Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Aziza Da Azima Macizai Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a ranta ta ce "Inno Fandi! Yau inaso ki bani abunda kika sha miƙa min ina ƙin karba,ko ta wace hanya ce ina so na dakatar da Azima,ina so na san wa zata kashe da zaren saƙar dana dan na basa kariya,duk da zuciyata tana zargin Baffa Azima take son kashewa! Amma ita baka iya tunanin abunda zatayi dan komai ma zata iya yi! Inno Fandi yau ina so ki bani" Aziza a ranta take magana idonta a lumshe, wata farar tsohuwa ce fara sosai tsohuwa tukuff ta bayyanawa Aziza tana murmushi ta ce "Wani lokaci domin tsaida zubda jini! Muma sai mun wanke hannayenmu da jini! Magaji Bawa ya ajiye baiwarsa yayinda ya binnesa, na zabi shiga jikinki dan taimaka miki ke da mahaifinki a lokacin da na hango bala'in da zai faru a rayiwarku bayan an haifeku, Magaji ya yi tunanin binne baiwarsa zai ce wannan yanki ta yi sanyi, amma kashe Banju shine babbar bala'i ma wannan al'karya dan yace zai dawo, ba zaki iya jin komai a bakina ba Aziza dan alƙawarin da muka yiwa Magaji cewa daga bakinmu wani nasa ba zai ji tahirinsa ba sai dai idan shine ya bayar, sabida alkhairin da Magaji ya mana ba zan manta da shi ba, hakika Magaji Bawa jarumi ne, Aziza wannan abunda zakiyi ba ƙaramin yaƙi bane wanda ke daya ba zaki iya yi ba,ni kuwa bazan iya tayaki ba, amma ga wannan ki ɗora shi a ɗamtsen hannunki zai taimaka miki sosai,sannan karki taba rabuwa da shi dan wani sirhitaccen karfi ne, duk sadda kike bukatar taimakona ki kirani zan zo!" tana shirin b'acewa da sauri Aziza ta ce "Inno Fandi! Jejin lore! Ina so naje" zaro ido Inno Fandi ta yi ba tare da ta yiwa Aziza magana ba ta b'ace, a hankali Aziza ta buɗe ido ta kalli Azima wacce har yanzu take tsaye take magana a kan zata kashe Aziza. Ɗora zaren da Inno Fandi ta bata ta yi a damtsen hannunta sannan ta juya baya ta rintse ido nan fatar jikinta ya hau sab'ulewa alama ce na zata koma macijiya, nan ta zama wata katuwar macijiya🐍fiye da yadda take zama a da, fara sol sai kyalli take yi, Azima dake ta zuba tin dazu bata san abunda ke faruwa a bayanta ba, sai bayan da ta gama maganarta na karshe da fadin "Sai fa hakuri! Amma yau za ki mutu! Ni haka nake! Muguwa ce ni! Ban san sani ba! Ban san sabo ba!" tana gama faɗi ta juyo dan cakawa Aziza wuka nan ta ga babu Aziza, ɗaga kan da zata yi ta hangi kanta a can sama, Aziza ta zama katuwar macijiya mai cike da tsoro da firgici, da mugun tsoro Azima ta ja da baya tana fadin "Ya haka?" bata ankare ba ta ji anyi sama da ita an yi kasa da ita, kafin ta girgije ta ji an dauketa ana zagaye iska da ita, sai da aka wujijjigata sosai sannan aka yi wulli da ita, faɗuwa ta yi ta bugu. Buɗe baki Aziza tayi a tana macijiyar🐍ta hau yiwa Azima ruwan macizai🐍 su na fita suna saren Azima, sai da ta cikata da macizai sannan ta koma mutum tana tsaye tana kallon Azima wanda macizai ke sara, Azima ta kasa tabuka komai, da taji jiki taji tabbas zata iya mutuwa ita kuwa ba zata yarda ta mutu ba tare da ta dauki fansa ba yasa ta ce "DAN ALLAH AZIZA! KI KWASHE MACIZANKI! ZAN GAYA MIKI WANDA ZAN KASHE!" jin haka yasa Aziza ware hannu ta janyo macizan sannan