Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Aljana Ce Ko Mutum Book 1 Complete Hausa Novel 1,184 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ne, sai autar su mimi itama karatun take afannin boko tana ss 1, afannin islamiya kuma tana *sanawiyya* . wannan shine lbrin su nawwar. ***************** *dunyar aljanu* sarki gulmiyanu ya tara dukkan aljanu yana shaida masu" nan da wata daya za ayi gaga rumin bikin dansa *ambar* da *sameeratun nawwara*, nan take taji gabanta yafadi, shi ko ambar da kiyara me zasuyi inba murna ba har gaban mahaifin nashi yazo yana godiya" ambar ya dago ido yana sakar ma nawwara murmushin samun nasara, sarki gulmiyanu yaci gaba da cewa' nan da sati biyu ina son akashe ameenatu bintu saifullah' cikin tashin hankali samiratu taje gaban sarki ta tsugunna tana rokonshi da abar yar fulani da ranta!!" amma ina sarki yaki amince wa, ganin sarki yaki sauraronta" tuni ta garzaya duniyar bil adama wajan nawwar don neman mafita, tafada mashi abunda ke faruwa shima hankalinshi atashe yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un , la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin"" ai bashiri nawwar yashiga koyar da sameeratun nawwara addinin islama, addu'oi iri2 yasoma koya mata' kan kace kabo sameeratu tayi zurfi sosai, idan yana koya mata wani abun ma sai ta dinga tunanin kamar ta tabayin abun ada:!!. akwana atashi ba wuya a wajan Allah, a yaune su awwal da nawwar da sameeratun nawwara, suka shirya hanyar da za adauko *ameenatu bintu saifullah* _sai ku biyoni agaba don jin shin zasu samu nasarar ku6utar da ameenatu bin saifullah ????._ *EDITED* by *UMMEE ADNAN* ~TAKU A KULLUM UMMU RUMAN~ *nusnim* *pyar* [1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* 3⃣0⃣&3⃣5⃣ sameeratun nawwara ta kammala shirinta tsaf tare da daukan makaman ta, saboda tsaro , bayan tagama ne ta garzayo duniyar su nawwar , ayayin da ta iskesu suna zaman jiranta shida awwal' nawwar ke kara karfafama awwal gwiwa akan wannan tafiya daza suyi.ganin yadda duk yake a tsorace, yace haba abokina" kada kabada maza mana' kadafa kamanta *Allah yace yana nan aduk inda bayawansa yake tsammaninsa'* kasa aranka Allah yana taredamu kumashi zai taimakemu" inafatan dai kayi azkar d'in safiya, da addu'ar dana baaka jiya? murmushi awwal yayi cikeda kwarin gwiwa yace nayi Allah ya taimakemu' Ameen... Sallamar sameeratu ne ya katsesu da karatun suratul yaseen dasuke bayan sungama karanta wasu ayoyi acikin suratul baqara" takaraso ciki, dukansu suka amsa mata sallamarta,fuskarta dauke da murmushi yayin da take kallon nawwar, shima ya mai da mata martani, tace masu *masa'un khair* suka ce mata *masa'u *noor*. auwal ne yace ai nayi zaton baza kixo ba, tace tab mai zai hanani zuwa, yanxun ma duk nakosa muje, nawwar yace ' ki kwantar da hankalinki insha Allahu zamu samu nasaran zuwa wajan ameenatu bin saifullah, tace toh Allah yasa nagode sosai" awwal yace ya naganki da makamai, tace ai saboda tsaro na dauko, yayi dariya, yace haba ai ayar Allah kadai ta ishemu makami' sbd haka karki samu damuwa, to awwal, yanxu sai kutashi muje don lokaci na kurewa. nawwar yace to amma bari mugabatar da addu'a kafin mutafi, suka ce to, nan suka karanta *suratul iklas* *falaq* da *nas* sai *ayatul kursiyu* sannan suka shafa, sameeratu tace kurufe ida nuwanku, yadda ta umur ce su haka sukayi. *duniyar aljanu* awani kurmin k'ogo suka sauka' tace subude idanunsu" nawwar ne yafara budewa tare dayin addu'ar neman tsari, shiko awwal yakasa bude idonshi saboda tsoro, don bai San me zai fara gani ba idan yabude idon. nawwar da nawwara suka dubi awwal cikin mamaki, nawwar yace