Chapter 8
Chapter 8
ALLAH YA IYA MIKI.* Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din 0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu. *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *MARUBUCIYAR.* 1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._ 2- _GUDU A JEJI._ 3- _SHUHADA._ 4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._ 5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._ 6- _COLONEL UBAIDULLAH._ 7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._ 8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._ 9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._ 10- _DA NA SANI NA._ 11- _BADAWIYYAH_ 12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_ Now 13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_ 🍃🍃🍃🍃🍃 *JINJINA GAREKI HAJIYA MAMAN YUSUF MAI KAYAN MATA😍 SAFIYAR YAU KECE KIKA FARA SAKANI DARIYA😂 DAN HAKA GA KYAUTAR PAGE HAJIYA JIRGIN DANƘARO*😂 *MAMIE'S CLUB HAKIKA SHARHINKU YA TAFI DA RUHINA, A KODAYAUSHE KUNA NUNA MIN E KU ƊIN YAN AMANA NE NA GASKEN-GASKE, AZIMA DA AZIZA FANS GRP, WLH KARKU YARDA A ZO GARINKU A FI KU RAWA AHA TO😜, DAN ARADU YAN MAMIE'S SUN CE BA ZAKU KAMO SU A SHARHI BA,KUMA NA YABA🌹🥰, A KAFTA*🤾🏻♀️ *ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA, YA ALLAH KA KARAWA SHUGABA JA GABA ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM DARAJA! DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA DA MAGOYA BAYA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO! HAKIKA AZIMA DA AZIZA YA YI FARIN JINI FIYE DA TUNANINA! ALHAMDULILLAH! MASOYA A CI GABA DA NUNA MIN ƘAUNA TA HANYAR SIYAN BOOK DIN NAN CIKIN FARASHI MAI RAHUSA, ƊARI KACAL*👌🏻 *FREE..* 🅿️==9️⃣↪️🔟 Dambe suke yi sosai a tsakaninsu ba ji ba gani, yayinda Azima ta yanki Aziza a gefen wuya,nan ta koma mutun ta faɗi kasa, ita ma Azimar rabi mutum rabi Macijiya ta zama tana kallon Aziza ranta a haɗe idonta ya kara rinewa zuwa blue, a hankali Aziza ta miƙe tsaye tasa hannu ta karkaɗe jikinta ta juya baya,ta sa hannu a gefen wuyanta inda yake zubar da jini ta lumshe ido, kamar ƙiftawar ido da bismillah ta shafe wajan, sannan ta daga hannunta sama ta haɗa wani guguwa mai karfin gaske ta turawa Azima, Azima bata ankara ba taji anyi sama-sama da ita, sai da taje can sama kafin ta faɗo timm! Da kasa nan ta koma mutum, a hankali Aziza ta juyo tana kallonta yau fuskarta babu fara'a, haqiqa dan faɗa su na faɗa amma basu taba dambe ba, bar su a cacan baki. Saurin tashi Azima ta yi ta sake komawa macijiya ta yi hajijiya ta tada ƙura ta yi kan Aziza, da sauri Aziza ita ma ta sake zama macijiya suka haɗe aka hau dambe, da jelarta na maciji ta nannaɗe wuyar Azima ta shaƙeta sosai, murkususu Azima ta hau yi tana son kwacewa daga hannun Aziza amma ta kasa, inda karfinta ya fara karewa dan duk muguntarta bata kai Aziza karfin dafi ba. Nan numfashinta ya fara yin sama inda a karshen jikinta ya sub'ale ta koma mutum sumammiya, ganin haka yasa Aziza sakinta ta wullata kusa da rafin ita ma ta koma mutum sannan tasa hannu ta dibo ruwa ta watsa mata a fuska, wani wawan ajiyar zuciya Azima ta sauke alaman ta sha wuya, da tari ta farka tana yunkurin tashi ta ce "Duk abun da zakiyi Aziza kema kin sani ba zaki iya kasheni ba!" Kafadarta Aziza ta kama hawaye cike a idonta ta ce "Nima bana fatar kasheki! Har na bar duniya bana fata na kashe ko da tururuwa! Azima kisan ya yi yawa! Azima me kikeson zama ne! Ga shi yau kin sani na aikata abunda bana son aikatawa wanda ban ma taba aikatawa ba! meyasa Azima! Me yasa! Me yasa!" Aziza ta karasa tana sakin kuka mai cike da ruɗani. Zufa Azima ta goge tana ture hannun Aziza daga kafadarta ta ce "Kullum ba zan gaji da faɗin cewa da ni ce da karfin gubarki da na shafe jama'ar yankin nan an wuce wajan! