Chapter 7
Chapter 7
billah meyasa zaku aikata wannan mummunan abun, ambar yace sbd mahaifinta yaraba mu da farin cikinmu, saboda haka muma zamu rabashi da farin cikinsa ta hanyar d'auke y'ar wacce yafi so aduniya" daman kuma tamuce. mallam yace menene wannan abun daya rabaku dashi!, ambar yace yasa ansare bishiyoyin dake gdansa batare daya sanar mana ba, balle mu kwashi muhimman ajiyarmu' kuma alokacin gimbiyarmu me suna sameeratu, tana kwance akan gadon hutawarta abun ya afka da ita' da sauran yan uwan mu, saboda haka baza mu yarda ba, muna so a Isar masa da wannan sakon" mun sassauta hukuncinmu akansa ne sbd sonda muke ma nawwara" badan hakaba damun dad'e da d'aukar mummunar fansa akansa" kafin mallam yace wani abu har yafita daga jikinta , ita kuma sai tari take aka bata ruwan addu'a tasha sai bacci ya dauketa. Bayan kwana daya da faruwan haka shugaban makarantansu da mallamin ajin na su suka je gdan Alhaji idrisa , bayan sun gaisa ne suke bayyana mishi abunda ke faruwa, yace sam shi bayyarda da wasu aljanu ba, yar shi kuma bazai wuce maleria bane ke damunta, ai wannan ma tatsuniya ce, aljanun banxa aljanun hufi, duk wannan ta tsuniyace, da karyan yara, mallam yace a'a Alhaji, kar kamanta fa Allah da kansa yana fad'a acinkin alqur'ani cewa ( *wama khalakatul jinna wal insa illa liya'a budun* _bamu halicci mutane da aljanu ba face dan su bauta mani_ ) Ashe kuwa kaga aljanu gskya ne, su suna ganin mu amman mu bama ganin su, kuma maganan gsky sare bishiyan nan da kayi batare da kasan matakan daya dace kayiba kafin hakan akwai matsala, sannan kasan bishiyoyinnan sunyi sama da shekara talatin da y'an doriya ba asare su ba sai yanxu? kaima kasan dole asamu matsala, zaman lafiyarka da iyalinka shine kabasu hakuri, inba haka ba, watarana zakayi kuka da idanun ka, don bakasan kaidin aljanu bane shiyasa, muna kara baka shawara da kabasu hakuri kawai" dan tsira da iyalanka" , Alhaji idrisa mutum ne mai taurin kai da kafiya akan ra'ayinsa, da kuma karyata aljanu, ya tashi cikin fushi yace mallam dan Allah kutashi kutafi sun dad'e basu dauke ta dinba makaryata kawai, cikin fushi suma suka bar gdan. aljanun sunji duk abunda Alhaji idrisa yace, kuma sun dau alwashin sai sun dauke sameeratun nawwara, duk ranar da taje islamiya sai suntashi mata kuma sai sunkara fada zasu sace ta. Ranar jumma'a sameeratun nawwara taci kwalliya zataje gdan yayar babanta ta gaidata daganan ta wuce shagon dinkin su"" dayake tana koyan dinki, bayan taje gdan goggon nata ta wuce shagon su, kawar tace khadija tace kin makara nawwara yau nariga ki zuwa , nawwara tayi murmushi" tace wlh nabiya gdan goggona ne, Ayya ke kadai ce ashagon ina aunty marry, khadija tace taje kasuwa ,ok, nan sukaci gaba da hirar su har la' asar tayi, nawwara tace Khadija bara nashiga gdansu baba rabi nayi sallah tunda ke kina fashin sallah, tace to fad'awa duniya bana sallah yau takarashe fad'a tana dariya, nawwara tayi dariya. ta kama hanyar zuwa gdan kenan sai ga wani guguwar iska yataso ya dumfaro nawwara, kiyara ce tazo ta dauke ta, tun daga lokacin nawwara bata sake sanin ita wacece ba, kawai ta ganta ne aduniyar aljanu , duk sun tsafeta da abubuwan su tazama irinsu, amma kuma kana ganin nawwara sai kace ruwa biyu ce, wato aljana da mutum, haka takoma"" wannan zoben dake hannunta shi yakara bata duk wani karfin tsafi, shiyasa tazama kamar aljana, amma kuma akwai wajajen dabaza ta iya zuwa ba aduniyar aljanu, kasan cewarta ita ba asalin aljanar bace. in baku manta ba ko wajan da aka daure ni bata karasa daku ba sai da kafa fuwanku kuka karasa, sbd