Chapter 5
Chapter 5
kike tunani zai faru Aziza?" "Ban sani ba!" Aziza ta faɗa a ƙufule ta yi gaba, ita ma Azima a macijiya ta hau bin bayan Aziza, yau tsananin takaici ya hana Aziza ta cewa Azima ta koma mutum, Azima kuwa da gangan take wani abun dan Aziza ta mata magana. A macijiya ta shiga gidan Allah ya so Hajja na bandaki, zama Aziza ta yi ta buga tagumi, Azima kuwa bukka ta shige, bayan Hajja ta fito ta ga Aziza da tagumi ta ce "Ah Aziza kun dawo?" shuru Hajja taji dan Aziza ta yi nisa cikin tunani, sai da Hajja ta tabota tukunna ta dawo hayyacinta ta ce "Na'am Hajja magana kike yi ne?" "Tunanin me kike yi haka Aziza?" murmushi Aziza ta k'wak'ulo ta ce "Abunda yake faruwa a mahaifana shine yake tayar min da hankali Hajja" "Karki ce zaki saka hakan a ranki,addua ita ce mafita,duk abunda ya yi tsanani maganinsa Allah" kuka Aziza ta fashe da shi ta rungume Hajja ta ce "Dole ne na saka a raina Hajja! Idan mun san abunda ya faru yau ba bamu san me zai faru gobe ba Hajja!" sosai Aziza ke kuka yayinda hankalin Hajja ya tashi, Azima ce ta fito daga bukka dauke da abinci a hannunta zama ta yi ba tare da ta kalli Hajja ko Aziza da ke kuka ba,abincinta ta hau ci hankalinta kwance, Hajja ta kalli Azima wacce ta jima da gane ita damuwar wani bai dameta ba, ta ce "Azima meke faruwa da yar uwarki!?" Cikin halin ko in kula ta ce "Oho mata! Tana son ɗorawa kanta damuwar da bata da mafita a kansa, ta ga zata iya ne, Hajja ki daina damun kanki a kanta!" Hajja zata yi magana sai ga Baffa a fujajan ya shigo ko sallama babu, da sauri hankalin Hajja da Aziza ya koma kan Baffa akasin Azima da ta yi kamar bata san da shigowarsa. "Baffan yan biyu lafiya kuwa na ganka a cikin wannan yanayin?" Sharce zufa Baffa ya yi ya ce "Jumala ina kuwa lafiya! Ku zo muje gaban gari ana neman dukka mutanen yanki, kin san an kashe Jarman Macizai kuwa?" hannu Hajja ta zuba a kirji tare da fadin "Ma'asabumin Musibati qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! An kashe jarman macizai to waye kashesa!?" " *MACIJI! SARAN MACIJI NE A JIKIN JARMAN MACIZAI!*" Baffa ya faɗa yana sauke idonsa a kan Azima wanda hankalinta sam baya kansu, Hajja ta ce "Ba ri na dauko mayafina mu tafi gaban gari din" Hajja ta karasa maganar tana shigewa bukka, Aziza kuma tana gyara mayafin kanta hankalinta a tashe! Baffa ya ce "Ke Azima? Ana gaya miki mahaifarki babu lafiya amma kina zaune hankalinki kwance ba tare da kin nuna damuwarki ko a fuska ba kina cin abinci! Za ki tashi ne ko sai na saka sanda na roɗe miki shingen kafafunki nan masu kama da fuffuken sauro!" Baffa ya faɗa yana yin kan Azima da sauri ta tashi tana huci tare da juya baya, hanyar randar kasan dake tsakiyar gidan taje ta ɗibo ruwa a kwarya tare da fakan idon Aziza ta watsa dafi a ciki, sannan ta juyo tana kallon Baffa a ranta take fadin "Ba zan taba samun salama ba idan har ban kasheka ba!" tunkaro Baffa ta yi har ta zo gabansa tana tura baki ta ce "Baffa na ga alama kan ka ya dau zafi kaɗan sha ruwa zuciyarka ta huce! Baffa ita fa damuwar duniya bata karewa barin ma idan mutum yasa hannu ko nace mutane suka sa hannu suka jawo bala'i wa kansu, sannan dole akwai abunda ku ka aikata ma wasu yake bibiyarku! Dan haka