Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Aljana Ce Ko Mutum Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

isha allahu nawwara matar kace INA ji ajikina. sameeratu zaune adakinta ita da khadija, tana bata labarin abunda abbanta yace mata, khadija tace sameera me kika gano cikin maganar abba, na lura abba yana son na mijin dazai rike mishi ke sosai kuma ya kauna ce ki, shiyasa yace kije kiyi tunani. hakane Indai wannan AI nasamu, tunda ga Yusuf yana matukar sona hakane, yauwa nawwara nikam ya zancen maganar nawwar ne, nawwara tace ni Sam na manta da wani nawwar ma. khadija ta kalleta da kyau tace sameera inda zakiji ta tawa ni aganina, duk duniyar nan babu mai sonki kamar nawwar, shi yafi dacewa da yazamo mijinki, ki kalla fa irin kasadan da yayi adalilin sonki, ya kamata kixau na ki duba zancena. sameera tayi shiru kamar mai tunani, sai alokacin ta tuna da katin numbern wayan daya bata, ta sauke ajiyar zuciyarta, Allah dai yashige mana gaba amin, cikin mafarki sameeratu taji kamar ana ce mata. sameeratun nawwara karki yada soyayyar da nawwar ya miki kimishi halarci, shine masoyinki na asali, mai kaunar ki, mai tausayinki, kuma shine mijin da iyayenki suke son ki aura ki daure ki amshi soyayyar sa, don yanxu haka yana cikin wani hali kitaimaki nawwar dan Allah. tayi saurin bude ido tana dube dube cikin tsoro ta kudundune tana addu'a. nawwar zaune a asibiti ya samu sauki Mimi na bashi abinci abaki tana mai hira yana dariya, Mimi tace hamma dan Allah ka daina dumawa in Allah y yarda sai ka auri aunty sameera, yayi murmushi, yace Allah ya yarda yar kanwata. ansaka ranar auren nawwara da Yusuf sai shirye shiryen biki akeyi, abun mamaki kuma Sam nawwara bata zumudin yin auren Yusuf din , hankalinta na kan nawwara. tana son sake ganinshi don tasan halin dayake ciki, SBD tana tayawan mafarkai mafar kai, duk ta sukurku ce. biki sai matsowa yakeyi nawwar kuma ya warke amma har yanxu yana tunanin nawwara, kuma gabanshi na yawan faduwa, addu'oi kawai yasa gaba. yau jumma'a ya kama ranar auren sameeratun nawwara da Yusuf, wajen daurin aure ya Tara mutane da dama ga ustazai ango Yusuf sai washe baki yake. *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN *Nusnim* *PYAR* [1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* 7⃣6⃣➡8⃣0⃣ Ango Yusuf sai washe baki yakeyi, yayin da abangaren amarya ji take kamar tayi hauka saboda bakin ciki, jitayi bata son auren"" hankalinta y karkata kan nawwar. tana son ta kuma sashi a ido kafin akaita dakin aurenta, khadija ne ta dafata tace lfy nawwara kike irin wannan tunanin? tun da'zu nake miki magana amma hankalinki ya tafi wani wajen, gashi baki shirya ba kuma kin San ana sauko Daga daurin auren abokanan ango wajenki za su zo. sameeratu ta sauke ajiyar zuciya tace khadija kin San Allah Sam bani son auren nan da da yadda zanyi Dana warware auren, vaki galala khadija ta bita dashi cikin mamaki. tace nawwara kinsan me kike fada kuwa anya kina cikin hankalin ki kuwa?bafa auren dole ake miki ba, ke kika zaba mijin da kanki, ko kin manta ne, nawwara tayi murmushin da bai kai ciki ba, tace tabbas ni nazabi Yusuf daya zama mijina amma kuma yanxu Sam bani sonshi , hankalina y karkata kan nawwar, ina son Insan halin dayake ciki khadija. sai ga hawaye yana gangaro a idanunta, ni ban San meke damuna ba, da nayi tunanin Yusuf shi yadace da rayuwata, sai Daga baya nagane, nawwar shine mijin dayafi dacewa dani, shine mutumin daya kaunace ni tun fil