Chapter 54
Chapter 54
girgiza kanta sannan tace. "Kar ka damu Awwalu, ina sane dashi so nake ya kammala da mutanen RTL ɗin nan tukunna, idan sun gama daidaitawa kuma kuɗaɗen sun shigo zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne, kafin ya dawo hayyacinsa munyi gaba da kuɗin kuma munyi gaba da shi Mr. Okafor ɗin... Kamar koyaushe sai bayan ya tashi zai fara lalube cikin duhu!" *** #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA BIYU. Life is what happen to us when we are busy making other plans. -Unknown. ** Ranar lahadi ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma, Amina na tare da Samirah da kuma Munaya a kitchen suna aiki tare da hirarsu wanda mafi yawanci Samiran ce ke tsokanar Munaya akan zuwan da tayi, tunda tun farko Samiran ce ta fara zuwa kafin ita kuma ta shigo m daga baya. "Wallahi sai ayi baƙi kashi-kashi su zo gidan nan su tafi baki ganta ta fito ba, amma kiga wai itace yanzu tazo taya aiki babu gaira ba dalili." Cewar Samiran a lokacin da take daka tafarnuwa ƴar kadan da zata saka a miyar dake kan wuta daga bayanta. Munaya tana yanka carrots ta ɗago ta kalle ta tace. "Ki kara faɗar abu guda ɗaya ki gani idan ban jefe ki da grater nan ba." Amina tana murmushi daga inda take blinding abarba tace. "Ki ƙyale ta haka mana Samirah, shikenan don tazo sai da dalili? Da nan da cikin gidan ai duk ɗaya ne." Samiran ta girgiza kanta. "Ba zaki gane bane Aunty Amina, saura fa sati biyu ta fara exams, da su Zahra suna nan zasu gaya miki a irin wannan lokacin ba'a ganinta wallahi, idan ta shiga ɗaki sai ta yini akan littafi sallah ce kawai ke tada ita, ko Hajiya sai dai tayi ta faɗan taci abinci, Allah karatun da take yi har na gama rayuwata a duniyar nan ba zanyi rabinsa ba..." Bata karasa ba kuwa lokacin da Munaya ta saita daidai bakinta da wani katon karas din dake gefenta ta jefe ta dashi, amma duk haka Samiran bata yi shiru ba, ta cigaba da bayanin ta tana faɗin ita bata yarda da zuwan nan nata ba sam, wanda ke saka su dariya. Amina ta tsiyaye ruwan abarbar a hankali cikin wani katon bowl tana kokari kar ya taɓa ciwon hannunta da bata daɗe da jinsa ba wajen yanka albasa, tana jinsu har yanzu Munaya na rokonta akan ta kyale ta amma Samiran taki yin shiru. Munaya tana da saukin kai sosai, don tazarar shekarun dake tsakaninsu da Samiran da ɗan yawa, amma idan suna hira irin haka ba zaka ce ba, ta juya tana kallonsu, ita kanta dai ta ɗanyi mamaki zuwan Munayan tunda tun bayan ranar da suka zo gabaɗaya suka gaisa sau ɗaya ra kara shigowa ranar da suka yi zancen littafin nan. Samirah ce dama kusan kullym zata leko ɗan bsyami ko saƙonta, a dazu ma tazo kawo mata wata darduma ne mai kyau daga Hajiya Maimuna taga tana aikin shine ta tsaya don ta taya ta, bata daɗe ba kuma sai ga Munayan itama ta shigo, ganin suna aikin yasa itama ta tsaya taya su. "Ki cigaba Kar ki fasa, I have my ways of torturing you kin sani wallahi." Munayan ta faɗa yayin da suke dariya dukkaninsu, Amina ta ɗauko bowl din da ta juye ruwan abarbar ta taho don ta saka shi fridge ya ɗanyi sanyi kafin ta ƙarasa abinda zata yi tazo haɗa lemon. Fridge ɗin yana daga gefen kofar shigowa kasancewar shine na karshe a yadda drawer kitchen ɗin take a jere, don haka ta taho wajen daidai lokacin da