Chapter 3
Chapter 3
bincikoni kun hanamin kwanciya cikin natsuwa?, bakin kiyara yafara rawa, cikin rawar murya tace kiyi hakuri sameeratun nawwara bamu san kina tare da itaba, ambar shima yashiga bata hakuri, cikin daga murya tace" ya isheku haka, meyasa zaku takura ma rayuwar ta? kun manta abunda nace kafin na mutu" kenan baku rike amanar dana barmuku ba? ambar yace a'a ba haka bane, toh inba haka ba meyasa zaku takura rayuwarta? kiyara tace Allah yaja zamanin gimbiya sameearatu, ta taka dokan da aka kafa mata ne shiyasa, soyayya taje tanayi da jinsin bil adama, wanda hakan kinsan yasabawa dokan da aka gindaya mata" gimbiya sameeratu tayi saurin zabura cikin kakkauran murya tace soyayya da bil adama, me kukeyi har tafara soyayya da bil adama? tuntuni kuka kasa daukar wani mataki da wuri sai yanxu?, duk cikin fushi da d'aga murya take maganar, nan take ran gimbiya sameeratu ya kara mugun baci, babu abinda ta tsana arayuwarta irin bil adama, saboda su sukayi ajalinta tabar duniyar su. *sai agaba zamuji wacece gimbiya sameeratu, kuma menene alakarta da sameeratul nawwara* ambar ne yayi saurin cewa kiyara janyo wancan kahon ki busa ma gimbiya sameeratu" da saurinta ta aikata abunda yace mata, tana busa kahon nan take gimbiya sameeratu tasaki wani irin hargitsatstsan kara mai karfi tare da zuwan guguwa mai karfi, har sai da su ambar suka rike bishiyar dake kusa dasu sbd karfin guguwar zata iya tafiya dasu, zuwa can wajan yayi tsit kamar ba abunda yafaru, ambar ne ya taimakama kiyara data fad'i kasa ta mike. dube duben sameeratun nawwara suka somayi, can suka ganota kwance gindin bishiya, suka karasa wajan, kiyara tayi tsafin su suka bace daga wajan. haka sameeratun nawwara taci gaba da rayuwar kunci da wahala akan nawwar dinta, duk sanda ta zauna babu abinda take sai tunanin rayuwarta tada mai dadi cikin kwanciyar hankali da y'an uwanta, hawayen fuskarta take gogewa tace kai kajamin wannan rayuwar bakin ciki da tashin hankali ayanzu babana" kaine silar komai ga rayuwata" gashi duk cikin yan uwanta aljanu ita kadai ce musulma, amma sam bata iya ibadan taba, gashi tanason bautama ubangijinta, sai dai bata san yadda zatayi ba, dalilinda yasa take matukar son hamma nawwar kenan. *mafarin haduwar tada hamma nawwar shine*, tashigo duniyar bil adama zagayawa, yakasance ranar sallar su ta EDI can ta hango wani kyakkyawar matashin saurayi yana sallah acikin natsuwa da kwanciyar hankali, bayan ya idar da sallah, taga ya daga hannayenshi sama yana kwararo kirari ga ubangijinsa" sannan yasoma rokan Allah bukatocinsa na alkhairi, ya kuma kareshi daga mugun abu. duk tana tsaye tana kallonshi yana addu'oi, ya matukar bata sha'awa' tafara tunanin kamar itama ada ta taba irin wannan addu'an, amma kuma meyasa yanxu bata iya ba" wani bangare na zuciyarta yace wani boyayyan sirri ne tattare da rayuwarki, wanda amayar da wannan sirrin bakaramin haddasa bala'i zaiyiba tsakanin bil adama da jinsin aljanu, birne wannan sirrin acikin kokonta zaifi zaman lafiya ga mutane dubu" taja wani dogon numfashi tare da karkata hankalinta gun nawwar daya gama addu'oin shi yakama hanyar gida. haka tayi ta bibiyar rayuwar nawwar da yadda yake tafiyar da ibadunshi, anan take son nawwar yasoma mamaye duka sassan jikinta, taji bazata iya rayuwa batare dashi ba" tun daga lokacin zuwa duniyar bil adama yazame ma sameeratun nawwara wajan zuwa,,tun tana zuwa ma nawwar amafarki, har takai da zuwa mai azahiri, anan ne shima yasoma kamuwa da son sameeratun nawwara, yakasa tantan cewan *Aljana ce ko mutum?