Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Aziza Da Azima Macizai Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rabin gashinta ya sauko ya rufe mata rabin fuska wanda ya sake hana asalin kyawun nata fitowa sosai a gani,kafarta babu takalmi, a hankali ta bi mai kama macizai wanda aka kashe da kallo, ranta a b'ace ta juya a hankali tana tafiya dukkan sassan jikinta yana lankwasawa, a yadda take taka kasa da ka ganta kasan bata yi maka kama da cikakkiyar mutum ba, daji ta yanka ta shiga cikin korayen bishiyoyi inda zata samu yar uwarta kawai take hari, can kusa da wani rafi mai sanyi da dadin kallo ruwan fari k'al da shi abun sha'awa taja ta tsaya, bata ankara ba taji saukan wani zureriyar wutsiyar maciji🐍, ko kaɗan hakan bai tsoratata ba, tunda ita ma macijiyar ce, d'aga idonta ta yi saman bishiyar da wutsiyar macijin ya sauko mata, ta kalli yar uwarta wanda dukkanta macijiya ce,a hasale ta ce " *AZIMA!!?* me yasa kika son kashe mutane kwanan nan ne kam?" macijiyar da aka kira da Azima a hankali ta sulalo daga saman bishiya ta kanannaɗe yar uwarta tana lasarta da harshe, hannu dayar tasa ta ture kanta a macijiyar, sannan ta ce "Azima tambayarki fa nake yi?" gefe ta koma ya yinda ta saki wani huci ta girgije nan ta zama rabi mutum rabi macijiya, daga ƙugunta abun da ya yi sama mutum ce, daga kugunta abun da ya yi ƙasa macijiya ce. Dariya ta sheƙe da shi cikin wata murya mai amo da rashin dadin sauraro, sai jijjiga take yi tana naɗe jelar macijinta ta ce " *AZIZA!* bana mantuwa kuma bana yafiya!! Duk wanda ya shiga gonata sai na hallaka shi, sai na ga bayansa ko ma waye! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Dan haka bana bukata ki din ga tuhumata akan abun da kike da masaniya a kai" "Amma Azima kisan ya yi yawa! Da an miki laifi kaɗan sai kisa? So kike yi sai an gano mu ba mutane bane macizai ne mu a kore mu a gari?" Rintse blue eyes dinta Azima ta yi sannan ta buɗe tana zaro harshenta suffan na macizai sak ta ce "Ina so na bar wannan alk'aryan, ina so na shiga cikin gari wanda yake da al'umma da yawa ta yadda zan tarwatsa su!" girgiza kai Aziza ta yi ta ce "Ke nan za ki iya tafiya ki bar su Baffa da Hajja?" "Me zai hana Aziza!? Ina da burin shiga cikin jama'a masu yawa duk da na san ni din ba mutum ba ce!" "Shigarki jama'a ba alkhairi bane Azima, dan haka ki bar wannan maganar ki zo mu tafi gida kar mu koma mu samu Baffa ya dawo ya titsiye mu da tambaya daga ina muke, amma dan Allah ki koma mutum tun daga nan" Aziza ta faɗa tana yin gaba, dariya Azima ta yi a madadin ta zama mutum kamar yadda aka ce mata sai ta rikiɗe ta zama katuwar macijiya mai sheƙi da ban tsoro, ko da Aziza ta juya ta ganta a haka girgiza kai ta yi, ba tare da ta ce mata uffan ba. Sai da suka kusan isowa gida kafin ta girgije ta zama mutum, yadda yar uwarta Aziza ke tafiya haka ita ma take tafiya, mayafinta da ta ajiye ne kusa da gida ta dauka ta yi irin lullub'in da yar uwarta ta yi, su na yin wannan lullub'i ne saboda idanunsu da yake abun tsoro barin ma kwayar idon Azima blue, ita kuma Aziza idon mage mai fari-fari, ko kaɗan basu da baƙin ido,shi yasa Hajja mahaifiyarsu ta basu su din ga lullubi, shi yasa idan sun