Chapter 13
Chapter 13
Hadiza da sauran 'yan uwanta sai kuka suke, ita kuwa Talatu tana zaune a kofar wani gida abin duniya ya dame ta, ma'kota da 'yan uwanta sai bata baki suke, Saminu yasa k'aton kwado (dan mukkuli) ya kulle gidan yayi tafiyarsa. Hujaj tunda yake bai ta'ba tozarta irin yau ba, ya rasa da wane ido zai kalli Jama'ar dake gurin, kawai sai ya huce! fushinsa akan Shahida ya dinga gaura mata mari yana fadin." Kin ga irin abinda ki ka janyo min ko? kin ga tozarcin da ki ka janyo min ko."? ya dinga kwashe ta da mari yana haurinta da kafarsa har sai da ta durkushe a gurin tana wani irin kuka! da kyar aka janye shi daga gurin ana bashi hakuri. Malam Habu makocinsa ya ja shi gefe yana bashi baki da fadin ." Haba Alhaji Jamilu ka nutsu mana ita kuma wannan yarinyar da kake dukanta meye laifinta da zaka huce fushinka a kanta dama tuntuni nake fada maka ka gyara kuskuranka saboda irin wannan rana to yanzu ga abunda ya faru." Ya cire hular dake kansa yana firfita da ita ya ce." Malam Habu wallahi ban taba tunanin Saminu zai yi min wannan tozarcin ba, amma babu komai tsinanniyar yarinyar can ce ta janyo min domin da ta amince da bukata ta da tuni haka ba ta faru ba kamar ni a ce an tozartani irin haka.'' Malam Habu Ya ce." Yanzu dai mu bar wannan maganar insha Allahu komai zai daidaita, akwai daki da rumfa a cikin gidana zan baka aro ka shiga ka zauna kafin mu ga abunda Allah zai yi." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke da fadin ." Na gode sosai Malam Habu Allah ya saka da alkairi." Ya ce." Babu komai bari yanzu nasa yara su kwashe kayan su shiga dasu Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba .'' Ya amsa da "Ameen yana bin gurin da kallo, manya da yara sun cika sunyi dafifi a gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa. **** "Ranka ya dade wallahi na dauka binkicen da ka sanya ni zai bani matsala sai gashi cikin hukuncin Allah komai ya zo da sau'ki don lokacin dana shiga Unguwar ban sha wahalar sanin waye Alhaji Jamilu ba." Zamansa ya gyara a nutse ya ce." Sule nima nayi farin ciki da haka ina fatan zan samu kyakykyawan labari daga gare ka." Fuskarsa ta sauya da alhani da kuma jajantawa. Ya ce." Yallabai al'amarin mutumin dai babu arziki babu kuma kima da mutunci.'' "Ina sauraranka." Ya fada tare da mayar da hankalinsa gare shi. Cikin rashin jin dadin abubuwan da ya gani da idonsa ya shiga warware masa abunda ya faru ya kuma dora da bashi labarin da ya samu daka bakunan mutane da sauran jama'ar dake makotaka dashi, domin ya tabbatar masa da gaskiyar binkicensa ya nuna masa hotonan da ya dauka a lokacin da yake ta zazzabgawa yarinyar mari ana ta bashi hakuri. Ya karbi wayar yana duba hotonan ransa yayi masifar 'baci ganin yanda yake dukan yarinyar har da kafarsa, babu shakka wannan mutumin bashi da mutunci kuma bai san darajar dan adam ba, kuma jahilci shike da damunsa ba wani abu ba, hakika ya ji ciwon yanda ya ke tozarta yarinyar a gaban jama'a amma bai nuna hakan a fuskarsa ba, ya mika masa wayar da fadin." Goge hotonan daga wayarka." Da sauri ya goge gabadaya kamar yanda ya umarce shi. Ya kalle shi a nutse ya ce." Da safe idan Allah ya kai mu ka je ka nemi shi mutumin da yayi tozarcin domin jin cikkenan karin bayani daga gare shi, ina so ya tabbatar maka da iya adadin kudin da yake bi daga baya sai mu ga ya za'ayi ." Ya ce." Insha Allahu zanyi kokarin ganin hakan ya tabbata." Ya ce." Ma sha Allah ka tashi ka je kawai sai Allah ya kai mu goben ." Ya mike yana godiya sannan yayi masa sallama ya tafi. A daran ranar bai kwanta ba sai da yayi Istahara akan al'amarin, ya wayi gari da yarinyar a cikin ransa, yana tausaya mata sosai yana kuma so ya aure ta amma yana tunanin wani abu a cikin ransa, duk da hakan ba haramun bane amma yana ganin kamar yarinyar tayi masa 'kan'kanta da yawa idan anyi duba da matakin shekarunsa, yayi mata girma domin yana kallonta ne kamar 'yar sa Shukura a zahiri shekarunsu na iya zuwa d'aya. **** Sule ya zo masa da cikakken bayani akan Saminu ya warware masa komai da yanda Hujaj din ya dinga yaudararsa har yayi masa alkawarin bashi auran 'yar sa, daga baya kuma ya dinga yi masa yawo da hankali wannan shine dalilin da ya sa ya yanke wannan hukuncin. Ba a ja dogon lokaci ba ya Umarci Sulen da kudi dubu dari hudu ya je ya kai wa Saminun domin kashe wutar yace koma lallai ya je ya bude gidan ya kulle. amma ya gargadi Sulen cewa kada ya kuskura ya sheda masa cewa ga wanda ya biya kudin. Saminu ganin har da riba akan kudinsa yasa da saurin gaske yasa rigarsa ya fito kai tsaye gidan Hujaj din ya nufa, lokacin ya fita yawon Malamai burinsa kawai a daure bakin Saminu sannan ya wulakanta a duniya kamar yanda ya wulakantashi. Sai Malam Habu ne ya kar'bi mukkulin ba tare da ya bi ba'asin komai ba ya bude gidan, yasa yara suka dinga kwashe kayan suna shiga dasu. A gari ya ji cewa Saminu ya dawo da mukkuli har iyalinsa sun koma ciki, sai ya sake gazgata karfin aikin malamin da ya taimaka masa, domin duk a ganinsa aikin malamin ne yayi tasiri. 'Bangaran Baba Asabe kuwa da kyar ta wayi gari, domin tunda Sha'aibu mai kanti ya sheda mata cewa Hujaj ya tafi da Shahida hankalinta ya tashi mutu'ka! har tayi niyyar zuwa gidan suyi wacce za suyi Kawu Musa ya hana ta yace a rabu dashi su ga iya gudun ruwansa. Kasa hakuri tayi washe garin ranar da yamma ta shirya ba tare da tayi shawara da kowa ba ta nufi gidan, domin bata tsammanin zata zubawa mutumin ido yayi abinda ya keso a kan marainiyar Allah, dole sai tayi masa karakare! sannan za su daidaita. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira
Table of Contents