awwal lafiya bude idanunka mana mun isofa, cikin rawar murya awwal ya soma magana , yace nawwar wallahi tsoron budewa nakeyi" sameeratu tace kar ka damu ba abunda zaifaru da kai kabude , nawwar yace haba doctor be a man mana, Kasa aranka kana tareda sojojin kariya daga Allah , ahankali awwal ya bude ido shima tare dayin addu'a. haka sukabi wajan da kallo cikin kurmin dajine , sameeratu tace nayi mana Rabin zuwa, sauran tafiya kuma da kanmu zamu karasa, saboda bani da karfin da zanjamu a iska mukarasa wajan, suka ce to " nan da nan suka doshi hanya tafiya suke sosai kowannan su da abunda yake tunani azuciyar shi, tafiya suke babu kakkautawa, har suka gaji suna samu gefe don su zauna suhuta. Duk abunda ke faruwa su sariki *gulmiyanu* ba su sani ba' sbd kafin sameertu sutafi sai da taje ta to she madubin da suke ganin hangar da zai sadasu da ameenatu bin saifullah , cikin ikon Allah kuma dukkansu babu wanda ya hankalta da hakan, itako ameenatu tananan cikin dakin azaban da aka ijyeta, tanaji ajikinta sameeratun nawwara natunkaro wajanta don taimako. awwal yace sameeratu wai bamu iso bane! wlh nagaji nikam, sameeratu tace yi hakuri saura kadan mukarasa, Allah dai ya kaimu lafiya amin. *Ambar* ne zaune da kiyara suna hira sai sukasa ajuyo musu madubin dazai sada su da ameenatu bin saifulllah , aiko anajiyo dashi sukaga abu bakin kirin, Akbar yayi saurin mikewa, yana cewa garin yaya wannan abun yafaru?tayaya ba aganin hoto? kiyara tace lallai akwai wani bakon al'amari ayi sauri aje abin cika, sannan kuma akira sameeratun nawwara , labari yaje kunnan sarki shima hankali tashe don ba'a taba mishi irin wannan abun ba. kiyara ta dawo cikin sauri tace babu sameeratu , nan take aka bude madubin da kyar , kafin subude su nawwar sun Isa ga ameenatu , duk sun kashe masu tsaronta da ayar Allah, sameeratu ta rungume ameenatu bin sai fullah, daidai lokaci sarki dasu ambar, suka hango abunda ke faruwa, ambar yasaki wani irin gigitaccen kara nabakin ciki, saida su sameeratu sukaji , ameenatu tayi saurin cewa maza maza kuzo mu wuce dan sun ganomu, su nawwar gabansu sai faduwa yake, yana ta karanto addu'a" haka awwal ma. sarki yace garin yaya haka tafaru bil adama har suka samu damar daza su shigo mana duniyar mu, cikin huci kiyara tace wannan duk aikin sameeratun nawwara ce, ambar yace mufar musu baza abar su da rai ba. nawwar suna ganin bak'in abu natasowa da sauri duk suka tsorata , sameeratu tace ameenatu kiyi sauri kifitar da mu gasu nan zuwa, tace to ni yanxu ina zamuje, nawwar yayi saurin cewa musauka aduniyar mu kawai, aiko dafda wani guguwar iske ya kusa dasu suka mace bat, cikin nasara, sai gasu aduniyar bil adama, cikin office din doctor awwal , suka zube akasa awwal da nawwar kamar wasu matattu, can suka farfado bakinsu d'auke da addu'a' nawwar yace anya baza su iya biyo mu nan ba? aminatu tace a'a, nayi wani abun da baza su iya gano inda muke ba, nawwar yace akwai wani gdna dake kusa da asibitin nan, yakamata muje can. suka ce to kowannan su zaune awwal dai shiru yayi don sai yanxu yakejin gajiya, bayan kwana daya da dawowan su duk kan su zaune afalo, idan kuka ga sameeratu da ameena bin saifullah sai ka rantse da Allah mutanene, sbd idan zasu hadu da bil Adam sukan fito asuffan mutane , yauma hakan takasance . nawwar yace naje nasamu malamina nayi mishi bayanin komai, kuma ya amince dashima yataimaka mana , gashinan zuwa nan da yan mintuna, don agabanshi za awarware wannan kullalliyar al'amarin, amenat tace tabbas kayi tunani nawwar , hakan nada kwau ,bata gama rufe baki ba

Table of Contents

Chapters

14 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});