Ƙofar kitchen din ta buɗe Ma'aruf ya shigo ciki, yana sanye da wata loose riga fara mai dogon hannu, gashin kansa a barbaje kota'ina kamar yadda yake tun safe kasancewar bai fita ba yau, amma babu banbanci da cewar yana nan din, don tun safen yana ɗakinsa yana faman wani aikin a computer, banbancin jiya da yau shine a yanzu fuskarsa fayau take, babu gajiya irin ta jiya ko kadan, ya riga ya manta duk wannan tunanin meeting din nan, don bayan dawowarsa a jiyan ya bata labarin cewa komai ya tafi daidai tsakaninsu da mutanen da suka yi meeting ɗin. "Kinyi addu'a mai kyau kuma Allah ya amsa." Kalaman da ya gaya mata kenan a jiyan wanda ta kwana suna yawo acikin kanta. Shi yasa a yau ma da safe breakfast mai daɗi suka yi yana kara gaya mata irin nasarar da suka yi suka shawo kan mutanen nan ɗaya kamfanin suka kulla alakar kasuwancin a tsakaninsu, hirar dake ƙara sawa tana fahimtar abubuwansa da yawa, tana jin zuciyarta na canjawa game da tunaninta akansa, wasu abubuwa da yawa a cikin kanta na gaya mata cewa ba shine wannan Ma'aruf ɗin da ya bata wannan saƙon ba... Ba shine kuma wanda Iyayenta suka gaya mata yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba. Shi yasa ko da ya gaya mata cewa Ishaq ɗin da suke waya kullum ya dawo daga tafiyar da yayi zai zo a yau, zuciyarta tayi tunanin aƙalla ta tarbe shi da irin tarbar da ya kamata, ba don komai ba sai don ta san hakan ne ya dace kuma ko zata yiwa kanta ƙarya ta sani cewa tana son yadda zamansu ke tafiya duk kuwa da yadda koina a tunaninta ke gaya mata cewa akwai abinda ke shirin faruwa. Ƙafarta ta ƙarasa wajen Fridge ɗin ne daidai lokacin da ya shigo, taga idonsa ya haska da mamaki yana kallon su Munayan da kuma aikin da suke yi. "Me yake faruwa anan?" Muryarsa tasa dukkaninsu juyowa a lokaci guda, kuma a taken fuskar kowannensu ta faɗaɗa da murmushi yayin sa Munaya ta kira shi cikin wani abu mai kama da waƙa. "Yayaaaaa B...." A ƴan kwanakin nan Amina ta fahimci kusan duk sanda suka ganshi haka ne, haka gaisuwarsu ke farawa kamar sun daɗe rabonsu dashi, hakan ya tabbatar mata cewar ba ganinsa suke yi sosai a baya ba, a yanzu ne lokaci ya kawo musu shi kusa dasu wataƙila kamar yadda suka saba a ganinsa a baya. Kuma kafin tace wani abu, dukkansu suka ajiye mata aikinta sunyi wajensa, wani abu ya faɗa a zuciyarta ganin yadda kowannensu fuskarsa ke ɗauke da fara'a sun baibaye shi da maganganun da kallon fuskokinsu kawai yake yi, ba irin Samirah da ta shiga bashi labarin da ta gama bata a ɗazu na wani competition ɗin kamfanin Maggi da aka zaɓe ta zasu je suyi a Abuja, Munaya kuma tana ta maimatawa wai ta gaya masa labtop ɗinsa take so ko kuma ya siyo mata wata sabuwa irinta... Me yasa ne wai take tunanin akwai wani rami a rayuwar waɗannan mutanen? Tana jiyo muryoyinsu har lokacin da ta shiga store don neman wani abu ba tare da ita taxe komai ba, kuma ba'a daɗe ba taji an ƙwankwasa kofar store ɗin dake buɗe a hankali sau biyu kafin muryarsa tayi magana a bayanta. "Akwai ruwa anan?" Ta juyo ta kalle shi, yana tsaye daga ƙofar store ɗin, ta manta cewa ruwan dake ajiye a kitchen ya ƙare tun dazu kuma bata fito da wani ba, don haka da sauri ta juya bayanta inda katan din ruwan yake a jere
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73