batada karfin isacan, da sunyi niyyan kasheta ne sai ambar yace yana sonta , acan kuma duniyar bil adama, khadija tajiki shiru baki dawo ba. nan aka bazama neman nawwara lbrin batanta yazagaye ko ina, har makarantar islamiyar su, mallaman su sunyi takaicin haka' shiko mahaifinta kamar zaiyi hauka, yana cewa karya kuke kud'auke min yarinya ta, yayi ta sambatu yana tsine musu, abu wasa² har anfidda tsammanin ganinki, kowa ya dangana anmik'ama Allah lamuransa" sai bayan batanki ne mahaifinki yafara daya sani sai alokacin mahaifinki yayarda da akwai aljanu, shi sam daya karyata aljanu, yana ganin duk karya ne, damuwa tamasa yawa' wanda hakan ya kwanta ciwo na tsawon shekaru biyu sannan y warke duk yan uwanki sun dangana. ke kuma kina can kina rayuwa da aljanu, sun gusar miki da kwakwalwa, wannan shine abunda ya faru deke nawwara, awwal saida ya zubda hawaye , nawwar yace wai meyasa mutane ke son karyata aljanu, bayan kuma Allah yafada, da akwai, acikin aljanun ma akwai masu bauta mai, kamar yadda akwai amutane akwai musulmai a kwai kafurai, sameeratu dake zaune tazuba musu ido tarasa meke mata yawo a kwakwal warta. nawwar yace to meza ayi mata ta dawo yadda take cikakkiyar mutum,ameenatu bin saifullah tace kunga wannan zoben dake hannunta za'ayi kokarin cireshi, sannan kuma sauran aikin malllam ne yasan yadda za'ayi. mallam ne yayi magana yace nawwara ba ita kadai bace akwai gimbiya sameeratu ajikinta kuma karya wayannan asiren dake jikinta bakaramin aiki bane, zamuje da ita Maiduguri, don nikadai bazan iyaba , bai gama rufe bakinshi ba sukaji gdan y girgiza yayin da nawwara ta xube kasa wani bakin abu nafita Daga bakinta,duk kan su suka nufo kanta cikin tsoro wutan dakin ya dauke ko ina bakin kirin. *EDIDTED* BY *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN *Nusnim* *pyar* [1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* *By* *Nusnim* 4⃣6⃣➡5⃣0⃣ wutan dakin ya dauke ko ina bak'ik'irin baka iya ganin komai" ameenatu bin saifullah tace mallam ya kamata kayi wani abu don suna dab da isowa inda muke, kuma ga nawwara cikin wani yanayi, wannan bakin abun dake fitowa daga bakinta alamun suna son fitowa ta jikinta ne, wanda hakan daidai yake data rasa rayuwarta, nawwar yana jin haka yace mallam kataimaka dan Allah. bani son in rasa nawwara arayuwata" shikansa mallm al'amarin yasoma firgitashi' bayyi tsammanin abin yakai hakaba' karatu yasomayi cikin gaggawa, suma su nawwar suna karanto duk ayar datazo abakinsu"saida sukayi kusan minti 30, sannan hasken dakin yasoma dawowa , gdan kuma yadaina girgiza, nawwara ta bud'e ido, sai dai takasa magana, sai binsu take da kallo kamar wata tab'abb'iya. *DUNIYAR ALJANU* lokacin da su ambar suka karaso basuga su ameenat bin saifullah ba' don sunriga sun bace musu, sunyi sunyi su bisu amma ina sun kasa" sarki yayi takaicin haka sosai, suna tunanin ta ina zasubi suje duniyar bil adama, saboda wani katanga dake tsakanin su, sunyi tsafin su amma ina sunkasa rusawa, shine suka yenke shawaran fitowa ta jikin nawwara, amma ina basu sami hanyar fitowa ba, saboda karfin addu'ar da mallam keyi don saida ta kona wayansu, dole suka koma ta katangan suka fara aikin rushewa. *MAIDUGURI* Tunda suka kama hanyar zuwa mai duguri, mallam yafad'ama babban mallaminsa gasunan tafe, sun isa lfy an tarbesu cikin karamci, inda akayi musu masauki da kayan abinci' mallam ne zaune da babban mallaminsa isma'il maiduguri"" yana fayyace mishi matsalan dake tafe dasu akan nawwara"" sai daya numfasa sannan yace lallai rayuwar yarinyar nan yana cikin had'ari. amma
Table of Contents