Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Aziza Da Azima Macizai Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Azima zuwa? Ita kullum ta fi so ku ta zama a bakin zargi" "Ai ko basu zauna a bakin zargi ba, ba lallai bane yaranki su kasance mutane ne!" da sauri Hajja da Aziza suka juya su na kallon Mairo da Hadi wanda suka riƙe ƙugu sai kace zasu dake su, Hajja ta ce "Mairo me kike nufi?" "Oho miki kuma! Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, yara ko ma dai nace iyayen yara! Ace kamar su Azima da Aziza a wannan yankin gote-gote dasu amma babu aure! Sannan suna tafiya jiki na lankwasa! Daga mai idon mage (wato Aziza kenan) sai mai ido ruwan ganye(Azima kenan) taya kuwa zasu zama mutane, ga shegen kyau! Duk da lokacin da muka yi yan matanci dake duk yankin nan babu mai kyawunki sannan babu jarumi sama da Magaji, ba wai hakan yana nufin zaku haifi yara masu kama da mutanen wani duniya daban bane ehe! Ko ki so ko karki so Azima da Aziza dai ba mutane bane!" Idon Hajja ne ya kawo ruwa ta ma kasa magana, da kyar ta ce "Mairo idan ke kike aurar wa sai ki zo ki aurar dasu, sannan kuma idan kina canza halitta ki zo ki canza musu" caraf Hadi ta cab'e zancan da cewa "Wa ye bai sani ba, ba mamaki duk wannan kisan da ake yi a yankin nan Azima da Aziza suke yi, kuma da saninki ke kike daure musu....." "YAAAA ISAAAAAAAA!!!" Aziza ta faɗa da kakkausar murya, ganin yadda fuskar Mahaifiyarta ya jiƙu da ruwan hawaye, gaban mahaifiyarta ta tsaya yayinda idonta suka kara rinewa zuwa fari-fari ,yatsarta manuniya ta ɗaga tana nuna Mairo da Hadi cikin gargaɗi ta ce "Zan iya jure komai! Zan iya shanye komai! Amma kar na ga hawaye a idon MAHAIFIYATA SANYIN IDANIYATA! ku fita tsabgarmu! Mu mutane ne, maganar da kika fada yanzu kuma Inna Hadi ki bar shi a iya nan kawai kar yaje gaba!" Aziza na gama fadi ta kamo hannun Hajja suka bar su Mairo da Hadi jiki na rawa, Hadi ta ce "Mai....Mai...Mairoo....ban....gaya...miki....da...da..da cewa ba mutane...bane...wollah inaji ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba...kalli ki ga lokaci daya yadda idonta ya canza...anya ma ni kuwa ba su bane....." saurin dakatar da ita Mairo ta yi ta ce "Hadi ki bar maganar nan a nan dan ban shiryawa mutuwa ba, zo mu tafi" Mairo ta fizgi hannun Hadi. @@@@@@ Sun ɗan yi tafiya Hajja ta tsaya, Aziza tasa hannu tana sharewa Hajja hawaye tare da fadin "Kiyi hakuri Hajja, dan kuka mai ja wa uwa jifa ko Hajja!?" Aziza ta faɗa tana fashewa da kuka, Hajja ta ce "A'a Aziza, har ga Allah ni har zuciyata ban taba zargin yarana ba, na san ni dai mutane na haifa" "To me yasa kike kuka Hajja?" "Saboda dukkan uwa ta gari ba zata so a dinga sokin yaranta ba! Har raina nake jin zafi" Hajja ta fada tana mai kamo hannun Aziza, wani tausayin mahaifiyarsu ne ya ɗarsu a zuciyar Aziza, duk yadda take tausayawa kanta da yar uwarta tafi tausayin Hajja, ranar da zata gane cewa su din ba mutane bane MACIZAI NE ranar da zata san duk kisan da ake yi Azima ke yi, shin ya dace ta ci gaba da boyewa Hajja cewa su ba mutane bane? Ko dai ta fito ta gayawa Hajja da Baffa gaskiya? Kai amma kuwa gunduwa-gunduwa za ayi dasu, sannan Azima ta ce ko da ta faɗi ba shi zai hanata cika burinta ba! Girgiza kai Aziza ta yi ta sake rungume Hajja tana kuka, Hajja zata yi magana suka ji nishi na tashi ta gefensu wanda yake ciyawa ne kore shar a wajan, saurin maida hankalinsu