Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Aziza Da Azima Macizai Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,225 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zauna a rafin yau, ammm Hajja ga wannan ki sha" "Inji waye?" Hajja ta tambayi Aziza "Ba kowa nina haɗa miki sabida ciwon bayan da kike fama da shi" "Ayye Aziza ai naji sauki tun wanda kika bani kwanakin can" "E duk da haka ma ki sha wannan Hajja" ba tare da Hajja ta sake magana ba tasha, tana gama sha Aziza zata yi magana taji ana shelan kiran sallar magriba, hakan ne yasa kawai ta rungume Hajja wacce taji komai na kanta ya dauke, sun ɗau lokaci a haka kafin Aziza ta saki Hajja ta yi alwala ta gabatar da sallar magriba ta jima tana addua kafin ta tashi ta canza kaya ta ɗauki abubuwan da zata dauka ta kara da wa inda Inno Fandi ta bata ta fito ta fice a gidan kafin Baffa ya dawo, tana zuwa bayan zanar gidansu ta rufe ido nan ta b'ace b'atttt!!. 🍃🍃🍃🍃 Ko da Azima ta dawo gida ita ma shiri gwabzawa ta yi da Innu Maciji,dan ta lashi takwabin kashesa!. Hajja kuwa bata tambayi inda Aziza take ba. Tun tsawon dare Azima ta zama macijiya ta sulale a hankali ta fice a gidan, bata zarce ko ina ba sai tsakanin shigowa yankin kwana da yankin ja'i. 🍃🍃🍃🍃 HAHAH NA HADA MUKU DA PG DIN JIYA DA NA YAU, MUN RABU LAFIYA🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ COMMENTS AND SHARE by Mom Ahlan, macijiya🐍😂 [3/21, 12:31 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. Sanarwa. Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku. *IDAN AKA CE ƘAWANCE ANA NUFIN AMINTAKA! WANDA WANNAN AMINTAKAR WATA DANƘO CE MAI MANNUWA,ANA SAMUNSA NE IDAN AKA SAMU YARDA DA AMANA! IDAN NA KIRAKI DA SUNAN ƘAWATA BAI KAI INDA ZAN NUNA YADDA NAKE YINKI A CIKIN RAINA BA, HAKIKA MU DIN BA IYAKAR KAWANCE BANE,INAJINKI TAMKAR WACCE MUKA FITO CIKI DAYA,INA MIKI SON SO SABIDA ALLAH! ALLAH YA BAR MINKE ƘAWALLITA _RASHEEDAT USMAN UMMU NASMA&NASREEN_ ALLAH YA ALBARKACI ZURI'ARMU ALLAHUMMA AMIN, INA KU KE MAKARANTA? UWAR NASMA TA YUNƘURO FA A BOOK DINTA MAI SUNA _GELLE 'BINGEL_ WANDA ZAKU SAME SHI CIKIN FARASHI MAI SAUKI, KU NE ME NI TA LAMBATA DAN ISA GA FASIHIYAR MARUBUCIYAR KAI TSAYE, KARKU BARI A BAKU LABARI, SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*👐🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ _Follow me on wattpad,@Fateemah'0_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *FREE..* 🅿️==1️⃣7️⃣↪️1️⃣8️⃣ A wani ƙasurgumin jeji Aziza ta tsinci kanta, jeji mai cike da wani mugun duhu da abubuwan tsoro tare da wasu mugayen halittu marasa kyawun gani da ban tsoro, haƙiƙa ganin wa innan abubuwa sun tsorata Aziza, amma tunowa da maganar Inno Fandi da cewa kar ta tsorata yasa ta takure tare da tattaro jarumta, ta hau tafiya, tare da furta kalman "makarin zaren saƙar dana!" wani sowa ne taji na tashi ta tsakiyar kanta da wani irin mugun jijjiga nan wasu halittu suka yi sama da ita, saura qiris Aziza ta saki ihu amma kuma ta daure tana karanto dukkan adduar da ya zo zuciyarta, nan halittu suka dauketa suka kara yin sama da ita suka hau tafiya da ita a cikin duhu,amma duk wannan duhu ba shi ya hanata ganin mugayen halittu marasa kyau da ban tsoro ba. Wa inda suka dauketa basu ajiyeta a ko ina ba sai a gaban wani katon halitta wanda bata san dame zata fasalta halittarsa ba sabida tsananin muni da girmarsa, ana ajiyeta muryar wannan katon abun ya ce "Keeeee! Me ya kawoki jejin lore!!!" a yadda muryarsa take ɗan adam idan ya jita ya ci ace ya mutu tsananin amo marar daɗi da kaifi, cikin dakiya Aziza ta ce "Makarin zaren saƙar dana, shi nake so" shewa wannan halittar ya yi,sannan ya ce "Ya matsayinki yake a halittu!?" " *NI MACIJIYA CE!*" Aziza ta bada amsa, wannan halittar ya ce "Ke ba iyakar macijiya ba ce, akwai wani sirri a tattare dake, dan haka ko ba mu baki makarin zaren saƙar dana ba,kaifin gubar dake jikinki zai iya ƙonasa! Amma kasancewar sau daya tak! Muke bada alfarma zamu baki taimako guda daya, zamu ƙara miki karfi, da kinje ki hurawa zaren wuta ta idon ki zai ƙone ƙurmuss! Ga wannan" ya faɗa yana daukar wata kyakkyawar dutse mai cike da hasken gaske ya hura mata shi ya shige ta goshinta, abun na shiga jikin Aziza sai da ta girgiza ta yi kamar zata faɗi amma ta yi iyakar iyawarta bata faɗi ba,dama tana tsaye ne ita ba a sama ba ita ba a kasa ba, abun na shiga jikin Aziza nan ta kalli fatar jikinta ta ga yana sab'ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama dawowa hayyacinta tuni ta fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce "Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah" "To Baffa" Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta jima tana addua sannan ta tashi. Abu na gaba da zata yi shine daukar zaren saƙar dana taje ta kona shi, to amma abun tambayar a nan shine a ina Azima ta ajiyesa? "zaki iya dubawa ki gani ta tafin hannunki ai an baki karfi a daren jiya a jejin lore" wata zuciyar ta bata amsa da haka, da sauri ta buɗe tafin hannunta na dama tasa hannun hagunta tana shafe tafin hannun daman tare da lumshe ido, nan ta ga ashe ma a cikin kayanta Azima ta ajiye zaren saƙar danar, tasan tabbas Aziza sai ta binciko,kuma duk bincikenta ba zata duba kayanta ba tunda ba zata yi tunanin zata saka a ciki ba, da sauri Aziza

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});