Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Aziza Da Azima Macizai Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

an sha gasan kisa a tsakani, yankin tudu kuwa dan sarkin yankin ne ya zo yankin kwana ya yiwa yar yankin fyaɗe bai kyaleta ba har sai da ya kasheta! Hakan ce tasa ARƊO ya bada umarnin a kashesa shi ma,aka gille masa kai aka turawa mahaifinsa da shi daga nan gabar ta soma, yanzu taya zasu fara neman taimakon Yankin Tudu ko kuma yankin ja'i? Yanzu dai ba shi bane tashin hankalin, tashin hankalinn shine yadda zasu fara tunkaran yankin jimo da sakon an kashe jarman macizai. @@@@@@@ Su Baffa sun iso ana kan shawara ba a tsaida mafita ba, sai da Baffa ya karaso aka sake yin shawara a kan a rubuta sako a tura mutum huɗu da suje yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da rigan Jarman Macizai wanda yake jina-jina da jini, sannan ayi musu bayanin abunda ya faru bai kai ga yin aikin da yazo yi ba aka iske gawarsa, tare da sakon ban hakuri iri da kala daga wajan mai unguwan yankin kwana da kuma sarkin fulanin yanki kwana tare da Arɗo, hakan ce ta kasance aka tura mutum huɗu izuwa yankin jimo, tare da kayan Jarman Macizai da kuma dokinsa da takwabinsa. Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita. Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba. Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce "Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha'i za a zauna ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu" da sauri Baffa ya ce "Arɗo yankin tudu kuma?" "E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan" "To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja'i" Nauyayyiyar ajiyar zuciya Arɗo ya sauke ya ce "To Magaji mai zai hana kai ka maida hannun agogo baya?" "Bangane ba Arɗo?" "Ina nufin ka dawo yadda kake a da dan mu taimaki yankinmu, Kayan aikinka da kaje ka binne kaje ka hakosu saboda......" girgiza kai Baffa ya hau yi yana ja da baya, ya ce "A'a Arɗo na riga da nayi alkawari ba zan sake ba, har kwanan gobe ban manta da kuskuren da na aikata bisa tsautsayi a baya ba, abun shekara ashiri amma a yanzu gani nake yi yanzu abun ya faru, Arɗo ba a son raina na kashe *BANJU* ba, na kashesa ne sabida shafe mutanen yankin nan da ya fara, sannan idan baka manta ba yace zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan! tunda na kashe Banju nayi alkawari na dai na! duk wani abu wanda na gada daga gareka da kakanni! Dan Allah Arɗo a bar wannan maganar" 🍃🍃🍃🍃🍃 WLH IDAN NAYI POSTING A GRP BAN CIKA BI TA CIKIN GRP DIN BA,AKWAI WASU GRP DIN MA BANA BUDEWA INDAI BA GOGE SAKONNI ZANYI BA, IDAN KINA SON BIYAN KUDIN BOOK DIN NAN KI TUNTUBENI TA LAMBAR WAYATA TA SAMA, IDAN TA ACCT NE KO KATI. AND PLS&PLS 4 ALLAH'S SAKE, IDAN KIN SAN BA BIYA ZAKIYI BA KARKI KIRANI KI GAYA MIN MAGANAR DA BA HAKA BA, A BOOK DIN NAN DAI BAN CE DARI BIYAR KO DARI UKU BA,HAR TA DARI BIYU MA BANCE BA, DARI NE NACE DAN MASOYANA,BAN SAKA TA INDA BA ZAKI IYA BIYA BA, SO PLSS A DINGA FAHIMTA,DAN WATA MAGANA JIYA BAI MIN DADI BA SAM.👏🏻 MASU KIRA NA DAN KARA MIN ƘWARIN GUIWA NA GODE,NA SAN ZAKU GANI DIK DA BAN SANKU BA AMMA KUNA RAINA🌹🤝🏻 COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN [3/21, 12:28 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *JINJINA GAREKI SIRKATA MAMAN NOOR, 😍 SANNU DA COMMENT,INAYINKI OVER.* *FREE..* 🅿️==7️⃣↪️8️⃣ Shuru Arɗo ya yi yana kallon Baffa na wasu lokuta kafin ya ce "Shike nan Magaji, ba zan takura maka ba, amma ban yi tsammanin zaka tsorata da maganar Banju haka ba" "Ba tsorata nayi da maganar Banju ba a lokacin da ya faɗi, amma a halin yanzu ina cikin zullumi na maganar Banju, dan idan baka manta ba ya ce zamu gani ko ba jima ko ba daɗe sannan kuma zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan, abunda yake faruwa a halin yanzu abun a duba ne, sannan bamu san wani martani sarkin fulanin yankin jimo zai maidowa mutanen da suka je ban hakuri garesu ba, ba kowa bane zai lamunci hakan, munyi aiken neman taimako anzo dan a taimaka mana amma kuma sai a mai da musu da kaya ace an kashesa! Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!" Baffa ya faɗa fuskarsa dauke da zallar damuwar da yake ciki, Arɗo yaja ajiyar zuciya ya ce "Ko ma miye ne idan suka dawo ma ji, yanzu dai ka je amma ka tabbatar bayan sallan isha'i ka halacci fadar mai unguwa" "In sha Allahu zan zo" daga haka suka yi sallama, Baffa ba hanyar gida ya yi ba dan ba gidan zai koma ba illa cewa da ya yi su Hajja da Aziza su koma gida, ina Azima bata zo ba? Aziza ta ce "Eh Baffa bata zo ba" girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Hajja da Aziza suka dauki hanyar komawa gida, su na tafiya su na hira, Hajja ta ce "Ohh Allah ni Jumala, ko me ya hana

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});