Chapter 6
Chapter 6
WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *25&26* Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki yaji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai yace." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? tabe baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi musu, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu. Babu ladabi a maganarta tace." sai ranar da akayi hankali nima zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo. Tace." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi." Yana kokarin tashi zaune yace."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan." "Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne."? Yana kokarin magana su kaji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje." Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni. Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, tace." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka." Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa. Tace." Kai har mai ka siya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bukatar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji." Yace." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri." Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai. Jallabiya yasa ya fita. Wani shirgegen katon mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne. Ya mika masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo." Ba tare da ya rike hannun da ya mika masa ba yace." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba." Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna kaji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka." Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wa'inda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin." Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa. 'Yar dariya yayi irin wacce ya saba yace." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina nafiso muyi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka." Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah." Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli digon gashi babu kan sumul sai uban kyalli yake. Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin hakkinsa. **** Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har dasu zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya. Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa. A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara." "Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci." Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane." Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi tace." Shahida ba wai bana so bane. Aa
Table of Contents