Chapter 8
Chapter 8
insha Allahu komai zai daidaita zata dawo yadda take da izinin Allah, nan mallam yasa aka kawo mishi nawwara sam takasa hada ido dashi""yayi mata magana bata amsa shiba" d'aya daga cikin almajiransa yakira yace yad'au kasko yasamo garwushin wuta acikin gida" garin hantiti yad'ibo yazuba acikin kaskon, yamik'ama nawwar man jeedah y'ar saudiyya' yace yashafa mata a fuska" dakyar nawwar yasamu yashafa mata" da taimakon awwal dayarik'e mata hannaye" mallam isma'il yasa aka kira mai sauran malaman dasuke karatun dasu". yatashi yahada magani misk habbatus sauda da zaitun sai man ta farnuwa, da kuma gayen magarya duk yahada waje daya, sannan ya karanto addu'oi ya tofa aciki, ya umurci wasu malaman dasu sake riketa dakyau, ya matso yashafa mata a fuska da kafafuwanta" wani irin uban k'ara sake tana fizge fizge, tace mallam kusakeni kada ku kasheni, ni ban zamto daga cikin jinsin bil adama ba, niba jin___bata karasa ba sai ta fadi sumammiya, zoben dake hannunta yana fitar da hayaki, nan take yakoma launin ja, sai alokacin ne mallam ya hango zoben, yasa hannunta acikin wani kokon magani don cire zoben" da kyar zoben yafita. amma kuma me zai faru ana cire zoben sai sukaji kara acikin zoben kamar ana cewa kar Ku karasani tuni mallam yasaka shi cikin wani kwalbar magani ya narke , juyowar dazasuyi gareta kuma sai sukaga halittan nawwara yacanxa, bakaman da datake ruwa biyu ba, yanxu ta dawo asalin nawwararta. awwal yace mallam yanxu duk asirikan dake jikinta sun karye kenan, yace a'ah da sauran kadan dama babban matsalan itace wannan zoben, shine karfin asirin , yanxun kuma mun cire shi alhamdulillah, jira muke ta farfado sai ad'ora da ruqiya"" ameenatu Bini saifulla dake gefe, tace lallai babu abun bautawa da gsky sai ubangijin mu Allah, yanxu da ayoyin Allah akacire wannan zoben mai karfin tsafin, kuma anriga da angama halaka wannan zoben da me zoben wato gimbiya sameeratu. yanxu saura sarki gulmiyanu da mukarrabansa' dan bazai ta6a yafewa ba" gwara ma a halakasu duka, don muma musamu yancin kanmu da yadda zamu bautama ubangijinmu Allah , _Allahu sami'ul Aleem_. duniyar aljanu kuwa afadan sarki gulmiyanu' masarautar su tana girgixa yayin da wayanxu suka fadi suka mutu, saboda wannan zoben da aka kona , gininsu sai zubewa kasa sukeyi yayin da ruwa yacimma masarautan, suna neman ceto, sarki da kiyara da ambar suntsira da kyar, sarki yace ankona zoben nan shiyasa wannan abun ke faruwa, cikin huci ambar yace baza su yarda ba sai sun d'au fansa" kiyara tace mu koma jikin nawwara mudagargaza naman jikinta,munakasa ta tareda duk wanda keson ganin bayan mu, sarki yace haka za ayi.ta kalli ambar cikin 6acin rai" tace ai duk laifin kane' badan ka nuna kana sontaba aida tuni mun dad'e da mance shafinta" can kuma kowa ya bude alqur'ani donyin karatu sai sukaji ihun nawwara tana cewa wayyo zasu kasheni, ameenatu tace mallam kuyi kutaimaketa zasu kasheta wlhy,tunda hartayi silar tarwatsewar komai nasu bazasu barta da rai ba" nandanan suka fara karatu sosai, su sarki dasukaga za a kona su, sai suka fara cewa zamufita karku kona mu, itako ameenat cewa take mallam kuci gaba kada kubarsu azzalumai ne basa yafiya' zasu iyayin abinda yafi wannan idan aka barsu" duk yadda su sarki da ambar sukaso fita sun kasa' sbd yadda d'akin gaba daya yake warin magunguna ga kuma ayoyin Allah dake fita abakin manyan malaman cikin sauti" karatu suke har sai da suka tabbatar dasun konasu kurmus, sannan suka daina. ita kuma ta fadi kasa kamar matatta ,mallam yace alhamdulillah komai ya daidai ta ankona su, yanxu kawai mujira muga yanayin