibazama duniyar bil adama kine mi addinin musulunci domin shi zai iya taimaka miki wajan gano asalin jinsin da kike. *EDITED* BY *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN *nusnim* *pyar* [1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* 2⃣5⃣&3⃣0⃣ Tun daga lokacin da ameenatu bintu saifullah tace nabazama duniyar bil adama don neman addinin islama"daga ranar na dau niyyar shiga duniyar bil adama, da haka rayuwata taci gaba da tafiya, ba abunda nasa agabana sai neman addinin musulunci, nayi yawo dayawa acikin duniyar bil adama, narasa wazan tunkara da wannan batu nawa" ana haka ne ranar sallar ku ta edi na hadu da kai, alokacin da kake k'ask'an da kanka wurin ubangijinka' kana addu'a, kana niman taimakon Allah. tun a lokacin naji ka burgeni' zuciyata ta aminta dakai, naji bawanda yadace na tunkara sai kai, daga ranar nafara bibiyarka, atunani na kaine zaka taima kamin gurin gano wacece ni, kuma ka koyar dani addinin islama""nawwar kataimaki rayuwata ina cikin tsaka mai wuya, ka taimakeni ka tsamoni daga duhun jahilci" ta karashe mgnr muryarta na rawa" Nawwar ya numfasa yace sameeratun nawwara naji bayaninki, amma wannan batu da kika zo dashi daidai yake darasa rayuwar mutum, ayanayin labarin da kika bada na fahimci duk wanda yayi yunkurin taimaka miki gurin gano asalinki, to shima dai dai yake da rasa tashi rayuwar gun wad'ancan azzaluman!!" amma addu'a itace takubin mumini, *innallaha laa' yamli lizholimin.* _lallai Allah baya kyale azzalumai_ da sannu zai nuna musu isar sa.... zan taimaka miki don Allah da kuma son dana ke miki, sannan da yar dan mahaifiyata" idan ta amince shikenan sai mu tsananta addu'a Allah ya mana jagora. Tace nagode nagode sosai kuma insha Allahu wani abu bazai taba samunka ba, namaka alkawarin haka" kuma mami hafsat baza ta hanaka taimako ba da yardar Allah"" dr awwal ne yayi gyaran murya yace wani hanxari ba gudu ba, kun manta abu guda daya, kar ku manta sai da taimakon ameenatu bintu saifullahi zaku samu cikan burinku, saboda ita ta turo nawwara duniyar bil adama don tasamu mutumin daya rike addu'a don suje su taimaketa tafito daga hannun su ambar, ta bakin ameena ce za agano wacece nawwara!!! yanzu dai abunda zakuyi shine kutaima keta tafito, ko ba hakaba" sameeratun nawwara tace tabbas gskyan kane awwal dole sai yar fulani tafito, amma gurin da take akwai hatsari, nawwar yace karki damu da taimakon Allah zata fito. toh yanxu dayaushe ne zaka fara koya min addininna ku?, inshaAllah nan da sati daya ok nagode, bayan sunyi sallama sai ta bace. nawwar da awwal sunshirya yadda zasuyi su samu mami hafsat da wannan zance, labari har yakai kunnan mami hafsat, sai da ta girkiza dajin labrin" amma dayake da awwal ne kuma shi yake mata bayani sai ta amince musu tare dayi musu addu'an samun nasara,nawwar yaji dadi sosai da maminsa ta amince daman mace ce mai hakuri da tawakkali!!! *wanene nawwar* da'ne ga alhaji isma'il da hafsat, alhaji isma'il haifaffan garin yola ne iyayenshi duk acan suke gaba da baya shi ba fulatani ne, yayi makarantansa tun daga primary zuwa universty abti yola, yayin daya gama ne, aminin mahaifinshi wato alhaji kasim shiyasa ma mishi aiki a jahar kaduna" isma'il tun yana karami alhaji kasim ke sonshi" anan gdan alhaji kasim na kaduna isma'l ya zauna, yana da yaya mata uku, maza biyu babban dan alhaji kasim namiji ne me suna abdalla, sai ibrahim, sai hafsat da mariya sai khadija autar su kenan, mahaifin isma'il takanas yazo kaduna wajan amininshi alhaji kasim, don ne mama dansa auren hafsat, , kasan cewar dan nasa yaje masa da batun son auren hafsat , alhaji kasim yaji dadi sosai" kuma antambayi hafsat din itama ta amince, mafarin auren iyayen nawwar kenan!!" bayan auren su da shekara biyu Allah ya albarkace su da d'a namiji wato nawwar sai kuma sulaiman, daga sulaiman sai autar mami wato, maryam wace ake ma lakani da mimi, macen ta daya tal maza biyu,, mami hafsat ta bama ya'yanta tarbiya dai dai gwargwado, ga kuma addini daya ratsa jikin su, dukkansu suna da haddan alqur'ani mai girma, don shi sulaiman ma baban malamine a islamiya, yayin da nawwar shi kuma doctor

Table of Contents

Chapters

14 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});