suka yi, Aziza ta ce "Hajja kamar fa nishi nake ji?" "E nima naji Aziza, kamar ta nan yake fitowa zo mu duba mu gani" suka yanki gefen ciyawar, wani yaro suka gani kwance fuskarsa ta koma blue bakinsa sai fitar da farin kumfa yake yi tare da jini, salati Hajja ta saka, da sauri Aziza ta dagosa tana kallonsa tare da jinjigasa, gefen wuyarsa ta kalla ta ga saran maciji, wanda bata raba dayan biyun *AZIMA* ce, girgiza kai ta hau yi cikin tashin hankali, ta buɗe baki, Hajja ta ce "Aziza me ya faru da shi?" "Hajja maciji ne ya saresa, bari na gwada yi masa magani" kasancewar lokuta da dama Aziza na gwada wa Hajja kamar tana magani wanda Hajja ke danganta hakan da nasaban Baffa, bata jira Hajja ta yi magana ba ta hura iska a bakinta ta rufe ido gam na wasu daqiqu sannan ta buɗe, yayinda idon ya koma fari sol, hannu tasa a bakinta ta dibo farin yawu ta gogawa yaron a wuyarsa dai-dai shatin saran, sannan ta koma kallonsa, duk fuskarsa ta yi blue, tana saka masa ya hau gurnani yana murkususu sannan ya koma ya yi ɗifff! Hajja ce ta daga hannunsa ta ga ya koma, da sauri ta janye Aziza ta ce "Aziza zo mu bar nan wajan" Kallon Hajja Aziza ta yi cikin damuwa ta ce "Hajja taya zamu barsa bayan yana buqatar taimako,ki bari na taimaka masa Hajja kar ya mutu" "Ai ya riga da ya mutu Aziza! Ki zo muje kar ace kece kika masa wani abun" Suman tsaye Aziza tayi tun sadda Hajja tace ai ya riga da ya mutu, kallon yaron kawai take yi, hannu Hajja tasa ta ja Aziza da sauri suka bar wajan basu tsaya ko ina ba sai gida, suna shiga gida Aziza ta shige bukkansu bata ga Azima ba, duk yadda akayi tana rafin jimulo, hannu tasa ta goge hawayenta tare da daukar mayafinta, Hajja ta juyo zata bata ruwa ta ga ta fice a gidan da sauri Hajja ta bi bayanta tana fadin "Aziza! Ke Aziza!? Azi..." Hajja bata karasa ba sakamakon dakatar da ita da Aziza ta yi, ta rufe mata ido ta hura mata iska, haka kawai Hajja ta tsinci kanta da komawa gida, Aziza kuma hanya ta yanka ta yi rafin jimulo, a yadda take tafiya zaka gane cewa ba mutum ba ce, haqiqa yau Azima ta kai ta karshe! Me wannan karamin yaron ya mata da zata kashesa!. Tana isa rafin ta kwala kiran sunan Azima. "AZIMAAAAA!" sulalowa Azima ta yi hannunta dauke da mangoro fuskarta wasai, ganin fuskar Aziza ya sakata sakin baki dan bata taba ganin fuskarta a haka ba "MACIJIYA AZIZA LAFIYA!" Azima ta fada cikin halin ko in kula. "AZIMA ME YARON DA KIKA KASHE YA MIKI!?" kyalkyalewa da dariya ta yi ta ce "Sabida ya cancanci ya mutun ne, saboda ya ganoni, kuma yace sai ya faɗa kin ga kuwa dole na kashe sa tunda...." dauketa da mari Aziza ta yi, tana dagowa ta sake kai mata wani marin, ran Azima ya tunbatsa nan ta riƙiɗe ta koma macijiya,in da ita ma Aziza yau ta rikiɗe ta zama macijiya fara sol, nan dambe ya kaceme. 🍃🍃🍃🍃 WAI YAU MACIZAI NA FAƊA,NAYI NAN🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ A lallaba chaji wala🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ COMMENTS AN SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻 [3/21, 12:28 AM] Fatima: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨ (🐍 _Macizai ne_🐍) MALLAKAR. *ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)* SAHIBAR KAINUWA. *JINJINA GAREKI UWA BA DA MAMA, ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA, SHUGABA DAYA TAMKAR DA DUBU,(GWAGGOTA TA KAINA

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});