Chapter 68
Chapter 68
komai ba a wannan fannin. Ta rufe idanunta tsawon wasu sakanni kafin ta sake buɗe su tana ƙoƙarin saita kanta. Amma ta gaya mata cewa lokacin wani rauninta ya kare, kar ta yarda wani abu ya gaya mata cewa an fi ƙarfinta ba zata iya ba, tace mata itama macece, duk wani abu da take taƙama dashi itama tana dashi, kawai ita tana amfani da nata wayon ne ta mummunar hanya, don haka idan ita zata ɓullarwa gaskiya, a lokaci kadan ne zata kawo karshenta don gaskiya itace sama da komai a duniyar nan. "Kilishi bata fi kowacce mace ba a duniyar nan Amina, yadda take takama da wayo da kuma dabararta, haka Allah ya halittawa ƙwaƙwalwar dukkan mata don ita mace uwa ce, an halicci mutane da yawa da zasu rayu a ƙarƙashinta wanda kowanne da irin ƙalubalen rayuwarsa, shi yasa Allah ya buɗe ƙwaƙwalwarta ta yadda zata iya samar da mafita kala-kala a fannin rayuwa. Wasu matan basa gane hakan ne har suyi yunƙurin sanin abinda zasu iya, matan kuwa da kika ga suna zaune lafiya tare da mazajensu ƴaƴansu harma da duk wanda zai raɓe su, sune wanda suka iya buɗe wannan baiwar tasu, Mata irin Kilishi kuma sune wanda suke amfani da wannan baiwar ta hanya mai munin da har suke ganin cewa sun fi kowa. Yanzu girma yazo kanki da gaske Amina, kin fara ganin hakan tun daga ranar da kika bar karƙashinmu, kuma hausawa sun ce aure yakin mata, yaki ne da kowacce mace akwai kalar nata, don haka kema dole ne ki bude ƙwaƙwalwar ki, ki karɓi wannan girman sannan ki fuskanci naki yaƙin Amina..." A daidai wannan lokacin suka shigo harabar wani haddadden gini mai tarin fitulun dake ta haske suna maraba da daren da bai kai ga ƙarasowa ba. Ma'aruf ya tsayar da motar a jerin motocin dake tsaye a wajen daidai lokacin da idonta ya zare akan sunan wajen. Haseenah Guest Inn. *** "Mene ne total charges for Adjustment and Uncollectables?" Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar da yake yi daga cikin dakin, yana zaune ne akan wani dan karamin dining table dake can karshen dakin yayin da hannunsa ke rubutu a cikin notepad din dake kan teburin. Kayan jikinsa wata loose T-shirt ce da ya siyo da kuma wani gajeran wando kalar grey. "Next..." Ya sake faɗa bayan mai maganar na ciki ya gaya masa wani adadi da ya rubuta a cikin wayar. "Ka gaya min Net Patient Revenue din?" "Na gaya maka yallabai, shine na biyu bayan total charges na Patient Care gabaɗaya." Mai maganar daga cikin wayar ya fada, sai ya gyada kansa yana bude shafin baya, ya karanta abinda ya rubuta sannan ya sake dawowa inda yake yace. "Operating Expenses din fa?" Mutumin na ciki ya sake faɗo masa wani adadi da ya shifa rubutawa. "Sannan sir akwai Bad debts ɗin wancan..." "Sai kuma Natural Expense ɗin?" Ya katse shi ba tare da ya saurari abinda yake cewa ba, mutumin ya ɗanyi shiru kafin ya faɗo wani adadi na makudan kudin da saida Ma'aruf ya jinkirta kadan yana saurarar sa kafin ya rubuta. "Yallaɓai ka saurare ni akan zancen bashin nan, bamu da wata hanya ne dole..." "Just tell me the total Sadiq." (Kawai ka gaya min jimlar komai gabadaya Sadiq.) Muryarsa ta fito a hankalin da take tun bayan sallar magariba da yayi buda baki. "Wallahi yallabai zai fi kyau ka duba Report ɗin gaba ɗaya tukunna gabadaya 42 pages ne, idan ka karanta komai you will realize that..." "Ka gaya min total din kawai Sadiq." Yadda