Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Farar Wuta Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsaf da ƙasa. "Ko baki ɓata kanki ba meye amfanin zuwa wajen yashi da magriba Hafsa?" Amina ta faɗa a hankali tana kama wata jelar, don ita ko kaɗan ba ta fadan nasu take yi ba, jikinta ne kawai zaune a gidan amma hankalinta ruhinta zarya kawai suke a hanyar gidan Kawu mallam kamar tururuwa, shi yasa ko girkin daren ma tace Maryam tayi. Allah ya sani abu na ƙarshe da zata so a yanzu shine wata matsala ta sake gifta musu, rayuwarsu ta haska da kaloli mabanbanta a shekarun baya, sun fuskanci abubuwan da ko a labari basa son tunawa, kuma har yanzu ƙoƙarin tashi suke, ƙoƙari Baba yake don ganin rayuwarsu ta daidaita ko da ba kamar a baya ba, don haka ta yaya zasu taɓa son ace sai sun sako daga farko idan wani abu ya sake gifta musu ya a yanzu... Har sai da ta gama wankewa Hafsa gashin nata da karkashi sannan Amma ta dawo, Baba kuma bai shigo ba sai bayan sallar isha, wanda kafin ayi hakan har Aminu ya riga su dawowa, a tsakar gidan ya tarar dasu tana sake yiwa Hafsa wata kalbar bayan ta wanke matta kan, yayi wanka yazo ya zauna a cikinsu shima yana ta mita da tsokana akan girkin da Maryam ɗin tayi, jollof din shinkafa da taliya ce da ko a ido tayi kyau, amma tunda ya zauna yake sukar abincin yana kuma kai loma. "Wallahi akayi miki aure kika je kina irin wannan abincin sati daya zaki yi ya koro ki, ace jollof amma ba mai sa faman kora ruwa nake kamar dambu nake ci." An kawo wuta a lokacin don haka tsakar gidan yayi tar da wasu sababbin ƙwan fitilar da ya haɗa da kansa ya saka musu. Maryam da a lokacin take wanke uniform dinta daga can bakin famfo tace. "A haka babu man kake ƙoƙarin tayar da plate din ai." "To idan ina jin yunwa ya zanyi? rufa miki asiri kawai nake ma wallahi, don yanzu ina tafiya wajen Isah (mai shayin layinsu) kowa sai ya gane cewar a gidanmu ba'a iya girki ba kenan, kinga masu kokarin zuwa nan gaba ma sai su fasa. Kuma Amina ita ta riga ta samu kece a ruwa." Maryam ta juya bayanta amma yana ganin adadin yadda gefen fuskarta ke juyawa wajen murguɗa baki tana faɗar wasu abubuwa da ba jin su yake ba. Yayi murmushi yana sake faɗin. "Hotonki zan nemo a wayata in maida shi fari da baki in rubuta ga matar da akan girkinta aka ƙirƙiri sunan abincin 'Ci kar ka mutu, 1987.'" Bai saurari abinda take cewa ba ya juya ya kalli Amina da bata sanya baki a hirarsu har yanzu ba, ganin damuwar dake kan fuskarta har a lokacin ya dawo da hankalinsa kanta sosai. "Wai har yanzu damuwa kike? Nace miki fa ki kwantar da hankalinki tun dazu. Ni alamar ma da na gani kamar wasu maƙudan kuɗi Baba ya samo shine aka tafi gidan Kawu mallam ɗin ake ta faman lissafi." Ba shiri dole Amina tayi murmushi tana kallonsa. "Aminu Allah ya shirye ka, komai sai ka maida shi wasa wallahi." "To me yasa zaki yi ta damun kanki akan abinda bai ƙaraso ba tukunna." Ya faɗi hakan sanda ya juyo, idonsa ya kai kan hannun Maryam dake ta cuɗa kayan wankinta. "Ke, idan kinyi ƙunshin nan ma haka zaki cigaba da irin wannan wankin? Kwana biyu ya goge? Kuɗina zaki taso ki dauko min Allah indai haka ne." "Kudin ka ai sun riga sun shigo kenan wallahi baza su dawo ba, sai dai idan nayi ƙunshin ka kankare shi." Amina ta kalli