Chapter 2
Chapter 2
ranta tace."Talatu ina kwana anyi sallah lafiya."? A dakile ta amsa ta cigaba da juya zallar sokar naman dake cike da kaskon suya. Jamila ta shimfida mata tabarba tana zama ya shigo gidan fuskarsa a tur'bune! kamar koda yaushe yana sanye da tsadaddiyar shadda wacce taji uban aiki irin na manyan mutane, hula da takalmi da agogo duka babu na banza kamshinsa kuwa tuni ya cika gidan. Gabadaya su kayi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala ya bude dakinsa ya shiga babbar rigar ya cire ya rataye ya zauna kasan kafet zugum! daka gani yana da damuwa. Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya amsa yana bin ta da kallo har ta samu guri ta zauna tana sake gaishe shi. Ya amsa yana mata wani irin kallo kafin yayi kwafa da fadin." Sai yau ki kayi ra'ayin zuwa in da nake."? Shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Ya cigaba da cewa." Maganar aure ce bakya so nayi miki shiyasa ki ka dauke kafarki daga gidan nan ko.''? Ta kalleshi da fadin." Baba aure nufin Allah ne idan lokaci yayi zanyi aur......ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu da fadin." Ni zaki fadawa lokaci? zaman me kike kin zama uwar mata shekara ashirin kanwarki Hadiza saura wata uku bikinta ga Jamila nan itama nayi magana da yaron da yake son auranta mun tattauna da mahaifinsa, ke da kike babbarsu kina zaune to wannan itace magana ta karshe da zanyi miki wata biyu kacal na baki ki fito da mijin aure tunda kin kammala secondary kinyi saukar al'kur'ani to kuma me ake nema."? Tana shashshekar kuka tace." Wallahi Baba tunda nake babu wanda ya ta'ba cewa yana sona, duk wanda yake so nayi aure ba kamar ni ba, na dai fi tunanin saboda lalurata maza suke gudu na." Ya girgiza kai da fadin.'' Mace bata kwantai matsalar ki ba zai hana ki auruwa ba, ki na da duk abinda ake bukata saboda haka ni ban yarda da wannan maganar taki ba." Sai ta kasa ce masa komai domin duk abinda zata fada masa ba zai yarda ba, bahaushe yace." Mai daki shi ya san inda yake masa yoyo, gaskiya ne tunda ta taso babu wani namiji da ya taba cewa yana sonta. Hannu tasa ta goge hawayen fuskarta, ta kalleshi har yanzu fuskarsa bata sassauta ba." "Zan tafi Baba." tafada tana kokarin tashi. yace."Ki bari sai yamma idan an kammala soya naman ki tafi da naki." Ya sosa mata in da yake mata 'kai'kayi cikin fargaba tace."Baba ina ka samu kudi ka yanka *SAH!* har da rago ." Ya kalleta yana sake tamke fuskarsa." Ke ni kikewa wannan tambayar don ubanki." Ya fada yana zazzare mata ido! A sanyaye! tace." Kayi hakuri." Hanyar fita ya nuna mata da hannu cikin tsawa! yace." Tashi ki fita ki bani guri." Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo yayi bajinta burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai kudi ne. Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi *SAH!* da ragon a gurinsa. Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba. Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai da aka kwamushe haka ya dawo gida a motar haya. Kwabo yanzu babu a cikin account dinsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa. Ta shiga dakin tana gyara daurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take fuskarta na maiko. Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada." A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin." Ta juya ta fita bagazan-bagazan! Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu. Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma." ? Bai saurareta ba ya cigaba da loda tsoka da k'ashi cikin buhu yana fadin gidajan da za'a kai musu. Talatu kamar ta dora hannu ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a kai kuma."? Yace." Na bayar sadaka dama haka Allah yace ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya ishe ku." Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba. Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan kaunar da mahaifin nasu yake musu. Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata bukata ta siyan icce ko man gyada da makamantansu. *LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV* [9/7, 10:41] bintaumarabbale: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI* _NA_ *_BINTA UMAR ABBALE🍒_* _MANAZARTA WRITES ASSO_ _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna
Table of Contents