Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Aziza Da Azima Macizai Ne Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suke naje na haƙo kayana da na binne wanda haƙo wannan kaya sabon bala'i ne da barazana wa rayuwar su Azima da Aziza har ma dake! Balle kuma ace ni da ake neman fansa a kaina! Su tsaya su saurareni na gaya musu yadda za ayi amma sam!" Baffa ya faɗa yana riƙe kansa dake sara masa, shuru Hajja ta yi ta ce "Komai ya yi zafi maganinsa Allah Baffan yan biyu, mu dage da addua Allah na nan!" "Haka ne Jumala, Allah ya shige mana gaba" "Amin" Hajja ta fada tana miƙewa da fadin "Ko inasu Azima da Aziza suke? Kai wannan yara yanzu haka suna can rafin jimulo" Baffa dai bai kuma cewa uffan ba. AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE complete Document Wani murmushi Azima ta yi da saurin komawa baya, ta ce "Kai ashe dai ina da babbar mugun ƙulli! Gobe Innu Maciji zai zo, ayya Innu Maciji ashe kwana ya kare! Ajali ya yi kiranka gobe, wayyo dadi zan so na ci gaba da ganin tashin hankalin wannan yanki, hakika Innu Maciji gobe asalin Macijiya Azima zata kasheka! Wayyo farin ciki! Zanyi tsumayen jiran zuwanka yankin kwana!" ta faɗi tana dariya tare da gyara mayafinta, sannan ta shiga gidan da sallama wanda rabonta da sallama harta manta,tana yin sallamar taji har wani ɗaci wuyarta ke mata, da mamaki Hajja ta amsa ita da Baffa dake zaune, kusa da Baffa Azima ta zauna tana murmushi sai kuma ta koma tayi fuskar tausayi tana kallon Baffa ta ce "Baffa kayi hakuri da abunda nayi dazu ban san nayi ba, amma Aziza ta fahimtar dani, ka yafe min Baffa ba zan sake ba, ban san lokacin da nake yi ba dan Allah Baffa👏🏻" shuru Baffa ya yi yana kallon Azima a ransa ya ce "Kenan da gaskiyar Aziza, Azima aljanu gareta?" a fili kuma Baffa ya ce "Shikenan ya wuce Azima,Allah ya miki albarka, amma ki gaya mini gaskiya ina kika samu zaren saƙar dana?" Turo baki ta yi ta ce "Baffa ganinsa kawai nayi a hannuna! Yanzu kuma ya b'ace, ban gansa ba" Baffa ya sauke ajiyar zuciya har yana hamdala, Azima ta miƙe taje ta rungume Hajja wacce rabon da ta rab'eta ba zata iya tunawa ba ta ce "Hajja ke ma kiyi hakuri" murmushi Hajja ta yi har kwalla na taruwa a idonta tana shafa fuskar Azima, yatsine fuska Azima ta yi a ranta tana kallon Hajja ta ce "Ni dai bana jin shaukin komai a tare daku, ko da ba zan ji a kan Baffa ba a matsayinki ta mahaifiyata ya kamata ace naji shaukin uwa da 'yarta, amma bana ji saboda ni ba mutum ba ce! muguwar macijiya ce, shiyasa ma babu amfanin na dinga rab'anku, abunda nake so shine..... KU DANNA HOTON KASAN NAN DON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN KO 👇👇👇👇👇👇 https://t.co/t4jXpAXI6U maganarta ce ya tsaya jin Hajja ta jijjigata tana mata magana, dan tun dazu Hajja ke mata magana amma hankalinta ya yi nisa da tunani "Na'am Hajja me kika ce?" "Tunanin me kike yi Azima?" " kawai Hajja babu komai mai kika ce?" "Ina Aziza?" tsaki Azima ta yi a boye da tana shirin tace bata sani din ba, sai kuma ta tuno da abunda take son yi ta ce "Na barota a rafi, Hajja bari na tayaki aikin gida yau" tana gama faɗi ta hau gyara kara a murhu,Hajja har can kasar zuciyarta take jin farin ciki, Baffa ya miƙe yana fadin "Ba ri naje na gaida Inna Wuro (matar Arɗo) kwana biyu ma tace ba kuje kun gaisheta ba, wai dama Aziza ce yar albarka yar dakinta, ke kam ma Azima ko meyasa jininku bai zo daya ba oho!" "Ai ni babu wanda jinina ya zo daya da na shi!" Azima ta faɗa tana murmushin gefen baki mai ciki da ma'anoni, Hajja ta ce "Kinyi magana ne?" "A'a Hajja ban ce komai ba, bari naje na ɗibo ruwa" ta faɗa tare da daukar tulu ta yi waje. 