Chapter 3
Chapter 3
da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *21&22* Talatu tare dasu Hadiza kamar su mutu saboda takaicin da Hujaj ya k'unsha musu, babu shakka ya cutar dasu, domin naman da ya bar musu bai taka kara ya karya ba, da 'kyar zai kai sati d'aya, gashi sun ci burin ajiyar nama saboda bayan sallah idan kwadayi ya tashi su fito dashi su gyara abinsu, Talatu dai kasa hakuri tayi ta shige daki tana matsar hawayen bakin ciki, tunanin hanyar da zata kuntata masa take. 'Bangaran sa kuwa har ya manta abunda ya aikata domin wanka yayi ya shirya cikin sabon yadi mai tsada anyi aikin kufta a wuyan rigar da hannuwa, ya dora hula zannar bukar a kansa ya fito yana kamshin tsadaddan turaransa. Yaran ya samu sunyi jugum-jugum! kamar anyi mutuwa. Ya kallesu na minti biyu kafin ya girgiza kansa ya kama hanyar fita ba tare da yayi musu magana ba, Jamila ce kawai ta iya yi masa a dawo lafiya Hadiza da Amina kuwa harara suka bi shi da ita yana fita Hadiza taja tsaki ta mike tsaye tana kunkuni! daki ta shiga, Jamila ta bita da kallon mamaki! ita kuwa Amina bakin kasko ta nufa ta juya naman dake kan wuta kafin ta tsamo katuwar tsoka tasa a bakinta tana taunawa tare da hure zafin dake barazanar 'kona mata dadashi. *** Jiki a sabule ta koma gida. Abin duniya yayi mata katutu! matsalar Baban-Baba ita tafi damunta, sai kuma matsalar mahaifinta, sharadin daya gindaya mata na fito da mijin aure cikin wata uku yayi mata tsauri! ba ta da madogara sai Allah domin kuwa babu wani namiji da ya nuna yana sonta ballanatana har su kai ga maganar aure. Sallah ta wuce da sati biyu da yawa daga cikin wa'inda sukayi layya sun cinye naman su, har sun fara siyan na miya, ita kanta Baba Asabe da ta yanka RAGO a yanzu bata da nama sai diddiga da kakide domin ba tayi son zuciya ba tayi sadaka da naman kamar yanda Ubangiji ya umarta Saliha ma tuntuni ta cinye nata, Shahida ce kawai mai nama a gidan ta kime shi a cikin kakide ta boye a karkashin gado ita bata ci ba, ba kuma ta bawa wani yaci ba yana ajiye. Tana zaune a tsakar rumfa tana taimakawa Baban da daurin gishiri taji motsi a cikin uwar daki. Haka kawai jikinta ya bata wani abu, da sauri ta ajiye gishirin dake hannunta ta shiga dakin wanda yayi dai-dai da lokacin da Saliha ta janyo kwanon naman da ta boye a karkashin gado. Suka had'a ido Saliha ta diriri ce! sai ta wayance da fadin." Ke ni ba naman ki zan ci ba ina neman warin takalmi na ne." Tsaki taja ta dauke kwanon naman da fadin." Saliha ko kinfi kud'a maita wannan naman yafi karfinki wallahi domin wanda na ajiye wa ya fiki daraja a guri na." Saliha ta fusata! "Ni ce mayya." Tace." Me yasa to zaki zo kina min binkice naman nan an raba an baki naki kin cinye, sai kuma ki dinga bibiyar nawa." Tace." Don Uwarki sharri zakayi min naman banza naman wof.......! Shigowar Baban ya katse maganar tace." Menene wai ? tun daga soro nake jin hayaniyarku." Cikin yanayin maganar ta tace." Nama na zata satar min shine don na ganta take borin kunya." Cike da mamaki tace." A ina ki ka samu nama ke kuma."