Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka same shi. Amma don rashin mutunci irin nasa bai fito ya same su ba sai da suka yi kusan awa guda suna jiransa, har su Ibrahim da Ahmad da suka je suka taho da police ɗin da aka kai report wajensu, sannan ne ya fito da uzurin cewar wasu abubuwan yake kammalawa da baza su iya jira ba. Kuma duk da irin tashin hankalin da yaji suna ciki da kuma ma babban labari na ɓatan ɗan mutum guda, bai nuna ko a jikinsa ba bayan Allah ya sawwake guda din da ya furta. Ta sani cewa shi kansa Ashraf ɗin yaji haushi amma bai nuna bane saboda abu suke nema daga wajensa dole sune a ƙasa, amma duk da haka ta fahimci cewa akwai wani abu ne da ya faru da babu wannan kalmar ta abota a yanzu tsakaninsu. Sai dai ba wannan ne a gabanta ba yanzu, a cikin kwanakin da suka gabata, zuciyarta ta mutu ta miƙe fiye da ƙirgan mai ƙirga, ƙarya ne ta iya kwatanta tashin hankalin da take ciki, tashi hankalin da sai da ya shafi kowa a gidan nasu gabaɗaya, ya zamana ba abinda ake yi banda fafutukar neman Mary ko ta wacce hanya amma basu same tan ba, hatta mahaifinta dake can ƙasar Romania yana aikinsa kullum sai yayi waya tsakaninsa dasu da kuma ƴansanda akan abinda ake ciki. Idanunta kaɗai idan ka kalla sune shaidar rashin baccin da kuma na abincin da take ciki. Ta rantse a ranta fiye da sau shurin masaki cewar Mary zata gwammace bata zo duniya ba idan har suka kama ta, tunaninta baya iya lissafa abinda ya kamata tasa ayi mata. Sun isa cikin unguwar ta sabon gari a lokacin da duhu ya riga yayi sosai, a lokacin kuma gabanta ya shiga faɗuwa cike da tsananin tsoro ganin irin cakuɗaɗɗun layikan da suke wucewa da kuma mutanen cikinsu, zata yi rantsuwa ba adadi cewa Mary ba zata taɓa rabarsu ba inda ta san daga waje irin wannan take fitowa, amma a haka ta zauna tana kula da ƴarta tsawon watanni bakwai. Kwatancen Bilal ya kai su har wai takurarren gidan da mutane ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, bata san lokacin da ta dunƙule ƙarshen mayafinta akan bakinta ba yayin da kwalla ta shiga fitowa daga idanunta da suka riga suka kaɗa, zuciyarta bata iya kwatanta mata cewa Hamida tana wannan wurin ko kaɗan. Ibrahim da Ahmad da suka fito daga motarsu bayan sun tsaya suka bada shawarar cewa ta tsaya su suka shiga ciki, amma jikinta na rawa ta girgiza musu kai, ruhinta zai bisu ciki ne ko da ta tsaya ɗin. Ashraf da Ahmad ne suka fara shigewa gaba sai Bilal da kuma Ahmad, ita tana daga bayansu sai kuma ƴansanda biyar dake rufa musu baya, warin iskar gidan ta fara shaƙa kafin ta fahimci girman da yake dashi daga ciki, ga tarin ƙofofi birjik daga kowanne gefe inda hayaniya ke fitowa kamar zata fasa kunne. Kuma ganin ƴan sandan yasa hayaniyar gidan ta ƙaru har da masu ihu suna shigewa ɗakunansu, a tsakar gidan su Ashraf da kuma ƴansandan suka shiga tambayar cewa Mary suke nema, kuma wasu ƙattin inyamurai da su kaɗai suka tsaya suka shaida musu cewar Maryn dake gidan sun fi mutum ashirin. Koina a jikin Rukayya kawai rawa yake yayin da take kallon ƙofofin ɗakunan da dukkan fatanta na duniya, da ƙyar da kwatance aka samu wani a cikinsu ya gane wadda suke nema, kuma kai tsaye suka shaida musu cewa kwana biyu da suka wuce Maryn tare da iyayenta suka kwashe kayansu tsaf! suka