🍃🍃🍃 Tsaye take a wani jeji suna magana da Inno Fandi, Inno Fandi ta ce "Aziza jejin lore ba kamar sauran jejin yankin kwana bane! Jeji ne da bai tara komai ba fa ce sai manyan aljanu masu mugun sihiri, babu abunda babu a jejin lore,kina tunanin zaki iya zuwa?" "Inno Fandi Azima ma taje ta dawo balle ni? Ba ma Azima ba, Baffa da yake mutum ma yaje" murmushin manya Inno Fandi ta yi na yaro-yaro ne ta ce "Aziza tabbas Baffanku mutum ne amma ba kamar kowa ba" "Eh ni dai Inno Fandi ko ma miye zanje" "To shikenan Aziza, dokar tafiya jejin lore, ba a yinta da rana, sai dai ki bari da magriba ki tafi, sannan ki tabbata kafin garin Allah ya waye kin baro jejin! Za ki ta gane-ganen abubuwa amma karki tsorata, dan tsoronki barazana ce ga rayuwarki!" "To amma Inno Fandi ina ga hakan ai babu amfani tunda ni ba mutum ba ce macijiya ce" sake murmushi Inno Fandi ta yi ta ce "Sanin kasancewarki ba mutum ba shiyasa nake gaya miki hakan, da ace mutum dan adam ne da ya kama hanyar sunansa gawa! Tun kafin ma ya kai ga shiga" Aziza ta jinjina kai, nan Inno Fandi ta gama gaya mata matakin da zata bi taje jejin ta dawo, godiya sosai Aziza ta mata daga nan Inno Fandi ta b'ace, Aziza ta kamo hanyar gida, tana cikin tafiya har ta kusa isa gida ta haɗu da wasu yan matan yankinsu wanda za a kamasu nan da sati daya wato amare kenan, wanda dukkansu babu wacce ta haura sama da shekara shaɗaya, su hudu suka sha gaban Aziza, dayar mai suna Lantai ta ce "Ke wacece Azima ce ko Aziza!?" Aziza ta ƙara gyara lullubinta tana rufe gefen idonta da gashinta da ya sauko mata har kirji ta kara dukar da kanta kasa ta ce "AZIZA" wata mai suna Huwe ta ce "Yau kwayar idonki muke son gani, da asalin fuskarki!" gaban Aziza ne ya faɗi ta ɗan dago a hankali ta ga rana ya faɗi ga shi dole taje gida ta yi shiri, dan haka ta ce "Kun ga bana son kalen rigima da jan faɗa ku barni naje gida ni ba sa'arku ba ce!" dariya suka kwashe da shi inda suka hau tureta tana ja da baya, har suna faɗin wai gandamemiya marasa farin jini sun ƙi aure, babu mai sonsu! Gajiya Aziza ta yi inda ta daka musu tsawa sai da suka dare, hannu tasa ta kwashe gashinta na gefen fuskarta farin eyes dinta na mage suka bayyana, da mugun gudu wannan ta yi gabas,daya ta yi kudu,daya arewa,daya kuma ta yi yamma, Aziza ta ce "Alhamdulillahi! Ni ku ka samu, da ace Azima ce sai dai a aurar da wasu amma ba ku ba" tana gama fadi ta wuce da sauri tana sake rufe gefen fuskarta. 🍃🍃🍃🍃 "Assalamu alaikum" Aziza ta yi sallama Hajja dake kwashe kaya ta amsa ta ce "Aziza sai yanzu? Tun dazu nake tambayar Azima tace min kina rafi, sawunta yau biyar tana ɗibo ruwa" "AZIMAR!?" Aziza ta tambaya a mamakince, Hajja ta ce "Eh wollah, yana ganki haka Aziza ba ki da lafiya ne?" "E Hajja kaina ke ciwo sosai, shiyasa ma na zabi na

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});