Chapter 12
Chapter 12
kawai ta dinga yi a zaman kan nata kamar mai jiran a buɗe mata ƙofar shiga. Shiru ya ratsa ɗaukacin dakin, shirun da a cikinsa Amina ta kasa ko zuƙar numfashi, kuma bata damu da tsayinsa ba don har a lokacin bata gane maganar da Baban ya faɗa ba, shiru kawai tayi kamar bata ji shi da farko ba a yanzu take jira yace wani abu, sai da shi da kansa yaga bata da alamar magana sannan ya sake kiran sunanta. "Amina.." Ta kuwa ɗago ta kalle shi, da idanunta dake haskawa a cikin hasken fitilar ɗakin, sai ya cigaba shima kamar bai fadi maganar farko ba. "Jiya da naje gidan Hajiya Kilishi da mijinta nayi magana ba da ita ba, kiran nasa ne ba nata ba, don da na isa gidan mota kawai tasa aka ɗauke ni aka kaini har ofishin mijin nata. Acan na tarar dashi tare da ƙaninsa, mutane ne manya-manya Amina masu mutunci da kuma kwarjini, kuma kai tsaye suka shaida min cewar aurenki suke nemawa ɗansu, yace min Hajiya Kilishin ita da kanta ta roƙe shi alfarmar hakan saboda yarda da hankali da kuma tarbiyar da muka baki. Al'amarin ya girgiza ni kamar yadda kika ji shi a yanzu kema, amma wallahi a wannan lokacin ba zan iya kallon idanun wadannan mutanen ince musu 'A'a' ba don bani da wata hujja ko dalilin da zai sa in faɗi hakan..." Ba fahimtar abinda yake faɗa Amina take ba har a lokacin, kallonsa kawai take tana jin yadda muryarsa ke karyewa da kowacce kalma daya fada, mahaifinta mutum ne da ta sani jajirtacce, ko a lokacin da yake cikin tashin hankalin karayar arziƙinsa, baya taba fasa binsu da alkawuran cewa zai inganta rayuwarsu don kar su karaya da komai. Amma a yau kiri-ƙiri take jin duk wata amon karaya a muryar tasa, amon da take ji yana bin jijiyoyin ta yana tayar da tsigar jikinta bi da bi ta kowanne ɓangare. "Na san karatu ne a ranki Amina, kuma na san ba sau daya ba sau biyu ba na sha yi miki alƙawarin cika miki wannan burin amma a kullum abinda muke tsarawa daban, wadda ƙaddara ta tanadar mana daban, kuma na san ba sai nayi miki bayanin wannan ba don a ƙananun shekarunki kin gan kalolin ƙaddarar mabanbanta, shi yasa nake son ki kalli wannan ɓangaren ƙaddarar ma, ki kalle ta idanun rahma Amina, Allah ya sani a zuciyata na yarda cewa ban miƙa ki inda zaki wahala ba, don komai halin da zan shiga a duniya ba zan yarda da duk abinda zai cutar daku ya matso kusa ba balle har in kai ku da hannu na. Kin san Hajiya Kilishi kin san kirkinta, kin san yanayin gidanta, ina ga kinje kusan sau biyu ke da mahaifiyarki, saboda haka Amina wallahi zuciyata bata bani cewa zaki wahala a wannan wajen, damuwata kawai shine yunƙurin rushe miki burin ki da nayi da kuma cewar na yanke hukunci a lokaci guda." Yayi shiru a lokacin, Amina ta haɗiye wani abu a makogwaron ta da bata san sunansa ba, maganganun Baba a gefe suke daga cikin kanta, har a yanzu damuwar dake cikin muryarsa itace a gabanta, ita take lissafawa tana son kirga adadinta. A hankali ta juyar da idanunta kan Amman dake zaune a saitinta, kuma a hankalin idanunta suka fahimci abinda ta kasa ganewa a fuskar tata ɗazu, damuwa ce fal ke yawo a cikin nata idanun! Wani abu da ya ƙara rikita tunaninta a lokaci guda... Don bata taba tunanin cewa irin wannan maganar ce zata saka Amma cikin damuwa itama ba, idan har zata iya tunawa tun farko dama ita tafi son zancen aurenta akan karatun da take naci, kawai ganin cewar daga ita har Baban akan son karatun suka tsaya yasa ta sallama itama, amma duk da haka tasha gaya mata cewar ba ba lallai sai ta gama karatun zata yi aure ba, to me yasa wannan maganar zata dame ta? Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa sannan ta gyara zamanta a hankali, tana jin nauyin idanun iyayen nata biyu dake kallonta, so take tace musu in har wannan ne abinda ya tashi hankulansu a gidan tun jiya to su kwantar dashi, don a cikin aure da zancen rashin karatun tana jin ba wanda na zata iya daurewa ba don farin cikinsu. "Baka ƙarasa zancen naka ba ai Mallam, baka gaya mata abinda yafi komai muhimmanci ba." Kamar saukar ruwan sama a lokaci guda muryar Amman ta faɗa, kuma a lokaci gudan Amina taji gabanta ya faɗi, abu muhimmanci tace, kenan wani abu ne daban, wani abu da yafi girman abinda ya faɗa, wani abu da wataƙila shine dalilin damuwar dake kan fuskar Amman da ma zuwansu gidan Kawu mallam a yau. Taji Baba ya sake gyara zamansa sannan ya kira sunanta. "Amina..." Ya kira kamar tayi nesa dashi, kuma ta san me hakan ke nufi saboda haka da sauri ta ɗago idanunta daga kan ƴan yatsunta ta kalle shi, ƙaguwar ya furta abinda zai faɗa na haskawa tar a cikin idanunta. "Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!" A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin! *** A wannan daren.... Wajen ƙarfe tara saura a lokacin da wata mota ƙirar kamfanin 'Elantra' ta shigo cikin layin, ƴan yara maza dake wasa akan hanya suka dinga darewa da gudu cikin wasansu suna bawa motar hanya kasancewar faɗin layin ba zai yiwu ta wuce kuma suna wajen ba. Ko'ina yayi tar da wutar nepar da aka kawo don gaka ƙyallin sabubtar motar haskawa kawai yake yi a idanun mutane kamar an shafe ta da maiƙo. A cikin motar saurayin dake zaune a kujerar gefe mai suna Jamilu ya nuna ƙofar wani guda inda hasken jan kwai ke ci a samansa. "Wancan ne gidan yallaɓai, in dai gidan Alhaji Sulaiman ɗin daka kwatanta min ne to shine gidan." Ma'aruf dake rike da sitiyarin motar a gefen sa ya gyada kai a hankali yana kallon ƙofar gidan shima. "Nagode sosai kaji." Saurayin ya washe baki. "Ah haba yallabai ai ba wani abu wallahi. A sauka lafiya." Ya faɗi hakan da tsantsar murna yana ƙara rike sababbin kudin da Ma'aruf ɗin ya danka masa tun lokacin da ya shigo motar, a can farkon layin ya dauko shi, cikin dandazon wasu samari a inda ake sayar da rake. Kuma duk yadda ya kai ga kwatanta musu gidan Alhaji Sulaiman ɗin da yake nema, saurayin ne kaɗai ya gane don haka ya roƙe shi yazo ya ƙarasa dashi. Saurayin ya rufe ƙofar motar daidai lokacin da kira ya sake shigowa a wayarsa, tun dauko shi dama ake kiran wayar kuma daga nambobi biyu kawai Ishaq da Mami, yana kallon yadda saurayin ma ke ta kallon wayar tun da ya shigo idanunsa na haskawa da mamakin cewa me yasa ba zai ɗauki kiran ba. Ya ƙyale wayar yayi gaba a hankali zuwa daidai kofar gidan da yake kallo ya tsayar da motar daga gefe sannan ya janyo ta. "Ma'aruf kana ina? Ina ka tafi?" Muryar ishaq ta fito a lokaci guda da ya amsa, sai ya koma da baya ya jingina kansa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73