Chapter 11
Chapter 11
cewa." Ashe dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai ya kai karshen maganar. Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karan dole ne ya nuna iko akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi, yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita. "Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fada ya sake katse shi a karo na biyu ya ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin kamar kububuwa! Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a tashe ya shiga gidan! Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake kokarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali. Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse? Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata karfin iko na a kan 'ya ta." Ta ce." Me take nufi to? Yana kokarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi magana." Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke." Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan Baba Asaben ya nufa. Dama ta shirya masa koda ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya ko kallonsa ba tayi ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa. Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya." Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon kansa ba, ai dama na shirya zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa."! Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce." Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki mai zai sanya ki dinga kokarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na cigaba da ganin mutuncinki." Ta ce." Jamilu cin mutuncin ka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan ba sai in da karfi na ya 'kare akan hakan." Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta." Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya daya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai Allah yayi muku hisabi." Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.'' Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata 'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa. Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata. Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda takaici! Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma mutumin da yake kokarin hada aure da Shahida bai cancanta ba." Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu." Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da abinda ya da ce ba, to ita muddun tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba. Tana fitowa daga kantin Shu'aibu ta hango shi ya fito daga gidan. Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango tsantsar tashin hankali a fuskarsa. Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a turbene ya k'arasa in da take ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja ta sukayi gaba. Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai faduwa yake tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya tsaye gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba, sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan kanta." Kallo guda yayi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shakiki ne a gurin ta saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu. Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya dauko dari biyu ya bashi domin shi duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.'' Girgiza kansa yayi kafin ya ce." Ina zaka kai min matata?" Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta na dukan uku-uku! "Kai ba na
Table of Contents