Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Majanuni Book 2 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sake tambayarta domin jin cikakken bayani. Murya na rawa da yanayin maganarta ta fara sheda mata hukuncin da baban nata ya yanke a kanta cewa lallai zai had'a ta aure da wanda yayi ra'ayi. Baba Asabe tayi tsalle ta dire! ta fara surfa bala'i ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce." Wato yanzu ne zai nuna iko a kanki saboda bashi da kunya an gama yi masa wahala kin girma kin zama mutum shine zai shigo da wannan maganar to wallahi bai isa ba mutukar ina raye ba za'ayi wannan auran ba." Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba. Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar." Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na aikata wannan abu." Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar al'amarin ba." Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so." Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake. A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana! Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa." Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce bata nan." Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa da tarin munin da Allah yayi masa. A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci! Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata. Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani! Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido. Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta. Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin. Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin. ''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta. Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."? Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa dake cikin wannan gari namu mai albarka." Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka ganta ka ga kana so."? Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci. Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake so."? Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa." Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza! Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin." Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .'' Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa domin muyi wacce za muyi." Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin. Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya. Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin...... *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:43] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *31&32* "Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});