Chapter 6
Chapter 6
mallam yayi sallama , suka amsa nawwar yanuna mai waje ya zauna" duk suka gaisar da malamin. saida mallamin yayi doguwar addu'a sosai sannan ya bukaci ameenatu bin saifullah data bayyana wacece sameeratun nawwara" kowa ido yazuba mata donson jin abun da zata fada, tace Allah y gafarta mallam sameeratun nawwara takasan ce ajinsin_____? *kubiyoni agaba* don jin me zai faru. *EDITED by UMMEE* *ADNAN* TAKU A KULLUM UMMU RUMAN *KUYI HAKURI DAJINA SHURUN KWANA 2 HAKAN YA FARUNE ASANADIYYAN LALACEWAN WAYAR TAWA AMMAN YANXU ALHMDLLH KOMAI YA DAI²TA* *nusnim* *pyar* [1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* *By* *Nusnim* 3⃣6⃣➡4⃣0⃣ A hankali *Ameenatu bintu saifullah* tace Allah ya gafarta mallam hakika sameeratun nawwara ta kasance acikin jinsin bil adama gaba da baya, awwal ya zaro ido, yayi saurin cewa kina nufin asalinta mutum ce ba aljana ba? tace tabbas mutum ce ba aljana ba, nawwar da nawwara sai kallon aminat suke cikin mamaki da d'aurewar kai. Nawwar yace ameenatu munaso kifad'a mana tayaya sameeratu tazama aljana" alhalin kuma kince asalinta mutum ce, daman mutum na rikid'ewa ya koma aljan? ta dago ido ta kalli mallam da baice dasu komai ba sai kallonta yake hana nazarin wasu abubuwan" ta juya takalli su nawwar da suka zuba mata ido suna jiran amsarta, sannan ta maida kallon ga sameeratu data matsu taji ko ita wacece' dafata tayi ,tace karki damu yau zakiji asalinki" kuma zakiji ko suwaye iyayenki. 🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹 *shekaru bakwai* *da suka wuce* 🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸 Akwai wani bawan Allah me suna Alhaji idrisa da matarsa hajiya maimuna, dukkan su haifaffun garin kano ne, Alhaji idrisa dan kasuwa ne kuma Allah ya hore mashi arziki, babban danshi na mijine me suna muktar, sai nabiyu mai suna isma'il sannan na uku macece mai suna sauda sai abba, sameeratun nawwara sannan zainab, yayanshi biyar kenan ukun sunyi aure , sai yarage daga sameeratun nawwara sai zainab. sameeratun nawwara yarinya ce me hazaka sannan tana da kyanta daidai gwargwado, tsakaninta da kanwarta zainab babu wani jaa, don ba ayaye sameeratu ba aka samu cikin zainab. gidan Alhaji idrisa babba gida ne, daya gada ga iyayensa" gidan hade yake d gdan gona, ko ta ina acikin gdan akwai bishiyoyi, kama daga bishiyar mangwaro, kashu, Tsamiya, dalbejiya, zogale, kukan Fulani, da dai sauran su"" lokacinda sameeratu na karama mamanta kan shimfida taburma da yamma sai ta ijye nawwara akai ita kuma tana aiki ga kuma tsohon ciki datake fama dashi, da haka sameeratu take gangarawa cikin wayannan bishiyoyin tayita wasa da y'ay'an aljanu, duk mahaifiyarta bata sani ba, dan duk sanda ta gama aiki tazo d'aukarta, zata isketa a inda ta barta" da haka yarinyar tasaba dasu, yakasance duk lokacin dabata je wajanba ta dinga kuka kenan, tun mahaifiyarta na hanata har ta kyaleta. akwai wani rana da ake meeting na aljanu, wacce shugaban aljanu itace *gimbiya sameeratu* ta garde akan kujeranta na sarauta kowa na girmamata, ga kayan marmari anjere mata agabanta, alokacin ne hajiya maimuna ta ijye nawwara agefenta don tayi sallar magriba afalo, tafara sallah bada dadewa ba nawwara ta rarrafa tafito waje har ta Isa wajan da aljanun suke taro ba su lura da itaba, sai dataje daidai kusa da gimbiya sameeratu, sukayi ido hudu, abunka da yaro sai nawwara tasakar ma gimbiya sameeratu dariya, itama ta maida mata tare da daukan nawwara tabata kayan marmarin dake gefenta, tundaga lokacin gimbiya sameeratu taji tana son nawwara, alakacin ne ambar yaji shi bawadda yake so aduniya irin nawwara. dahaka dai nawwara tashiga ran aljanu, amma tana karamanta