yadda yake murmushi yana kallon Maryam din, ta san shima ya damu, watakila damuwar ma har tafi tata, amma haka Aminu yake a kodayaushe, shi mutum ne da zai sa kaji kamar baka da wata matsala koda kuwa kana nutsewa a cikinta ne tsamo-tsamo. Lokacin da Baba ya shiga tashin hankalin karayar arziƙinsa, Amma tace Aminu shi ya ɗauki kaso mai yawa bayan addu'a wajen dawo dashi daidai. A daidai lokacin Amman tayi sallama ta shigo, kuma kallonta kawai Amina tayi taji gabanta ya faɗi duk duk da cewar yanayin damuwar fuskar tata ya ragu akan da safe. "Haba Amma kun barmu sai kace marayu a gidan nan, ko shirin yaƙin duniya kuka tafi yi yaci ace kun gama." Duk da yanayin Amman sai da tayi wani guntun murmushi tana girgiza kai sanda suka shiga yi mata sannu da zuwa, don ta saba a irin lokutan wasansa, Aminu ya riga ya mayar da ita kamar kakarsa. A lokaci guda sai komai ya dawo daidai a gidan, da duk yawansu ji suke kamar a cikin wani fanko suke, Adam ya dawo daga siyan wainar fulawar da Maryam ta aika shi, Aminu ya kafa ya tsare cewar sai yaci rabi don wai ya san da kudinsa ta siyo, duk dauriyar Maryam sai da ta rufe idaninta ta fito da duk masifar dake cikinta wanda dama abinda yake jira kenan don haka shi da Adam suka dinga kyalkyala mata dariya. Sannan a ƙarshe bayan sun shiga falo, wani film din indiyan da ake yi a tashar Bollywood ya ɗan daukewa Amina hankali daga wannan damuwar ganin cewar Amman ma har ta sake tana kokarin sakawa Hafsa maballi a wuyan rigar makarantar ta, tana yi tana mitar yadda Hafsan ke yawan yar da maɓallan rigar. Falon ya ɗauka da sautin wakar film ɗin da ake yi lokacin da take ke kallon fuskar kowa tana murmushi, yadda Hafsa ta zuba manyan idanunta tana saurarar kashedin da Ammar keyi mata akan maballin, da yadda Aminu da Adam ke cigaba da dariya tsokanar Maryam da bata ganewa ta daina biye musu, har ma da idanun Maryam ɗin da suka cika da haushi fal! Haka take so... Haka take so rayuwa ta kasance musu a kodayaushe. Sai dai rayuwar bata taɓa biyewa muradan zuciya, ita da zuciyar ma sunyi hannun riga, ƙaddara take kallo a kodayaushe tana bin takunta, don a lokacin da Baba ya dawo bayan sallar isha a lokacin komai ya ruguje, zuciyar Amina ta sake ruftawa cikin ramin da yafi wanda ta fito daga cikinsa zurfi. Su Hafsa suna makarantar dare a lokacin, Aminu kuma ya fita wajen abokansa sannan Maryam da wata ƙawarta sun tafi bakin titi wajen mai yin zayyanar allo kasancewar suna dab da yin sauka a islamiyya, gidan ya rage sai ita kaɗai, kamar dama ƙaddarar ta zaɓi wannan lokacin ne don ita kadai ɗin. Amma ta kira ta zuwa ɗakin Baba lokacin da take kokarin haɗa kan kitchen ɗinsu, kiran daya tabbatar mata da cewar abinda take jira ne zai kasance kuma a hanyar zuwan tunanin ta ya ɗan ɗaure don a zaton ta ita da Aminu ya kamata su zayyane wa komai. Ta shiga ciki lokacin da Baba ya rufe flask din nasa abincin da ya gama ci, ta zauna a daidai saitin Amma da har a lokacin ta kasa tantance yanayin fuskarta. "Amina jiya da naje gidan Hajiya Kilishi aurenki na bayar ga ɗansu." Maganar ta fito daga bakin Baban kai tsaye ba wane shamaki balle kewaye kewaye, kuma ta tafi kai tsayen har zuwa cikin ƙwaƙwalwar ta, sai dai bata nutse ba, zagaye

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});