tafi garin su. Sai da ƙyar ƴan sandan nan suka samu mutanen nan suka fito musu da wani tsoho da akace ɗanuwansu ne. Kuma shima ganin ƴan sandan ya ruɗa shi, ya dinga rantsuwa bai san komai ba sai da yaga da gaske ana shirin tafiya dashi sannan yayi bayani cewar ya san yarinyar da ake neman, kuma har da ita a dalilin barin su Mary garin bayan ciwon mahaifiyarsu. Ruƙayya gabansa taje ta tsugunna a lokacin yayin da yake bayani da gurɓataciyar hausarsa. "Wani mutum ne anan yazo ya dauki yarinyar ya tafi dashi, kuma Mary yace ya bawa yarinya maganin bacci mutumin zai kamata, kuma the madam she's serving zai ce ta ɓatar da yarinya, ita bata san yadda zata yi ba, don haka sun kwashe kaya nasu sun tafi." "Shi mutumin da yazo ya tafi da yarinyar waye shi?" Wani daga cikin ɗansandan ya tambaya tsaye akansa. "Mary yace shine oga na inda babanshi Mr. Okafor yake aiki." "Ka san wajen aikin nasa?" Ya ɗago cike da tsoro yana kallon ɗan sandan. "Ka san wajen da baban nata yake aiki?" Wannan karon Ruƙayya ce ta tambaya, muryarta na rawa da dukkan fatan na cewar amsar da zai bayar ta kasance abinda take son ji, kuma cikin abinda zata iya kira da sa'a, sai ya daga kansa yace. "Eh ya sani, wajen inda ana..." Bai karasa ba ɗan sandan ya bashi umarnin tashi su tafi, jikinsa na rawa ya miƙe tsaye ya shige gaba, aka sanya shi a motar ƴan sandan bayan sun fita, suka fara yin gaba sannan su kuma suka shiga nasu motocin suka bi su. Wannan karon Ibrahim ya shigo motarsu ya zauna a wajen Bilal da shi ya koma motar Ahmad, tana ji kowannensu na waya, Ashraf da matarsa yana gaya mata inda suke, Ibrahim ɗin kuma da Daddy yana yi masa bayanin abinda ya faru. Fuskarta ta juya waje idanunta na bin fitulun kan titi ke haskawa akan gilashin da kuma fuskarta, hawaye take sharewa da gefen mayafinta yayin da hannyenta ke rawa kamar zuciyarta, bata iya hango yadda zata kasance idan har bata sami Hamida a wajen nan ba. Sun iso daidai gaban wani dogon gini mai ɗauke da gilasaivda kuma fitulu kamar rana, akwai manya-manyan rubutu a sama wanda bata iya karantawa ba saboda halin da take ciki da kuma ƙwallar da ta taru a idanunta. Ashraf da ya tsayar da motar ya juyo ya kalle ta, kuma ganin yadda take share hawaye yasa ya girgiza kansa yace. "Stay inside, bari muje mu gani." Da haka ya buɗe ƙofar motar ya fita, Ibrahim na bin bayansa. Sai kawai ta kifa kanta akan cinyoyinta ta shiga rera kukan da take kasancewa a cikinsa duk dare, gani take idan har ta rasa Hamida rayuwarta ta gama rushewa gaba ɗaya, ba lallai ne ta samu fatan da dashi take ganin zai sake gina rayuwarta ba. Don samun Ma'aruf shine ƙarshen fatanta yanzu a duniya, bata hango komai a gabanta sama dashi, wani gefe na zuciyarta na jin cewa zata iya hakura da Hamidar ma idan har rayuwa zata iya dawo mata da Ma'aruf ta wata hanyar, amma ta san daga shi har iyayenta babu mai sake kallonta idan babu yarinyar, don haka ba zata taɓa rasa ta ba. Wayarta tayi ƙara a lokacin daga gefenta, ta kalli screen ɗin tana karanta sunan Jawad da ya fito tar! akai, tun da ta barshi a hotel ɗin nan bata ƙara bi ta kansa ba, ya kira wayarta sau da yawa bata ɗaga ba, a jiya da yamma har gidansu yazo amma ta aika masa da saƙon ba zata

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});