ne take ganin su, data fara girma sai sukayi kamar sunbarta , alhalin basu barta ba, Alhaji idrisa yasa ansare duka bishiyoyin gdansa inda yatada Gini aciki, sare bishiyoyin nan bakaramin tashin hankali ya afku a duniyar aljanu ba" don alokacin daza asare bishiyoyin gimbiya samiratu tana kwance tana hutawa, abun ya afka da ita daidai tsakiyar cikinta aka sare, sai yatsar ta mai duke da wani shegen zobe mai kyau yafado kasa, daidai saitin dakin nawwara" . anan rai yayi halinsa, duniyar aljanu sungirgixa da mutuwan gimbiya sameeratu, sarki gulmiyanu yayi takaicin rasa yar'uwar shi da sauran aljanun su," mutumin dayasare bishiyar ba ayi kwana biyu ba yarasu , mutane suka fara jita jita akan cewa ai bishiyan daya sarene agdan Alhaji idrisa na aljanune, kuma ba shakka su suka kashe shi, kuma daman sai da akace ma alhjy karyasa asare don dadewar bishiyoyin , yace shi sam bai san da wasu haittu aljanu ba, kuma koda akwaisu badai a gidansa ba" bayan mutuwan gimbiya sameeratu da sati daya, nawwara ta tsinta wannan zoben gimbiya akofar dakinta, taji yabata sha'awa tasaka a hannunta, ya mata kyau sosai. suko can duniyar aljanu sun kudirta aniyan raba alhaji idrisa da farin cikin shi kasan cewa Allah ya daura mai son nawwara, gashi yarinyar akwaita da haddan alqur'ani akanta,tana zuwa islamiya sosai. tun lokacin data sa zoben nan taji kamar bata da lafiya, kuma tayi rauni akaratunta, tun mahaifiyarta namata fada har tagaji takyaleta, ikon Allah kuma babu wanda ya ta6a lura da zoben hannun ta. akwai wata rana taje islamiya taji sam takasa zaman ajin duk ranta abace yake kuma tarasa dalili' tashi tayi tafita waje tasamu wuri ta zauna' me zai faru kawai sai jitayi ance sameeratun nawwara kitaho gareni zan yaye maki damuwarki' zan baki duk wata kulawa data dace ke tamuce har abada, a tsorace take waige² bataga kowa ba" mikewar dazatayi saiga___? *EDIDTED by UMMEE ADNAN* TAKU UMMU RUMAN *nusnim* *pyar* [1/11, 4:39 PM] +234 806 448 1931: *ALJANA* *CE* *KO* *MUTUM* *By* *Nusnim* 4⃣1⃣➡4⃣5⃣ Mikewar dazatayi saiga maciji yayi saurin bi ta kafafunta, tasaki wani uban ihu tare da sumewa kasa , nan take yan makaranta suka rufa mata, aka kira mallamin su, yasa yan ajin sanawiya su dauke ta sukaita aji. yasa aka kawo mai ruwa a kofi yayi addu'oi aciki ya watsa mata fuska, a firgice ta farka tana cewa gasunan suna kirana, wayyo Allah zasu..... mallam yayi saurin cewa suwaye ke kiranki nawwara? kasa magana tayi ta tafi suuu zata fadi aka tare ta, shugaban makarantar ne yazo, yace yana ganin alamar jinnu ne ajikin yarinyar nan" ayimata ruqiya agani idan aljanun ne za'a gane" mallamin su yace hakane don nima nayi tunanin haka. nan aka shiga yiwa sameeratun nawwara ruqiya , nanda nan aljanun suka bayyana ajikinta, alokacin ambar ne ajikinta, abisa umurnin mahaifinsa dayace yasoma bayyana gareta " don ya isar musu sakon dasuke dashi. mallam yace kai waye' kuma me kuke nema awajen wannan baiwar Allah'n, me tamuku kukeson cutar da ita? shuru ambar yayi' mlm yace zakuyi mgn kosai na kona ku da ayar Allah, cikin wani irin murya da babu dad'inji ambar yafara magana "" yace mallam kar ka kona mu zamu fita dama sakone muke son isarwa ga mahaifinta" kiransa zakayi mufad'a masa ko kai zamu barwa sakon ka isar gareshi!" mallam yaga idan yace akira mahaifin nawwara ana iya d'aukar lokaci, ga yarinyar nabuk'atar taimakon gaggawa" tunda sunce zasu iya bada sakon aba mahaifinta ai shikenan' yace wace irin sako ne! kafad'a zamu isar zuwa gareshi" ambar yayi wata irin dariya tukum sannan yace ciki tsawa mallam muna so afadama mahaifita zamu dauke sameeratun nawwara zuwa duniyarmu...... mallam yace wa'iyazu
Table of Contents