Chapter 5
Chapter 5
ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki da maik'o sai ka rantse da Allah cewa kafafun ba'a jikinsa suke ba. Tsoro yasa ta dan ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba. Ya bude idonsa tare da kokarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta. Bakinta na rawa ta kirayi sunansa. Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta dake kasan motar yasa bakin kazantacciyar butar da ko arzikin murfi babu a bakinsa ya gumtsi ruwan ciki ya fesar dashi har sai da ya same ta a kafafu. Ya sake kafa bakinsa a bakin butar yana kokarin shan ruwan dake ciki. Cikin rauni da tausayi tace." Kada kasha wannan ruwan bashi da kyau zai maka illah.'' Ko kallonta bai yi ba ya kafa baki ya sha ya ajiye butar a gurin da take. Tsigar jikinta gabadaya ta tashi, sam bata san kallon butar saboda yanda zuciyarta take tashi. Komawa yayi ya kwanta ya rufe idonsa yana takure jikinsa, taji wasu zafafan hawaye suna kokarin kwace mata, wallahi da tana da yanda za tayi akansa da tuni tayi ta samar masa nutsuwa da makwanci mai kyau. Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta siyi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba. daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, tace." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar. Ta fara kokarin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi kaci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a." Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba. Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka tace." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.'' Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne. Hannu yasa ya karbi wainar a takaice yace." Na gode." A hankali yayi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata. Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo." Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta. Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu. Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko."? Tace." Eh saura naki a kadai gashi can a jug." Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.' Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya." Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi." Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita. Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa sai wannan mahaukacin.' Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar." Tana 'yar dariya tace." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa." Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri. "Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci." Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bude kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai kamshi yake. Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba. Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba. A sanyaye tace." Sannu ko baka da lafiya ne?" Ya daga mata kai alamun ."Eh." gabadaya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka tace." Zazzabi ko ciwon kai.? Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa yace." Babu ko daya jikina ne yake ciwo." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwake amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka." Shuru yayi bai ce komai ba. Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so." Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya dauki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin. Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya. 'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata! Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka! Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.? Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta. **** "Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi yayi sallama da Hujaj. Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa." Tace." To za'a fada masa. Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai bayar. Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha nashi gobe ya koma da wani abun nashi domin samun nasara da nin ka abinda ya bayar. *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:42] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA
Table of Contents