Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Majanuni Book 2 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/8, 09:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN-ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITERS ASSO_ __________ *35&36* Lokacin da ta isa gidan baya nan, amma kuma daf yake da dawowa domin shiri na mussaman na zuwa mahad'arsu. Babu yabo babu fallasa Talatu ta karbe ta. suka gaisa sama-sama kafin ta bar ta zaune a gurun. Jamila ta shigo gidan hannunta rik'e da 'bakar ledar dake dauke da kayan miya gwalagwaji. ganin ta yasa ta washe baki da fadin." Baba ke ce a gidanmu."? Ta saki fuska da fadin." Ni ce Jamila ai na jima da zuwa ina zaune ina jiran dawowar babanku." Ta ce." Aikuwa yana kan hanya domin lokacin dawowarsa yayi." Talatu ta fito daga kicin ranta a 'bace ta harare ta da fadin." Sarkin shishshigi da cusa kai a maimakon ki kawo min aiken da nayi miki shine ki ka tsaya kina neman suna ko.'"? A sanyaye ta ce." Kiyi hakuri." Tsaki taja da karfi ta fizgi ledar dake hannunta aikuwa ta yage kayan miyan suka watse a gurin, sai kawai ta hau d'ura mata ashar! ranta a a bace tayi saurin barin gurin tana turr!! da halin mahaifiyarsu sam bata da d'abia mai kyau. Shahida ta fito tsakar gidan da alamun bacci a idonta, Jamila ce da ta shiga dakin ta tashe ta daga baccin tana sheda mata zuwan Baba Asaben. Ganinta yasa zuciyarta karyewa sai kawai ta zube a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai sosa zuciya. Jin kuka ya cika gidan ya sanya tayi gaggawar Fitowa daga kicin da ludayin miya a hannunta nan ta iske Baban na rarrashinta da fadin." Tayi shuru ta share hawayen ta mutukar tana raye babu mahalukin da ya isa yayi mata auran dole. Karaf ta bude baki ta ce." Wannan fa ba hurumin ki bane Baba kina nema ki wuce gona da iri a akan wannan yarinyar." Ta daga mata hannu da fadin." Saurara haka kada kiyi min rashin kunya ba gurin ki na zo ba gurin mijinki na zo kuma shi nake zaman jira saboda haka kada ki kuskura ki kara wata magana a cikin wannan al'amari." Ta ja dogon tsaki tana surutai kasa-kasa ta juya ta shige kicin domin cigaba da aikin dake gabanta. A gaggauce ya shigo gidan kawai yayi tozali da ita a zaune tare da yarinyar a kusa da ita, kallo daya yayi mata ya san da abinda ta zo. A tsaye ya gaishe ta fuska a daure ta amsa, da sauri ya nufi hanyar dakinsa ta dakatar dashi ya tsaya tare da soka hannuwansa a cikin aljihun rigarsa. Ta ce." Ba wani abu ne ya kawo ni gidan ka ba sai wannan yarinyar domin na zo ne na tafi da ita saboda ba zan ta'ba yarda ka cutar da ita ba." Ya ce." Kin taba ganin uban da ya cutar da abinda ya haifa."? Ta ce." Sau nawa kuma sai dai idan ba a sa son zuciya ba." Ya girgiza kai da fadin "Shikkenan Baba ni ba naso mu dinga jayayya da juna, zan baku dama da lokaci dake da yarinyar domin ni ba mutumin banza bane nayi nufin yi wa 'ya ta aure kin hana to wannan ce dama ta 'karshe a gare ku sati uku kacal ya rage bikin Hadiza kuma so nake na had'asu duka na auran, a cikin wannan satikan nakeso Shahida ta tsayar da miji idan ba ta tsayar ba wallahi tallahi zan had'a ta aure da duk wanda nayi ra'ayi. Cike da alhani da jajantawa yarinyar Tace." Wai shin Jamilu kai wane irin uba ne mara tausayi da jin kai? shin baka ganin halin da yarinyar nan take ciki ne, bata da koshin lafiya wane namiji ne a wannan zamanin zai iya da lalurarta" Ya ce." Tunaninki daban da nawa, ni a ganina duk wannan ba matsala ba ce kuma wanda zan bawa auranta zan sheda masa matsalarta cewa kurma ce to sai kuma me? tana da duk abinda da namiji yake bukata a jikin mace matsalar rashin ji ba zai ha na komai ba, saboda haka wannan shine hukuncin dana yanke." yana kai karshen maganarsa yayi gaggawar bude dakinsa ya shiga. Jiki a sanyaye suka koma gida, duk da cewa ba duka taji komai ba amma ta tsinci wasu maganganun, hawaye kawai take sharewa ta je ta kudindine a kan gado zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta. Kawu Musa ne ya kai ta chamis aka duba ta tare da bata magani, a wannan lokacin ya tausayawa yarinyar sosai amma ya za suyi da abinda yafi 'karfinsu Jamilu shi yake da iko da 'yarsa ko'ina aka je shiyasa da yaji Baba Asaben tana ikirarin kaishi kotu ya hana ta ya ce tayi hakuri kawai kanta za ta bawa wahala Jamilu yafisu rinjaye da yarinyar. Kwananta biyar a kwance tana jinyya kafin ta warware ta rame fuskarta tayi haske da tafin kafarta da hannunta alamu sun nuna tana bukatar ruwa a jikinta. Ta fito da hijabi a wuyan ta. Ta kalle ta da fadin." Shahida Na ce ." Ki bari yara su kai abincin nan tunda har yanzu jikinki bai gama dawowa daidai ba kiyi hakuri ki koma ki kwanta. Zumbura baki tayi cikin yanayin da Allah ya halliceta Ta ce." Ni dai idan kin zuba masa kawai ki bani na tafi na kai masa." Tayi murmushi da fadin." Shahida ko dai wannan mutumin dashi za ayi ne.? Murmushi tayi tana kawar da fuskarta. Wani irin tausayin yarinyar ya lullube ta idan ba sharrin zuciya ba mai zai ja hankalinta kan mahaukacin da bashi da asali kawai ganinsa akayi rana tsaka, wannan yana daya daga cikin sharrin *SO!* dole tayi wa yarinyar uzuri. Ta mika mata kwanon abincin da fadin." To gashi nan amma kada ki ce zaki zauna a gurinsa kamar yanda ki ka saba zaki janyowa kanki jifa da tsokanar yara domin dai duk wanda ya gan ki tare dashi zai dauke kema irinsa ce." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Yanzu zan dawo insha Allahu." Hanyar fita ta nufa, sai ta bita da kallon tausayi da jimami! **** Yana can cikin k'arkashin motar a kwance kafafunsa kawai take hangowa sunyi 'kura sosai amma babu kaushi ko faso! a tafin 'kafar sai dai daud'a. Da d'an karfi ta kirayi sunansa "Baban-Baba." Jin muryata a cikin kunnansa yasa da sauri ya bude idonsa ya fara kokarin fitowa daga kasan motar. Ido ya tsira mata yana mata wani irin sihirtaccen kallo, kaunarta yake har cikin kokon ransa. Murmushi tayi ta dan tsuguna kusa dashi ta ajiye kwanon abincin a gabansa, a nutse Ta ce." Ina wuni." 'Kin amsawa yayi kawai ya kafe ta da kwayoyin idanunsa wanda ta so ta fuskanci

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});