sautin muryar tasa ta fito wannan karon ita tasa Sadiq din sarewa daga dukkan ƙokarin da yake fanin zai iya shawo kansa, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya fadi wasu makudan kudade da shi kansa Ma'aruf ɗin ya sani idan za'a bincike account dinsa na bankuna tsaf a tattaro komai baza 'a taba samun wannan adadin ba, don haka bai ma rubuta ba, wani guntun murmushi ne ya suɓuce a lebbensa yayin da yayi baya ya jingina da kujerar da yake kai yana kallon gabansa tamkar Sadiq ɗin ne a wajen. "Wallahi yallabai..." "Sadiq" Ya katse shi, sautin muryarsa can ƙasa amma kuma a kausashe. "A rufe asibitin, a tsayar da komai, kwana kaɗan na baku, I'm coming in few days, ku san yadda zaku gyara wannan abin in a reasonable way kafin zuwa na. Idan ba haka ba, na rantse da Allah wasu ne zasu ci muku abinda kuka ɗiba ba ku ba, and just dare me and see.!" Yana faɗin haka ya kashe wayar, ya cilla ta kan teburin da karfi har sai da screenguard ɗin dake kanta yayi wata katuwar tsaga guda daya, sannan ya cusa hannayensa duka biyu a cikin gashinsa yana ƙoƙarin saita numfashinsa, ransa ne yake shirin baci ya sani, amma yana kokati da dukkan iyawarsa ya danne hakan kamar yadda ya saba yanzu a kwanakin nan. Bakinsa ya shiga karanto hasbunallahu wa ni'imal walkil daidai lokacin da kofar toilet din dakin daga can gefe ta buɗe bayan abinda zai iya kira aƙalla minti talatin. Ya sauke hannayensa daga fuskarsa kafin ya juyo ya kalle ta, tana tsaye daga kofar kamar zata koma ciki ne ta sake rufewa, babu shiri yaji dukkan abinda ke cikin kansa na sulalewa yana bin iska, rigar da ya siyo ita ta saka, kusan iri daya ce da wadda ya taɓa gani ta saka a gida ranar da tashi cikin daren nan, me tsawo daga baya amma ta gaba kuma iya gwiwa take kawai, kuma yadda idanunsa suka riƙe hoton siraran kafafunta a wancan lokacin shi yasa kai tsaye yace a mayar da wanda ya ɗauko a ciro masa ita. Daga yanayinta kawai ya san ta saka ne don bata da wani zaɓi, tunda wani mai wanki da guga na Hotel ɗin yasa yazo ya karɓi kayansu don ya wanke zuwa gobe, idanunsa kallonta kawai suke tun daga nan, ta yafa bakin mayafinta da bata bayar dashi ba akanta amma duk da haka gashinta na fitowa kamar ɗazu da safe. Daga inda Amina take tsaye, cakuɗa yatsunta kawai take yi cikin junansu saboda rawar da hannayenta ke yi musamman a yanzu da take ƙara ganin wautarta na fitowa a haka, amma ya zata yi, har tawul a cikin toilet din ta ɗauko ta ɗaura taga abin bai dace ba ta cire shi. A ajiye ma zancen ƙafafunta dake waje a gefe, tunda take bata taɓa lissafawa cewa zata yi kwanan hotel a rayuwarta ba idan har ba wai Makkah ko wata kasar taje ba, wanda shima ba'a irin wannan yanayin take hango shi ba, shi yasa tun da suka shigo zuciyarta ke rabewa gida biyu tana sake haɗewar da har a yanzu ta kasa samun sauƙi duk kuwa da ƙarfin halin da ta tattaro a ranta. Ganin yadda yake kallonta yasa ta juya da sauri ta ƙarasa jawo ƙofar toilet ɗin ta rufe sannan ta shiga tahowa cikin ɗakin. Wani abu ya zarce maƙogwaron Ma'aruf da yake kallonta tana tahowa sai mutstsika yatsunta take yi cikin junansu yayin da siraran ƙafafun nata ke tafiya. Tare da Ruƙayya yasha tambayar kansa meye babban interest dinsa game da mace, sai dai a lokacin ya kasa tsaida zuciyarsa akan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73