? Tace." Wanda ki ka bani ne na boye abina." Tace." Meye amfanin boye wa sai ya lalace yanzu lokacin zafi ne gwara ki fito dashi ki cinye ni bana san neman fitina." Kai tsaye tace ." Baban-Baba na ajiye wa." Gabadaya suka zuba mata ido. Baban ta sake maimaita maganar." Ki kace Baban-Baba ki ka ajiye wa ."? Ta gyada kai alamun "E." Ba ta iya cewa komai ba kawai ta kama hanya ta fita daga dakin da tunanin wani abu a ranta, lallai dole ne idan Kawu Musu yazo ta sheda masa abinda ke faruwa domin ta fara zargin wani a cikin ranta. *ABUJA* Tun daga bakin Estate din zaka gane lallai mazauna gurin manya mutane ne, gida hudu ne kacal sai tarin sucurites wanda suke kai kawo a gurin, can gefe kuma wasu lafiyayyun karnunaka ne biyu a kwance da alama suna rama bashin baccin da suka ci. Gida daya a cikin hud'un yafi tsaruwa da burgewa yanayin ginin zai baka sha'awa sosai babu shirman kyale-kyale irin na almubazzaranci. Daga saman babban gate din da ya katange gidan anyi ado da suna Annabi Muhammad SAW da gold an rufe da wani irin glass mai mutukar daukar ido daga ciki wasu irin fitilu ne da suke bada haske kala-kala sai dare abin yake sake k'ayatuwa da jan hankali. Ginin tsakiya ne wanda yake dauke da bangare uku sai filin ball dake can gefe da parking spece a in da yake dace, sai kuma gurin hutawa wanda akayi masa ado da wasu irin kujeru masu kyau da daukar hankali. Suna tsaye sanye da bakaken kaya a bakin kofar suna dakwan fitowarsa, Adamu ne da Sule Escort dinshi. Yana zaune a gabanta kafafunshi a tankwashe kamar karamin yaro da alama Umarninta yake jira." Hajiya Saude ce kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa ita kadai ce ta rage masa a duniya ita kuma yake gani yayi farin ciki duk mai son yaga walwalarsa ya mutunta ta, mai san ganin dariyarsa ya daraja ta. "Hajiya lokaci na tafiya." Ya fada yana duba tsadaddan agogon dake daure a hannunsa. Ta kalleshi tana ya tsine fuska kafin tace." Habu." ita kadai ce take kiransa da wannan suna *HABU* tun yana yaro, Asalin sunansa Abubakar-Assadiq mahaifinsa ne kadai ke kiransa da Assadiq sai kuma abokan karatunsa, amma da yawa daga cikin 'yan uwan mamansa kuwa suna kiransa da *DAN GASKE* wanda mahaifiyarsa ta sanya masa dalilin yaci sunan mahaifinta da kuma alkunya irin ta dan fari, wannan dalilin yasa 'yan uwanta suka boye sunan domin daraja sunan mahaifinsu, sunansa ya 'bace gabadaya a famliy idan zaka kwana kana kiran ainihin sunansa babu wanda zai gane wanda kake nufi mutukar baka kira *DAN GASKE!* ba. Ta cigaba da cewa." Na ce wai kai ina zaka kai kudi ne? kullum baka gajiya, kai ne can kai ne nan, a duniyar nan babu 'kasar da baka taka ba, wannan kudi dai haka zaka tafi ka bar su, ka naji kana gani Shukura ta zama magajiya tun da ita kadai ka ajiye gemai-gemai da kai da gemu da furfura kana zaune babu aure." Sai ta fashe da kukan bakin ciki ta cigaba da cewa." Ya jama'a ba zasu zarge ka ba, Habu nima na fara zarginka kana neman matan banza a waje." Ya sunkuyar da kansa yana sauraran kukanta dake mutukar tafarfasa masa zuciya! zubar hawayenta yana nufin abubuwa da yawa a tare dashi, dole ya rarrasheta domin duk irin bayanin da zai mata ba zata yarda ba bahaushe yace (mai daki shi ya san in da yake
Table of Contents