ta b'acer dasu, tana janyesu Azima ta zube kasa a galabaice, Aziza ta ce "Gaya min! Wa za ki kashe da zaren saƙar dana?" " *BAFFA*" Azima ta faɗa cikin muryan galabaita, saurin ja da baya Aziza ta yi ta ce "Baffa?" Da jan ido a tsawance Azima ta ɗago idonta ta watsasu a cikin na Aziza ta ce "Eh Baffa zan kashe da zaren saƙar dana! Ban san wani irin kalar baiwa Baffa yake da shi ba, amma abunda na sani shine duk wata hanyar guba da nabi dan son kashesa duk basu aiki! Tun ina gwada kashesa a boye har na fara bayyanawa kika sani! Bincikena ya nuna min cewa zaren saƙar dana ne zai kashe Baffa wanda da shine ya......." maganar da Azima bata karasa ba kenan Aziza ta wanketa da mari, za ta kara Azima ta riƙe hannun Aziza ta ce "Karki kuskura idan ba haka ba a yau din nan wannan al'karya zata koma toka, kodayaushe kina nuna min karfin dafi da baiwar da kike da shi, ga taken kalmata ta karshe wanda kika sani Aziza, *IDAN KIN ISA KI DAKATAR DANI!*" miƙewa tsaye Aziza ta yi ta ce "Na yarda da maganarki Inno! Domin tsaida zubda jini! Dole ne muma sai mun wanke hannuwanmu da jini! Ke dodon mutan yankin nan ne da Baffa ko Azima? To ki sa a ranki ni nice dodonki, dakatar dake kamar na yi na gama" dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce "Muje zuwa, ai ba a buga komai a wasan ba! " ba tare da Aziza ta sake magana ba ta bar wajan, a hankali Azima ta miƙe ta b'alli gashin kanta tsili ɗaya ta hura wani hayaki a jiki sannan ta haɗiye nan inda macizan Aziza suka sareta wajan ya koma ya yi fess sannan ta dauki hanyar gida, Aziza kuwa ba gida ta yi ba, dan bata ga ta zaman gida ba,dole ne taje jejin lore dan lalata zaren sakar dana in ba haka ba kuwa Baffa da sauran jama'a zasu mutu. 🍃🍃🍃🍃 A tunzure ta zo shiga gidan, amma jin maganar da Baffa da Hajja ke yi ya sakata maqalewa a jikin zana tana sauraronsu, Hajja ke faɗin "Innu maciji kam ina da sa rai a kansa sosai, zai iya kawo mana karshen wannan matsalar da yardan Allah, tunda yana gwagwarmaya da aljanu, a goben zai zo?" "In sha Allahu! Haka suka ce zai zo a gobe, amma a gaskiya da a so samuna ne da bamu nemi taimakon yankin ja'i ba sam wollah, karki so ki ga izgilancin da suka mana a cikin wasikarsu kafin su amince da bukatar yankin nan" Ajiyar zuciya Hajja ta sauke ta ce "Koma miye tunda sun amince shikenan Allah ya shiga mana gaba! Idan kuma tsohon gaba ne yanzu kuma ta kau ai, tunda yankin kwana ta duƙa musu" girgiza kai Baffa ya yi ya ce "Jumala! Ba shi bane abunda nake hange! Idan wani abu ya samu Innu Maciji ko da ƙwarzani ne to fa! Sabon yaƙin da ba ayi ba kwanakin baya shi za ayi yanzu! Duk inda ake neman rashin hakuri masu jiran sammacin yaƙi idan aka samu yankin ja'i to an kai karshen magana, mutanen da jira suke a tab'osu ko kaɗan ne su yiwa mutane cin mutunci, meyasa gabanmu dasu yafi tsanani? Ina sabida yankin kwana taƙi daukar cin mutunci ne, amma al'ummar yankina sun kasa fahimtar abunda nake gaya musu, idonsu ya rufe da neman mafitar wannan bala'i shiyasa duk shawaran da zan basu, ba su gani inda a karshe ma laifi ne suke gani, suna ganin kamar zan iya wani abu a kai amma naki, duka so

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});