Baffa a koma a yi tunani da kyau, ga ruwan ka sha" ta mika masa tana sunkuyar da kai kasa sai kace wata ta Allah, shuru Baffa ya yi yana son yayi tunani a kan maganar da ta fada amma tashin hankalin da suke ciki ya ƙi basa damar haka, hannu yasa ya karbi ruwan caraf idon Aziza ya sauka a kan ruwa ta hangi dafi, cikin azama ta ce "Baffa wani ruwa kuma zaka sha? Ka manta Azima ita bata damuwa da damuwar wani? Kawo ruwan nan Baffa" Aziza ta karba, wani kallo ne Azima ta bi Aziza da shi jikinta har na tafasa tsananin takaicin abunda Aziza ta yi, Aziza na karban ruwan da gangan ta yi tuntube ruwan ya b'are kwaryar kuma ta riɗata da dutse ta fashe, cije baki Azima ta yi, idonta ya kara rinewa tana shirin tunkaro Aziza wacce itama ke kallonta ko gizau bata yi ba, Hajja ce ta kara katse mata hanzari ta fito tana fadin "Yi hakuri Baffan yan biyu! Na zubar da wake ne na tsaya kwashewa shiyasa ban fito da wuri ba,muje" gaba Baffa ya yi Aziza ta bisa a baya, Azima ta zo fita Hajja ta ce "Ina mayafinki?" "Ba zan saka ba! bana jin saka wa Hajja! Raina a b'ace yake karki min maganar wani mayafi!" daskarewa Hajja ta yi jin amsar da Azima ta bata,ita ma Azima bata san lokacin da ta faɗi ba dan bata taba yiwa Hajja magana haka ba,ganin Hajja ta tsaya tana kallonta ne yasa ta cewa "yi hakuri Hajja bara naje na dauko,kuyi gaba zan zo a baya" Hajja dai bata iya cewa komai ba illa bayan su Baffa da Aziza da ta bi wanda sun yi gaba abunsu. Su na kan tafiya Aziza ta ce "Baffa?" "Na'am Aziza yaya ne?" "Baffa baka taba bani labarin kafuwar mahaifata ba, kullum kana cewa an sha gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma baka taba bani labarin kalar gwagwarmayen da ku ka sha dasu ba" "Yo to banda abunki Aziza ana cikin wannan tashin hankali kina maganar labari? Abunda ya kafu sama da shekaru hamsin? Ki bari Allah ya bamu ikon dakatar da wannan ambaliyar wutar masifan dake tunkaro wannan yankin" shuru Aziza ta yi ba tare da ta sake magana ba, da haka har suka karasa gaban gari inda cincirindon fulani suke tsaye kowa ka gari hankalinsa a tashe, har anyiwa jarman macizai jana'iza an binnesa. Ana ta shawaran yadda za a rubutawa sarkin fulanin yankin jimo sakon cewa an kashe jarman macizai wanda yankuna sun san shi jarumi ne, idan ka cire yankin ja'i da yankin tudu za a iya cewa babu wani jarumi wanda ya shahara a kama macizai sama da jarman macizai, amma a yankin Ja'i akwai wanda har aljanun macizai yana kamawa tsananin shahararsa wanda har laƙabi ake masa da INNU MACIJI, daga shi kuma sai na yankin tudu wanda shike takawa Innu Maciji baya wato IRO MAGANIN MACIZAI daga shi sai wanda aka kashe na yankin jimo wato JARMAN MACIZAI, lokacin da aka raba kambun girma na wa inda suka shahara a kama macizai aka ba wa INNU MACIJI lamba daya, aka ba wa IRO MAGANIN MACIZAI lamba ta biyu sai kuma JARMAN MACIZAI lamba ta uku, har ta Ilu mai Macizai da Azima ta kashe na yankin kwana shine aka ba wa lamba ta shidda, sannan aka rabawa na ƙasa dasu, tashin hankalin da yankin kwana ke ciki shine rashin jituwar da basu da shi da yankin tudu da yankin ja'i, barin ma yankin ja'i tsatstsauran gaba ce daɗaɗɗiya, dan kuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27