Chapter 9
Chapter 9
zube a gaban sarkin fulanin yankin jimo, daga kallon da ake musu yasa suka sha jinin jikinsu, da kyar garkuwan fulanin yankin kwana ya ce "Allah ya taimaki Sarki Haruna, da fari kafin muce komai zamu fara da ban hakuri da neman afuwa da gafarar duk wani wanda yake wannan yanki a kan rashin jarman macizai! Haqiqa munji kunya! Mun yarda munji kunya! Amma ba laifinmu bane, mai afkuwa ce ta afku, amadadin Sarkin fulanin yankin kwana da Arɗo, da mai unguwar yankin kwana wato Ori, dani Garkuwan fulanin yankin kwana da Magaji Bawa da duk jama'ar da suke yankin kwana muna mai neman yafiyarku a kan abunda ya faru na rashin jarman Macizai! Haqiqa ya cika jarumi kuma ya amsa sunansa, ba zamu manta da halaccin wannan yanki ba har izuwa karshen rayuwarmu! Mun gode da yunkurin taimakonmu! Haqiqa mu abun tausayi ne, kuyi hakuri ku yafe mana! Bai kai ga aiwatar da aikinsa ba muka iske gawarsa da saran maciji, ba zamu iya kawo muku tashin hankali goma da ashirin bane, shi yasa muka sallacesa muka binnesa muka yi masa sutura, zaku iya zuwa ganinsa tare damu gobe idan Allah ya kaimu sai muje ku ga ƙabarinsa!" Garkuwan fulani ya karasa maganar a sanyaye yana mai duƙar da kai. Tabbas jama'ar yankin jimo sunji mutuwar jarman macizai har can kasar zuciyarsu yayinda suka ji tsanar yankin kwana duk da hakika sun tausaya musu matuƙa, amma zafin mutuwar jarman macizai ya hanasu ce uffan wasu Garkuwan fulanin yankin kwana, ba a wani musu tarba mai kyau ba dan kuwa su na cikin ƙunci da jimanin mutuwar jarman macizai, inda suka sa da washe gari da safe zasu yi asubanci su tafi yankin kwana. @@@@@ *YANKIN KWANA.* Ko da su Aziza da Azima suka koma gida ba su shiga hidimar juna ba, harta abinci da Hajja ta haɗa musu ga mamakinta sai gani ta yi sun raba kwano, sosai abun ya damu Hajja ta yi musu tambayar duniya me ya hadasu, Aziza ce dai ta iya cewa babu komai fa Hajja, amma Azima kam ko kallon Hajja bata yi ba. @@@@@@ Bayan anyi sallar isha'i dukkansu suka hallara a fadar mai unguwa, kowa da kalar shawarar da yake badawa, shi dai Baffa duk sauraronsu yake yi ya gaza cewa kanzil, inda a karshe Arɗo ya ce "Magaji in ce dai lafiya ko? Na ga kowa na ta magana amma kai baka ce komai ba" ajiyar zuciya Baffa ya sauke ya ce "Hankalina yana can wajansu Garkuwan fulani, ko ya Haruna zai dauki lamarin? Abun fa sai wanda ya ɗaure" Ardo ya ce "Tabbas haka ne Magaji, to ya zamu yi? Mu ma ba yin kanmu bane, Allah yasa su fahimce mu" aka amsa da amin, tsohon sarkin fulani ya ce "Yanzu abun duba a nan shine taya zamu shawo kan wannan matsalar? Abun kara yawa yake yi fa? Jarman macizai da safe! Yaro dazu! Ba zamu zauna mu naɗe hannu a kirji mu zuba ido a shafe mu ba, mai zai hana mu aika da kokon barar mu neman taimako yankin tudu?" wani zabura Baffa ya yi yana girgiza kai ya ce "A'a Baffa Mandi, kar mu kara wannan kuskuren! Munyi kuskure na farko an rasa jarman macizai, yanzu kuma sai mu sake aikata wani ta