Chapter 44
Chapter 44
screen ɗinta, kuma sunan da ya karanta na farko akan call log din ya sashi jan tsakin da bai shirya ba. "Ban san ranar da asirin da yarinyar nan ta naka zai karye ba Jawad, har sau nawa zan gaya maka ka rabu da wannan tsilar abar, ub*n me zata tsinana maka da baka samu ba a duniyar nan? You're young, kana da kudi, kana da status mai kyau, kana kan lokacinka Man, sannan babu yarinyar da zaka kalla duk kasar nan ka kasa samunta. Me yasa ba zaka yi hankali ka fahimci cewa wannan yarinyar sharri ce ma a rayuwarka ba?" Jawad ya lumshe idanunsa ya bude yana saurarensa ta cikin sautin kidan dake tashi daga can kasa kuma sai da ya kai har karshe sannan ya girgiza kansa, idanunsa na kallon fitilar dake samansu mai kala-kala a cikin duhun wajen yace. "Ba zaka gane ba Haro, ba zaka gane abinda nake ji bane, na rantse da Allah idan Ruƙayya bata aure ni ba, ba zata sake auren kowa ba a duniyar nan!" *** "What do you find? Me ka samo?" Faruk ya tambaya riƙe da Tab ɗin hannunsa yana kallon Ma'aruf dake kokarin fitar da lissafin da suka kwashe fiye da awa guda suna yi akan kamfanin wasu abokan kasuwancinsu da suka gano cewar suna da nasu kamashon cikin wannan mummunar asarar da har yanzu suke bincike akanta. Suna zaune ne daga cikin office din Ma'aruf ɗin, bayan kusan jiran awa uku da Faruk din yayi yana jiran dawowar Ma'aruf da ya bar office din tun kusan sha ɗaya na safe. Kuma sai da ya dawo sannan ya buɗe email dinsa ya karanta bayanan da Martha sakatariyar tasa ta turo masa sannan suka fara haɗa komai suna tarawa da ƙaiyadewa. "So shi wannan Mr. Ishmael Grahm ɗin shine ya karbi aikin accountant ɗinsu a farkon shekarar nan kenan kuma sunansu ɗaya da wanda ya tafi har surnane ɗin." Ma'aruf ɗin ya faɗa, idanunsa manne da tab ɗin gabansa yayin da muryar tasa ta fito kamar ta ƙwace ne daga cikin tunaninsa. "What a ina ka ga hakan? Dama sun canja accountant ne? When?" Faruk yayi tambayoyin yana komawa cikin kan tasa wayar. "A cikin wanda ka min sending zaka duba, anyi naming dinsa 13th March na wannan shekarar." Kuma sai da Faruk din ya kusan zuwa can ƙasa wajen nemowa kafin ya isa inda yake gaya masan, idanunsa suka ƙanƙance yayin da yake karanta bayanin dake wurin. "Bala'i! B ya akayi hankalinka yaje wajen nan, I was goung through it fa tun safe amma wallahi ban gani ba." "Shi yasa na gaya maka na kusa korarka daga aikin nan, ban san me yake ɓata maka tunaninka ba kwana biyu." Dariya Faruk ɗin yayi yana cigaba da karantawa kafin yace. "Aikin Shahida ne wallahi, tunda ta yaye Aarif nake ji kamar watannin farkon auren mu muka koma." A lokaci guda Ma'aruf ya tsaya da karanta abinda yake yi ya juyo ya kalle shi, sai kuma ya girgiza kansa sannan yace. "Baka da hankali Faruk, na daɗe ina gaya maka." Faruk ɗin ya sake yin dariya yana daukar tambulan ɗin lemon da Martha ta kawo musu kafin yace. "Inji wanda yake amsa sunan sabon ango, you didn't even tell me ya yarinyar take." Yaya yarinyar take. Maganar ta sake tuno masa da fuskarta a yau da safe kafin ya fito, sati guda kenan da yin auren, kuma a cikin sati gudan nan baya jin magana ta haɗa su wadda tafi kirgen cikin yatsu, wani lokacin dai su kan haɗu da asuba idan