azal, har gida ya biyu ni, yana rokon barar soyayyata, ayayin da idonshi cike da hawaye, muryar shi adaushashe. kalma na karshe daya furta min yace nawwara koda baki aureni ba, bazan taba daina sonki ba har abada, taci gaba da kuka , tace khadij sai yanxu nasan ina son nawwar fiye da yadda kike zato, amma ina lokaci yakure, nayi Dana sanin da banta bayi arayuwata ba khadija. takara fashewa da kuka, khadija na lallashinta da ban hakuri, dakyar tasamu kanta har tashirya, alokacin kuma abokanan ango da shi angon sun isu har an daura aure. Abangaren nawwar kuma tunda aka daura auren nawwara gabanshi ke fadi sai addu'oi yakeyi, duk kan su suna zaune afalo suna hira Mami da nawwar da sulaiman da Mimi, duk sunsha ado, Mimi tace hamman na yace na'am autar Mami, yau zan maka wani kyauta Dana Dade ina son in maka, yace Allah ko,. eh mana ko bakaso ne, me zai hanani son kyautar da autar mu zata min sai suka saka dariya, yauwa hamman nah, shiyasa nake sonka, amma menene goron albishir dina, yace duk abunda kike so zan baki. tace ko menene natambaya zaka bani , sosai ma, to shikenan Allah y kaimu anjima, Mami yaya sulaiman duk kuna shaida ko, suka ce muna sheda Mami tace Mimi yau yaushe zaki fitar mana da mijinki mugani , cikin shagwaba Mimi tace kai Mami dudu du nawa nake, amma koda yake nayi sabon saurayi very soon zaku Ganshi, sulaiman yace Allah yashirye ki Mimi Sam baki da kunya, agaban mu kike wannan zancen. cikin shagwaba mimi tace hamman kana jin yaya sulaiman ko, yi hakuri rabu da sulaiman yana kishi ne din jiya budurwar shi tace bazata auri mai gemu ba sai ya aske, duk kan su suka kwashe da dariya. karfe biyar na rana inda za awuce da amarya gdan angonta dake kaduna , bayan iyayenta sun mata nasiha sosai tayi kuka rabuwa da iyayenta jitakeyi kamar ta gudu, da zainab kanwarta akatahu da khadija sai aunty sauda da kanwar baban su. sun iso Kaduna lfy Inda aka wuce da amarya gdanta dake malali halliru dan turo, gdan da aka kai amarya ya basu mamaki, gdane tsararre komai nashi dadai, amma kuma basuyi zaton yasuf yana da kudi hakaba, SBD dan makaranta ne shi. baki an vasu dakin daza su kwana ita kuma amarya tana dakinta tsakiyar gado sai sheshshekar kuka takeyi, tana bakin cikin kasan cewarta haka amatsayin matar Yusuf. Mimi ce tace hamman kai fa muke jira sulaiman ma yashirya Mami tace nikam wai ina zaku hakane, wlh Mami wani waje zamuje, sai ga hamman ya fito cikin tsadacciyar shadda Wanda Mimi ta dinka mishi sai kamshi yakeyi, yafito a fillon shi saf, duk kansu sunyaba da kwalliyarshi, don yayi kyau, kamar wanda baida damuwa. hon din mota sukaji awaje awwal ne shima yazo dashi za atafi, dukkan su suka fito haraban gdan , suka shiga muta suka wuce, hon sukayi mai gadi ya bude musu suka shiga cikin gdan, nawwar mamaki ne yacika shi, inane nan kuma, Yusuf ne da abokinshi suka karaso cikin murna suka tarye su, yayin da aka masu ISO cikin gda. mimine tace hamman dina kaga wancen dakin to kashi ga kyatar Dana maka yana ciki , dan Allah ka isa ga kyautar nan hamma n kuma kamin alkwarin zaka karba kyautar nan. yayi murmushi me hade d mamaki yace ya amince, yakarasa wajen daki gabanshi sai faduwa yakeyi, yabude dakin tare da sallama, nawwara dake kan gado taji gabanta ya fadi don bazata iya manta muryannan ba, icon nawwar ya sauka akan abunda ya hango kan gado yana mamaki yakarasa wajen batare da ta dago ba, kirjinshi na

Table of Contents

Chapters

14 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});