hanyar yin aike yankin tudu! Mu nemi taimakon IRO MAGANIN MACIZAI? Duk shawaran da za ayi a sauran yankuna amma banda yanki biyu, ban da yankin tudu ko yankin ja'i, kar mu taro wani yaƙin ba tare da mun dakatar da wani ba, kun san tsananin gabar da ke tsakanin yankin tudu da yankin ja'i da yankinmu, har kwanan gobe ana samun kisan kai a tsakanin yankin nan da yankin ja'i, har kwanan gobe yankin tudu su na riƙe da abunda ya faru sun kasa mantawa kiris suke jira su fasa abunda yake zuciyarsu, dan Allah ku fahimceni!" Shuru wajan ya dauka kowa da abunda yake tunani, Sai zuwa can anjima Mai Unguwa Ori ya ce "To shikenan, za ayi ƙuri'a duk bangaren da ya fi rinjaye shi za a zaba, idan bangaren kar aje neman taimako yankin tudu ko yankin ja'i sunfi yawa to ba za aje ba,idan kuma bangaren wa inda suka ce aje sunfi yawa to za a je" shi dai Baffa shuru ne ya yi yana hango musu gagarumar balbalin gobarar yaƙin da zai tashi amma sun kasa ganewa. 🍃🍃🍃🍃 COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN. [3/21, 12:29 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 🙇🏻♀️🙇🏻♀️🙇🏻♀️🙇🏻♀️🙇🏻♀️ *WANNAN DUƘAWAR NAKI NE SISINA, DAN ALLAH KIYI HAKURI KI HUCE KINJI🙇🏻♀️😟 KAR AYI MANA DARIYA, ALLAH YA HUCI ZUCIYARKI🥰 AMEENATUNA SLIMZY BABY🥰 MATAR MIJINTA🥰* *FREE..* 🅿️==1️⃣1️⃣↪️1️⃣2️⃣ Da washe gari asubanci yankin jimo suka yi, takwas na safe su na yankin kwana,a maƙabarta jikin ƙabarin Jarman macizai, kuka sosai sarki Haruna yake yi shi da jama'ar yankinsa wa inda suka zo, an sha musu mutuwa amma farat ɗaya na Jarman macizai wanda yake jarumi a yankinsu ya gigita tunaninsu, haka suka ƙarashi koke-kokensu suka gama dan ba dawowa zai yi ba, haka jamar'ar kwana suka taru ƙwansu da ƙwarƙwatansu suka sake yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da ban hakuri, daga fuskarsu kawai zaka kalla ka gane su na cikin mugun damuwa da tashin hankali, babu yadda yankin jimo suka iya dole suka hakura tunda dai Jarman Macizai ba dawowa zaiyi ba ya tafi kenan, sai dai fatan Allah ya yafe masa. @@@@@ Bayan kwana biyu an gama ƙuri'u, inda aka samu sab'anin ra'ayi, jama'ar da suka fi rinjaye shine wa inda suka ce aje yankin ja'i neman taimako kar aje yankin tudu a fara zuwa yankin ja'i, dan ba za a zauna da matsala ba tare da an bukaci taimakon Allah da wa inda zasu shawo kan matsalar ba, shi dai Baffa shuru ya yi bai ce kanzil ba, haka aka sa mai rubuta wasika ya rubuta aka yiwa yankin ja'i aike da shi. 🍃🍃🍃🍃🍃 Sarkin fulanin yankin ja'i na zaune Maga Isar da Sakon yankin ya zo ya zube a gabansa yana fadin "Allah ya taimakeka! Hakika a yau nasara tamu ce" wazirin fulani ya ce "Maga Isar da Sako meke tafe da kai ne?" murmushi Maga Isar da sako ya yi ya ce "Hakika yau muke da nasara, sako ce ta isko mu daga yankin kwana! su na cikin bala'i shine suke bukatar taimako daga yankinmu, yanzu haka ga takwabi sarkin kwana wato Chubaɗo ya aiko mana da shi alaman sun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27