Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Aziza Da Azima Macizai Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

warware mana wannan sarƙaƙiyar" Sarki Chubaɗo ya ce "Kowa zai iya kama gabansa" Da kaɗan-kaɗan aka fara watse wa, Arɗo da Baffa Mandi da Baffa ne suka fara tafiya, Baffa Mandi ya ce "Amma na rasa me yasa Magaji kake yawan maganar Banju" Baffa ya ce "Sabida ni kaɗai nake ganin abunda nake gani a gidana" yana gama faɗin haka bai jira amsarsu ba ya yi gaba, Arɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Mandi, akwai abunda yake damun Magaji" Baffa Mandi ya ce "Nima haka nake gani, amma anya baya da nasaba da yaransa da ake yawo dasu ake zarginsu kuwa? A gaskiya Magaji ya yiwa yankin kwana hidima bai kamata a dinga masa haka ba" "Gaskiya kam hakane" tafiya sukeyi a hankali suna tattaunawa, Baffa kuma hanyar gida ya ɗauka. 🍃🍃🍃🍃 Zaune ta sameta a rafin jimulo, ita ma zama ta yi kusa da ita ta ce "Azima tambayarki na zo yi" "Wai ni Aziza me yasa kika rainani ne? Ba nice gaba da ke ba?" murmushi Aziza ta yi ta ce "Au haba dai da gaske? Rainin babu dadi ne? To haka iyayenmu suke ji a ransu idan kika musu, balle ni da ba ki bani ko da kwana daya bane, kawai iskar duniya kika rigani shaƙa" Azima ta kyalkyale da dariya ta ce "Macijiya Aziza me ya kawo ki wajena?" Kallonta Aziza ta yi ta ce " ZAREN SAƘAR DANA! WA ZA KI KASHE DA SHI!?" sake kyalkyalewa da dariya Azima ta yi ta ce "Idan naki faɗi fa me zakiyi?" "Sai na gwada ta wata hanyar!" Aziza ta faɗa tana mikewa tsaye, da sauri Azima ta mike ta ce "Muje zuwa" tana gama faɗi ta hau ajijiya, Aziza na tsaye tana kallonta. 🍃🍃🍃🍃 COMMENT AND SHARE BY MOMYN AHLAN [3/21, 12:31 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️ *KASSH! WLH ALLAH TAMBAYAR NAN TA ISHENI! TUN BAN SO NAYI MAGANA BA AMMA INAJI DOLE NAYI YAU DA MANYAN HARUFA! FISABILILLAHI MUTUM NA GANIN ABU DA IDONSA AMMA A ISHENI DA TAMBAYA MARAR AMFANI! (BOOK DIN NA KUƊI NE? SANNAN NAWA?KO KUMA AU DAMA NA KUDI NE?) HABA DAN ALLAH! TUN A FARKON SAMAN PAGE NA RUBUTA NA KUƊI NE NAIRA ƊARI KACAL DAN MASOYANA, KI DUBI ALLAH IDAN KIN SAN BA ƊARIN ZA KI BIYA BA KI DAINA KIRANA KO TURO MIN SAƘON CEWA KINA BUKATA BA DAN NI BA DAN ALLAH,👏🏻 MAZA KUMA MASU DAUKAR LAMBATA KU MIN MAGANA MAY BE TA FACEBOOK NE,KU MA KU DUBI ALLAH KU DAINA KARKU JAZA MIN MAGANA, GRP DINA BABU MAZA👏🏻* *MASU CEWA CMPLT SUKE SO, ABUNDA KO SATI INAJI BAN KAI DA FARA SAKIN BOOK DIN BA, YANZU NAKE TYPING DINSA.* *SANARWA* _WA INDA BASU BIYA KUƊIN KARATUNSU BA, SU KOKARTA SU BIYA NAN DA KWANA UKU, SABIDA NA BUƊE PAID GRP YAU, SANNAN FREE PAGE ZAI IYA YANKEWA NAN DA KWANA UKUN IN SHA ALLAHU, DAGA NAN ZAMU ƊORA NE DAGA PAID GRP, BANA SO AYI WANNAN CAKWAKIYAR BABU KU DAN CAKWAKIYA BA A MA YI KOMAI BA😊 KU DAI KU BIYONI DA NAIRA ƊARINKU DAN KUJI YADDA ZATA KAYA A CIKIN LITTAFIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, NGD MASOYANA MASU NUNA MIN ƘAUNA_😊🤙🏻 *FREE..