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Bana mantuwa bana yafiya!" A fusace Aziza ta sa hannu ta dago Azima tsaye tare da fadin "Da anyi magana za ki ce ba ki mantuwa ba ki yafiya! Ni a iya sanina ban ga abun da aka miki ba kike wannan kisar! Shin zaki iya gayamin laifi daya tak ƙwaƙƙwara wanda aka miki kike kisa? Mutum ko da ya miki kallon bai miki ba shikenan ya cancanci kisa!? Kina fakewa da cewa dan kar a tona mana asiri da cewa mu ba mutane bane macizai ne, a da ina yarda amma a kwana biyun nan na daina yarda dake! A da kin san da cewa ke macijiya ce amma ba kya kisa kamar na kwanan nan me yasa Azima!? Me yasa!?" Idonta ne ya sake rikiɗewa zuwa blue sosai, fatar jikinta har na caccanza kala ta ce "Fansa! Fansa! Fansa! Fansa nake ɗauka Aziza!" "To fansar me Azima gaya min?" "Abun da mutanen yankin nan suka min shekarun baya" Da mugun mamaki Aziza take kallon Azima dan ba ta taba furta wannan kalman ba sai yau, ta ce "Shekarun baya fa kika ce!? Duka-duka yaushe aka haifeki da zaki dinga lissafin shekarun baya?" Murmushin mugunta Azima ta yi ta ce. "Koma yaushe aka haifeni! Ba damuwarki ba ce! Amma ina so ki sani ki kara sani! Sai na kashe BAFFA! sai na kashe ARƊO! sai na kashe TSOHON SARKIN FULANI KWANA! da kuma wanda suka sauka a bayansa! sai na kashe MAI UNGUWA! kee sai na shafe dukkan mutanen yankin nan! Sannan na shiga birni cikin inda yake da jama'a da yawa na tarwatsasu! Zan bar wannan alƙaryan!" Gabanta Aziza ta tsaya ta ce "NI KUMA AZIZA MAGAJI ARƊO! ZANYI YAƘI DAKE NA DAKATAR DAKE! ZAN TAIMAKI MUTANEN YANKIN NAN KO DA KUWA ZASU GANE CEWA NI MACIJIYA CE SU KASHENI! ZAN TSAYA A GABAN BAFFA NA KARESA BA KI ISA KIYI MASA KOMAI BA!". Murmushi Azima tayi ta ce "Idan kin isa ki dakatar dani Aziza! Na fi ki mugunta! Kin fini karfin dafi! Muje zuwa Allah ya ba wa mai rabo sa'a!" Aziza ta yi murmushi ta ce "Amin!" nan Azima da Aziza suka rabe ko wacce tayi hanyarta daban. 🍃🍃🍃🍃 Hankali tashe Maga Isar da sakon sarkin fulanin yankin jimo ya faɗo fadar sarki Haruna ya ce "Allah ya taimakeka! Mummunar labari! Mai cike da tashin hankali, hakika yau munyi asara! Munyi babbar rashi!" daga nan kuma ya fashe da kuka! Nan hankalin jama'ar wajan ya tashi yayinda Sarki Haruna ya miƙe tsaye ya ce "Maga Isar da sako, me ya faru!?" "Haqiqa mun shiga ruɗu da ruɗani! Munyi sallama lafiya-lafiya da jarman macizai, amma yanzu haka sako ne daga yankin kwana a kan cewa an kashe jarman macizai! Yanzu haka gasu can sun dawo da kayansa da dokinsa! rigarsa duk jini!" ba iyakar sarkin fulanin jimo ba harta jama'ar da suke zaune a wajan sai da suka miƙe tsaye. Waziri ne ya yi karfin halin faɗin "Ce dasu su karaso su mana cikakken bayani dan bamu fahimci maganarka ba Maga Isar da Sako!" da sauri Maga Isar da Sako ya tashi yaje ya ce dasu su karaso, jiki a sanyaye babu kwari suka karaso suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27