* kuma taki bashi dama yamata tambayoyin dazasu gamsar dashi, taki gaya masa wacece ita, yana cikin tsaka mai wuya. *wannan shine mafarin kulluwar soyayyar su* *******************bayan nawwar yatashi daga bacci awwal yasa aka kawo mishi abinci yaci" sannan yabashi magani yasha, Dr awwal ya gyara zama da kyau ya kalli nawwar, wanda haryanxu tun tashinsa baiyi magana ba. Dr awwal yace nawwar meke damunka halan? jin yayi shuru bai amsa masa ba, yakuma cewa wani irin damuwa kasama ranka haka? wanda ke barazana da lfyr ka, duk irin amintar dake tsakaninmu ka kasa fada min matsalarka?, kana wasa da lafiyarka nawwar, gashi ciwon zuciya na kokarin kama ka, what" sai a sannan yayi mgn, ciwon zuciya fa kace doctor, kai ya d'aga masa alamar tabbatarwa, mekasa aranka haka? me kanema karasa, me kakeso wanda baka samu ba? kana so ka kashe kanka ne, kar ka manta kaifa likita ne, mai kare lafiyar al'umma, to meyasa kai kake wasa da taka lafiyar? hawayenda awwal yagani a idanun nawwar shiyasa shi saurarawa ga tambayoyinda yake jero masa, jikinsa yayi sanyi, duk yabi ya rude, yasan ba karamin abu zaiza jarumin abokinsa kuka ba" haba nawwar meye damuwarka? kafada min ko zan iya taimaka maka," nawwar ya kalli auwal, yace duk akan *SO* ne awwaal,,Allah ya jarrabi zuciyata dason *AlJANA* bama *MUTUM* ba, a tsorace Dr awwal ya mike tsaye da sauri, yana yima nawwar kallon wanda yayi gamo, yace anya nawwar kana cikin hankalin ka kuwa, kataba ganin Inda akayi soyayya tsakanin aljana da mutum , wlh nawwar kayi gamo, kana bukatar rukiyyar gaggawa, idan ma mafarki kakeyi,kara ka farka, wannan abu ne da bazai taba yuwa ba" kafin nawwar yabashi amsa sai ji sukayi ance , karya kakeyi awwal sai na auri nawwar koda zan rasa raina ne wlhy saina aureshi, ae tuni awwal ya kwasa a guje sai bayan kofa yana salati jikinsa na karkarwa" *EDITED* *BY* *UMMEE* *ADNAN* _TAKU UMMU RUMAN_ *nusnim* *pyar* [1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* 2⃣0⃣&2⃣5⃣ taci gaba da cewa awwal karka shiga hurumin da ba naka ba, kar kasa nawwar ya gujeni, zuciyata bazata iya jurar rashin saba" awwal ina matukar son nawwar" idan ban sameshi ba banajin zan cigaba da numfashi a duniya!! shi dai nawwar yananan akan kujera ya zuba maa sameeratun nawwara ido, cikin wani irin matsanancin sonta" dakuma jindad'in ganinta aransa' tabbacin yanxu andaina azabtar da ita kenan, kamar yadda matar nan tafad'a masa" awwal da har yanxu yananan a bayan kofa' ji yake kamar kasa ya bude yanitse aciki, saboda tsabagen tsoro' tuni ya rufe idanunshi, cikin dauriya yake cewa baiwar Allah kiyi hakuri baso nake nashiga rayuwarki ba, ina so ne inceto amini na daga hadarin daya shiga" sbd zuciyar shi tana dab da bugawa" wanda hakan zai iya rasa ranshi ako wani lokaci ta dalilin sonki" nawwar ya runtse idanunshi, ya juya da kallonshi wajan awwal, yace aboki na taho ka zauna baza ta maka komai ba!!! saneeratun nawwara tayi dan murmushi, tace awwal kenan, ni ba muguwa bace kuma banida niyyar cutar da mutane, kasaki jiki dani, kutaimaka ma rayuwata kai da nawwar. sai alokacin nawwar yafara magana yace baiwar Allah me na mikine kike wahalar da rayuwata? kin hana min sukuni"" sonki yana azalzalan zuciyata, ban taba zama nayi second guda ba tare da tunaninki ba, sannan kuma ban san ke wacece ba? ban san ke wace jinsi bace? shin ke ALJANA ce ko MUTUM? meyasa kuma kika zabe ni amatsayin nazama abokin rayuwanki? dan Allah don son annabi ki amsa min tambayoyi na, shima awwal dake mak'e haryanxu a bayan kofa yace kitaimaki abokina please. Ta numfasa tace duk naji bayaninku, tabbas baku san koni wacece ba' hakazalika nima bansan nid'in wacece ba"
Table of Contents