* 🅿️==1️⃣5️⃣↪️1️⃣6️⃣ Bata motsa ba, har Azima ta gama hajijiyarta, ta girgije ta zama macijiya daga ƙasanta, ta ce "Mu gwada mana Aziza, yau inaji da abunda ba ki ji" murmushi Aziza ta yi ta ce "Dan kin saƙa zaren dana shine kike tunanin zaki iya dani? Kawai cewa nayi ki faɗa min wanda za ki kashe da shi, idan ba haka ba na gwada ta wata hanyar" sosai Azima ta haɗe rai fuskarta ya fara komawa blue ta ce "Idan zakiyi kawai kiyi! Bana son magana a baki sai dai a aikace!" Azima na gama faɗi ta daga hannunta ta huro wuta, Aziza na tsaye na kallonta, sai da Azima ta gama hura wutar ya yi jajur sannan ta yi wani gurnani ta hurawa Aziza, Aziza na ganin yadda wutar ya nufota ta yi tsalle ta haɗa wani farin hayaki ta maidawa Azima abunta nan ya sameta patttt! A ƙirji! Zubewa ƙasa ta yi tare da komawa mutum, a hankali Aziza ta zo gabanta ta ɗurkusa tana shirin yi mata magana taji yankan wuƙa a kafadarta ya shige, kafin ta farga Azima ta yi mata kafa ta nausheta a ciki nan ta faɗi kasa numfashinta nayin sama, Azima kuma ta miƙe tana dariyar mugunta gami da cewa. "Gaskiya bana da burin kasheki yar uwata, amma ya zama dole ko dan na kammala aikina a kan lokaci! dan zaman wannan dajin ya isheni ina da bukatar shiga gari, to amma idan kina raye taya burina zai cika? Ba ki san ta yadda akai na samu zaren saƙar dana ba taya kuwa zan gaya miki wanda zan kashe da shi!? To ba zan faɗa ba! Yanzu kuma idan na kasheki bani da wata sauran damuwa a rayuwata ko abunda zai dinga kawo min cikas da burina!" Duk maganar da Azima ke yi Aziza na jinta yayinda hannunta daya tana riƙe da kafadarta da yake zubar da jini dayan kuma yana kan cikinta da Azima ta yi mata naushi da kafarta, tsoronta daya shine Allah yasa wuƙar da Azima ta yanketa da shi babu zaren saƙar dana a jiki, idan hakane yana nufin Azima zata yi b'arna? Idan ta kasheta zata kashe sauran mutane sannan ta shiga cikin gari ta tarwatsasu? Inaaa! Hakan ba zai yu ba, dole na dakatar dake ko ta wace hanya! To amma me zanyi yanzu? Aziza take tambayar kanta mafita, Azima kuwa na tsaye ta juyawa Aziza baya tana ta zuba kamar indararo, wata zuciyar ta cewa Aziza "Kin manta ba zaku iya kashe juna ba? Amma ke zaki iya kashe Azima! Duba Taurarinku dake haɗe ke kaɗai aka yarjema wa dan ki gani da mai zaki dakatar da Azima" a hankali Aziza ta miƙe ta kama bishiya ta ɗan jinginu, ta lumshe ido, nan ta hau gane-gane, tabbas ba zasu iya kashe juna ba amma zata iya karyawa Azima kwarin guiwa, sannan wukar da ta yanketa da shi babu zaren sakar dana a jiki, Aziza na ganin haka tasa hannu ta shafe inda Azima ta yanketa nan wajan ya koma kamar ba a taba saka ma shi wuƙa ba, sannan

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});