Chapter 4
Chapter 4
masa yoyo) duk ta san gwagwarmayar da ya sha a baya, ya tabbatar da cewar ba za tayi masa uzuri ba tunda kullum fadi take ai matan ba duka suka taru su ka zama daya ba." "Ki kwantar da hankalinki Insha Allahu zanyi aure very soon." Hanci taja kamar wata karamar yarinya murya na rawa tace." Alhaji Habu ni nafiso ka dawo da Fatima Uwar Shukura domin matar fari itace rufin asiri." Lokaci guda fuskarsa ta sauya! idonsa yayi jah! kansa ya girgiza da fadin." Hajia kada ki sake min maganar Fatimah idan kina so mu shirya.'' Ta kalle shi ganin yanda kwayar idonsa ta sauya yasa taji tsoro kada ciwonsa ya tashi dama can Fatiman ce *SILA* tace." To yanzu ka samu wacce zaka aura din kuma 'yar wane gari ce? domin wannan karon ba na so ka fita daga Najeria kaje wata kasa neman aure." A cunkushe yace." Ina dubawa tukkuna tunda nace miki na kusa aure to kisa al'amarin a cikin ranki kuma ki taya ni da addua." A sanyaye tace ." Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ya amsa da "Ameen hankalinsa na kan agogon dake daure a hannunsa. Tsaye ya mike wanda yayi dai-dai fa fitowar Shukura daga dakinta. "Daddy yau fa duka kwananmu biyar da dawowa ba zaka zauna ka huta a gida ba." Hannunta ya ri'ke da fadin.'' Daughter ku kwantar da Hankalinku ba nisa zanyi ba KANO na nufa insha Allah zan duba ma'aikatu na (company's) domin ganin abinda yake gudana." Ita da Hajiyan suka sauke ajiyar zuciya domin duk a tunaninsu sun d'auka zai bar 'kasar ne kamar yanda ya saba tafiye-tafiye. *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *23&24* Cikin nutsuwa yake musabaha da jama'a bayan idar da sallar asubahi a massalacin dake jikin gidanshi wanda ke unguwar giginyu, ya fito daga massalacin da cazbaha a hannunsa yana sanye da farar jallabiya mai karamin hannu kanshi sanye da hula mai raga-raga irin ta larabawa kamar ko da yaushe ya nad'e kansa da farin rawani. Can tsallake ya hangi wasu matasan samari a tsaye, jikinsa ya bashi cewar shi suke jira ya fito daga massalacin, aikuwa dai gabanshi suka zube suna gaishe shi, ya saki fuskarsa tare da basu umarnin tashi. Bayan sun gaisa sai kuma su kayi shuru suna sunkuyar da kai dukkaninsu da alamun magana a bakinsu. Gyaran murya yayi cikin kamala da dattako yace." Ko meye yake tafe daku kada kuyi shakkar fada min ina sauraranku." Na farkon yace." Alhaji Taimako nake nema a gurin ka, kayi min suttura kamar yanda Allah yayi maka, tabbas nazo gurin da za'a share min hawaye na." Da rawar murya yake maganar. Ya dafa kafadarsa da fadin." Menene bukatarka? fadi kanka tsaye." Yaji kwarin gwiwa a tare dashi yace." Mata ta ce ta haihu yau kwana bakwai kenan bani da abin hakika da goro da Alawa hankali na ya tashi sosai Alhaji domin maula ba hali na bane, kawai don bani da yanda zanyi ne kasancewar gwamnati ta yanke min albashi na, babu laifin tsaye bare na zaune wannan dalilin yasa wahala tayi min yawa yara na biyar gashi karamin ma'aikaci ne albashin duka dubu talatin da biyar nake dauka amma yanzu tsayin wata shida kenan da gwamnati ta zabge rabin albashin ya koma dubu goma sha bakwai, to wannan dalilin yasa duk wani karamin ma'aikaci yake cikin tashin hankali." Ya dinga girgiza kansa yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. ido ya tsurawa mutumin yana tunanin wani al'amari daya faru a cikin shekarun da suka gabata lokacin ma da duniya take kwance kenan Malam me za'ayi da mulkin Najeria. Numfashi ya sauke kafin yace." Kada ka damu komai yana da sanadi kuma kowane bawa akwai hanyar abincinsa saboda haka ni zan taimaka maka daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri." Gabadaya suka amsa da "Ameen." Ya kallesu kafin yace."Abokansa ne ko kuma tafiyar kowa daban."? Hada baki sukayi gurin bashi amsa da cewa." Abokansa ne." Sai yayi murmushi wanda yake fitar da zahirin kyawunsa ya umarce su da su bi bayanshi zuwa gida. Dubu dari cash ya bashi da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai. Shi da abokansa suka rasa bakin godiya. To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu. **** Yau haka kawai ta tashi da kwadayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin Jakara take. Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai bata sha'awa ba, wainar geron dai take kulafuci. Ta kalleta da fadin." Baba bani dari zan siyi waina yau kwadayinta nake ji." Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika mata. Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta 'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma. Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da tayi dashi a kwance a k'asan mota akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da kazanta har da kashin awakai." Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da annuri. Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci. Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana mamakin abinda
Table of Contents