yi lullubin suke saukowa da dogon gashinsu ta gefe ya rufe musu gefen fuska, ga shi dai alk'aryan duk fulani ne kuma kyawawa, amma duk fadin yankin kwana babu mace ko namijin da ya kai su *AZIMA DA AZIZA* kyau. Ko sallama basu yi ba suka shiga gidan suka iske mahaifiyarsu Hajja a jikin murhu tana aikin hura kara, Aziza ta ce "Sannu da aiki Hajja" dagowa ta yi ta kalli kyawawan yan biyun nata ta ce "Yauwa sannu Aziza, daga ina ku ke haka? Tun safe fa ku ka fice a gidan nan" "Amm Hajja muna rafin jimulo" murmushi Hajja ta yi ta kalli Azima wanda idonta yake kan garin Mahaifiyarta, haka kawai take ji ta watsawa garin dafi, Aziza ta ce "Hajja karan ya ƙi kamawa ne?" "Eh Aziza ya ƙi kamawa wallahi ga idona ya yi ja yana min zafi" "Ayya sannu Hajja bari na hura miki!" "Yauwa yar albarka hura min, Azima lafiya kuwa kika ƙurawa garin da zamu yi tuwo ido?" murmushi ta yi ta ce "Lafiya lau Hajja" girgiza kai Hajja ta yi ta duƙa ta shige bukka, ita kuma Aziza Hajja na shiga bukka ta rufe idonta ta rintse nan idon ya dawo ja, bakinta ta buɗe ta fiddo da turirin ta hura a murhu nan kuwa ya kama da wuta, Azima kuwa wajan garin ta je ta bude bakin tana shirin zuba dafi sai ga sallamar Baffa, da sauri ta mai da harshenta, amsa sallamar Baffan suka yi tare yi masa sannu da dawowa ya amsa, fitowa Hajja ta yi,ita ma ta ma sa sannu da dawowa tare da shinfiɗa masa tabarman kaba, ya zauna, Aziza ta ɗiba masa ruwa ta kawo masa, sannan suka zauna dukkansu. Sai da Baffa ya sha ruwan sannan ya saki ajiyar zuciya, cikin fulatanci Hajja ta ce "Baffan Azima da Aziza lafiya kuwa?" "Ina kuwa lafiya, wannan alk'arya ya kafu tsawon shekaru sama da hamsin, anyi gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma a yanzu bala'in da yake tunkaro wannan alk'arya ya yi yawa, ina wannan shahararren mai kama macizai din nan, Ilu Mai Macizai?" Hajja ta ce "Eh na ganesa,waye bai san Ilu mai Macizai ba" "To shi ma an kashesa yau" salati Hajja ta sa tana tafa hannu ta ce "Hande in bone ni Jamila, yanzu shi ma Ilu mai macizai an kashesa?" "Eh har ma anyi masa jana'iza an binnesa, ga shi duk macizan da ake kamawa babu wanda bakinsa ya yi dai-dai da saran da ake samu, ga shi yanzu har zargi ya fara shiga tsakanin mutane da mutane, yanzu haka mai gari ya yiwa Jarman Macizai aike da wasiƙa,kin ganesa?" Hajja ta riƙe hab'a alaman tunani ta ce "Jarman Macizai ba wannan na yankin al'karyan jimo ba?" Baffa ya ce "Eh shi dai, ya ma amsa da gobe zai zo, zai taho da ruwan wani magani wanda za a ba wa kowa ya sha wanda hakan ne zai bayyana waye ba mutum ba a cikin al'umman yankin kwana, kin san titsiyeni aka yi a kan su Azima da Aziza, wai yarana basu abu irin na mutane, shi ne za ayi wannan gwajin" wani firgita Azima har ma da Azizan suka yi, suka kalli juna, ba tare da iyayensu sun san halin da suke ciki ba,tuni idon Azima ya kara komawa blue sosai, nan ta kalli fatar jikinta ta ga ta fara zama blue da sauri ta miƙe ta shige bukka, ita ma Azizan tashi ta yi, Hajja ta ce "Dan kawai yara basu mu'amala da kowa, sannan idonsu ba baƙi ba shikenan sai a saka mun yara a gaba?" Baffa ya ce "Amma kin san dai har da

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});