tashinta, ameenatu, tace mallam mun gode sosai yanxu ni zanyi tafiyata duniyar mu, tunda komai y daidai ta, idan nawwara ta farka agaisar min da ita, ta juya ta kalli nawwar da awwal tayi musu murmushi tace musu saduwar alkhairi, nawwar kari ke nawwara da amana, duk da dai nasan ayanxu idan ta farfado baza tasan waye kai ba, bazata tuna komai akan soyayyar da kukayi ba, amman nasan kai d'in jurumine, adalilin sonda kake mata ka tsamota daga aljanu zuwa asalinta (mutum) ka saida rayuwarka donka ceto abar sonka "" jarumtarka ta burgeni, sai dai kash ina mai tausaya maka saboda yanxu zaka sake shiga cikin wata jarabawar so' dan asalin nawwara bata soyayya' hasalima duk wanda yace yana sonta to daga ranar yazama makiyinta' don acewarta haryanxu bata had'u da namijinda yayi dai² da ra'ayinta ba" koda ta farfad'o yanxu batasan da soyayyar kaba, ba lalle bane ta amince maka, sai dai nasan kaid'in mijine wanda za'a kira dasunan namiji acikin jaruman maza" kayi hakuri da duk abinda zai biyo baya' inshaAllah komai zai dai²ta take anan nawwar yaji gabansa ya fadi' idanu yazaro cikin wani sabon tashin hankali" gumi tako ina ajikinsa........ _kutara agaba donjin anya nawwar yana daga cikin tsarin mazan da nawwara take so kuwa._ *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN *Nusnim* *pyar* [1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* 5⃣1⃣➡5⃣5⃣ gumi yake tako ina ajikinsa' innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai yake nanatawa a zuciyarsa, ameenatu tace nabarku lafiya cikin amincin ubangiji, cikeda kewar nawwara da tausayin nawwar ta tafi, ganin yadda duk ya d'aga hankalinsa akan abunda tafad'a masa" nawwar dake zaune cikin matsanancin damuwa kasa amsawa ameenatu sallamar data keyi musu yayi' sai tunanin zuccin dayake" anya zai iya jure rashin nawwara a kusa dashi kuwa? dan ba karamin illa soyayyarta yayi masa a zuciya ba; awwal ne ya dafa shi, yace kar kadamu abokina, insha Allahu kana cikin tsarin irin mazajen da nawwara zataso, kuma da yardar ubangiji sai kasamu soyayyar ta. uhummmm to Allah yasa' amman awwal na tabbatar da kaddara ce tafado min, kowani dan adam da kalar tasa kaddarar, fatana ubangiji ya kawomin agaji acikin al'amarina, awwal yace hakane doctor Allah ya shige mana gaba Ameen. nawwara dake kwance tasoma motsi alamun tashi kenan, awwal ne ya lura da hakan , da sauri ya ta6a nawwar yace kalla kaga tana motsi' barin kira mallam, su duka biyun suka shigo , mallam yace karku damu zata tashi da kanta, yana gama rufe baki, nawwara tayi mika tare dayin salati, bud'e idon dazatayi sai taga bak'in fuskoki akanta tsaye' tayi saurin waro idanu, tace nashiga uku lafiya naganku adakina, nan tafara laluben Neman hijabinta don ta kulle jikinta. karaf sukayi ido hudu da nawwar wanda yaji gabanshi yafadi, ita kuma tace mallam lafiya katsura min ido sai kace kaga sabuwar halitta? cikin tsiwa take maganar, cikinsa ne ya murna alamun kamar zaiyi zawo, nan kuma ta saki kuka tana kiran hajiya hajiya nashiga uku wasu mutane adakina' dan Allah kuyi hakuri kufitar min a d'aki" mallam yayi murmushi yace alhmdllh lallai kam sauki yasamu, sai ta juya ta kalli mallam da alamun tambaya abakinta, sannan kuma takara duban dakin data ke"" taga ashe ba gidan su bane, sai ta fashe da kuka, tana cewa ina ne nan kuka kawoni, mallam yace yi hakuri sameeratu baki da lafiya ne shiyasa, yanzu dai kitashi kiyi wanka ki canza kaya sai in miki bayani," batare data musa ba tace to, mallam yace dasu nawwar da su fito subata waje. mallam yakira yar uwarsa da ta taimaka mawa sameeratu tayi wanka, tace to
Table of Contents