jamlock ɗin kofar falo ya rufe bayan ya fita masallaci, zata zo ta buɗe masa idan yayi knocking sanye da dogoon hijabinta har kasa, ranar farko bata ce dashi komai ba, amma a rana ta biyu ne ta fara gaishe shi. Sannan kuma sau da yawa idan ya koma da daddare zai ganta, har ya fahimci wani lokaci ma tana fitowar ne kawai don ta gaishe shi. Bayan hakan maganganun da suka haɗa su baya jin sun wuce biyar, ya san ranar juma'a da zai fita masallaci ya tambaye ta dardumar sallah ta dauko wata sabuwa kuwa fil mai laushi ta kawo masa, sai kuma ita da ta tambaye shi Panadol ya fita da kansa ya siyo mata, amma bayan hakan baya tunanin wata maganar ta kara hada su don baya son ya takura ta ko kadan, so yake hankalinta ya kwanta ta fahimci cewa da gaske ba abinda zai mata, don a o farkon nan ya lura cewa da gaske a tsorace take dashi. Ya rasa irin tasiri kalamansa suka yi a zuciyarta, ya kasa gane ma me yasa ta yarda da auren idan har tana tsoronsa haka, wataƙila laifin tun na wannan ranar ne, da ta fito ya ganta, da tun a lokacin zai san tayi ƙanƙanta yayi mata wannan barazanar, don haka yake son da kanta ta karkade duk wani tunani da take yi game dashi da kuma damuwar kalaman nan. A shekaranjiya da yaji tana waya da wata tana yi mata bayanin cewa har yanzu bata fara girki ba, a cikin muryar tata yaji da wani abu kamar damuwa, wani abu da ya tsaya masa a rai yasa yasa ba shiri a lokacin da ya shiga cikin gida yaji Mami na yiwa Malam Sani lissafin cefenan wata, ya bishi a baya ya ƙara masa wasu kuɗin yace duk abinda ya siya na cikin gidan ya sake siyan rabin sa ya kai mata. Komai na wannan auren daban yake da lokacinsa da Rukayya ya sani, babu abu ko guda daya da zai danganta shi da farkon wancan ɗin, kamar komai ɗin yana zuwa ne a kishiyar ɗayan, sai dai abu daya kawai zai iya dorarawa shine a yanzu yana jinsa mutum mai ƴanci tunda babu ruwanta dashi sabanin a wancan da kwanakin farko suka sa shi yaji kamar an tsare shi a wani waje ne da lissafin abubuwan da ya kamata yayi. "Kaji ai matsalata da kai kenan, da an taɓo wani zancen ba na aiki ba you lack interest, na tabbata da nayi ta jiranka ma anan wani aikin ka tafi yi." Faruk ya faɗa yana jawo shi daga cikin tunaninsa, kuma ba tare da ya juyo ya kalle shi ba yace. "Saboda ni ba mutum bane kenan bani da wasu personal problems, to ka leƙa motata ka gani wanki naje na karɓo sannan na karbo ɗinki, har B&L naje samo maigadi, sannan na tsaya a zoo road nayi aski." Faruq ɗin yana nazarin sumar kansa da banbancin ta kaɗan ne da yadda ya ganta jiya, yace. "A haka wannan gashin naka an aske shi?" Ya girgiza kansa har yanzu bai kalle shi ba yace. "A'a fixing nayi." Sai kawai Faruq ɗin yayi dariya sannan ya juya kan tasa tab din dake blinking alamun shigowar wani sabon saƙon, suka cigaba da tattauna duk abinda ke gabansu har magariba ta tadda su anan, wanda kafin magaribar suka yi sa'ar ganowa cewa tabbas wannan kamfanin sun karbi kaya na maƙudan kuɗaɗen a hannunsu kuma dukkan receipt din kudin an saka adadin kudin daidai, har ma da alert din shigar kudin cikin bankin kamfanin, amma takardar da Faruk ɗin ya gano cewa an duba balance a wancan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73