Chapter 55
Chapter 55
ta buɗe na saman ta ɗauko ɗaya, yana tsaye yana kallonta har ta ƙaraso ta miƙo masa, kuma ga mamakinta tana ƙarasowa sai kawai ya hado robar ruwan da hannunta gaba ɗaya ya jawo ta zuwa gabansa, ƙafafunta suka taho dab dashi yayin da ya dago da hannun nata yana kallo, ba shiri numfashinta ya katse a ƙirjinta lokacin da yasa ɗan yatsansa ɗaya ya taɓa daidai wajen data yanke ɗazu. "Me ya faru?" Muryarsa ta fito a yana kallon ciwon. Sai da ta haɗiye yawu tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin tace. "Da wuƙa na yanke." "Me kika saka a wajen toh?" Muryarsa ta sake tambaya a hankali ta yadda har tana jin ƙarar wukar da Munaya ke amfani da ita daga can kitchen ɗin, da kuma nuryar Samirah da ta fita waje tana waya. Ta sake haɗiye wani yawun a makogwaronta. "Ba komai na wanke ne kawai." Sai ya kawo daya hannunsa yasa su duka biyu ya rike natan, sannan ya buɗa ciwon sosai don yaga zurfinsa, zafin ya tafi har cikin kanta ta runtse idanunta da sauri tana cije lebbenta, sai yayi saurin sakin wajen sannan ya rufe yatsan nata da duka hannayensa biyu kafin yace. "I'm sorry na duba ne na ga yadda yayi and it was deep." (kuma yayi zurfi.) Ta buɗe idanunta a hankali sannan ta ɗaga kai ba tare da tace komai ba, kuma bai saki hannunta nata ba sai ya cigaba da rike shi yana kallonta, hakan yasa ta ɗago da idonta kalle shi da ɗan ƙaramin mamaki. "Aikin me kuke yi haka?" Ya tambaya tun kafin tayi wani tunanin, sai ta girgiza kanta. "Abinci ne kawai." "Kala-kala haka?" Muryarsa ta sake fitowa da wani abu da ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta yana kassara ƙarfinta, taji kamar wani yana zazzaga mata wani magani mai karfi ne da aka haƙiƙance zaiyi tasiri akanta, kuma a yadda tata muryar ta fito tana rawa, kamar dama anyi mata baki ne cewar hakan ne zai faru. "Kace abokin ka zai zo." "Ishaq?" Ya tambaya kai tsaye sai kuma ya sake cewa. "Ya salam duka saboda shi kuke yin wannan aikin?" Shi ko kadan unaninsa bai kawo masa cewa don Ishaq ɗin zai zo ya kamata ayi wani abu ba, duk da a baya ma idan zaiyi baƙi Ruƙayya kan shirya musu wani abun amma a yanzu ya riga ya manta da hakan kwata-kwata, saboda haka a lokaci guda zuciyarsa taji dadin hakan, sai kawsi ya gyada kansa yana kallonta sannan yace. "Thank you." Ta ɗaga kanta da sauri itama tana fatan hakan ne karshen zancen nasa, don bata san me zata zama ba idan har ya cigaba da magana rike da hannunta a hakan. Kuma kamar yaji fatanta, sai ya zare hannunsa nasa a hankali, taji ɗuminsu yana barin fatarta. "Zan nemo abu in rufe miki ciwon anjima insha Allah." Da haka ya juya ya fita rike da robar ruwan a hannunsa. A lokaci guda Amina taji kamar numfashinta yayi wata tafiya mai nisa ne sai a yanzu take iya zuƙo shi, ssi kawai ta juya itama ta ɗauko wata robar ruwan ta balle hancinta ta shiga sha yayin da bayanta ya jingina da drawers din store ɗin. Sai da ta kusa shanyewa sannan ta tsaya, tasa bayan hannunta tana goge wanda ya zuba a gefen bakinta. Bata san me yake shirin fara damunta ba amma koma meye, so take ta tunawa kanta cewa duk abinda ke faruwa wannan gaske ne ba labari ba da komai zai tafi daidai, abubuwa ba zasu tafi kamar a mafarki tare da mutumin da daga shi har ita basu san juna ba sai bayan aurensu kuma har yanzu bsta san manufarsa akanta ba. Ma'aruf ba zai taɓa sauko da kansa haka akan ita ɗin da ba kowa ba, don ta sani cewa bayan matar daya aura Allah kadai ya san matan daya sani a a rayuwarsa ko ma wanda yake tare dasu a yanzu, to don me yasa hankalinsa zai tsaya akan ita din da ba kowa ba, ita ɗin da sa baiyane yake cewar ba sa'ar rayuwarsa bace. Ta girgiza kanta tana kokarin rufe robar ruwan, wannan lokacin kamar zubar ruwa ne kawai kafin zuwan tsawa, kamar iska ce mai daɗi kafin guguwa, sannan kamar kaɗawar ruwan teku ne a hankali kafin ambaliyar sa, akwai wani abu dake jiran ta bayan wannan, kawai dai dan adam baya taba sanin lokacin da ƙaddara ko kuma wata masifar rayuwar ke zuwar masa ne. Muryar Amma ta cikin mafarkin nan ta gifta a cikin kanta lokacin da take cewa "Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina..." A hankali tayi ajiyar zuciya tana fatan Allah yasa koma meye ke shirin faruwa ta iya tunkararsa da ƙafafunta a tsaye, daidai lokacin da a zahiri ta jiyo muryar Samirah ta shigo tana kiranta. "A ina kika ajiye sugar?" Sai kawai tayi sauri ta ƙarasa goge bakinta sannan ta ajiye robar ruwan ta fita. **** Karfe Bakwai daidai Ishaq ya iso, kuma Amina bata san me ya faru ba, don minti biyar bayan zuwansa sai ga sallamar ɗaya abokin Ma'aruf da shima ta riga ta haddace shi a waya mai suna Faruk. Su uku kaɗai suka cika falon da surutu kamar su biyar, kuma duk yadda take ganin Ma'aruf na da magana sai a lokacin taji nasa mai sauki ne, don kafin taji muryarsa taji tasu da yawa musamman Faruk ɗin, don shi yafi Ishaq yi mata magana sosai ma, har matarsa da ƴaƴansa yayi alkawarin kawo mata tunda yace yanzun a sama kawai Ma'aruf ya kira shi yace masa yazo. Kuma har lokacin da suka zo ɗin su Munaya basu tafi ba, Samirah dai taso tafiya amma sai Munayan tayi ta roƙonta akan su ƙara tsayawa tukunna, wani abu da ya ƙara bawa Amina mamaki don ita kanta ta san babu wani dalili Munayan ba zata yi ta cewa su tsaya ba. Ilai kuwa a lokacin da suka je kai musu abincin nan, a lokacin ta samu amsarta, saboda idon Ishaq na kan Munaya tunda suka shiga har ta juya Kitchen don ta ɗauko wani abun, kuma zata rantse ma taga sanda suka yiwa junansu murmushi lokacin da take zuba masa lemo, Allah ya sani yau ta fara ganin Ishaq ɗin amma sai taji zuciyarta na jiyewa Munaya daɗi idan har hasashenta akansu gaskiya ne, don duk inda nutsatsen namiji yake za'a saka Adam a wannan layin, kuma itama Munaya babu ruwanta da wani hargitsi sam. Sun ji daɗin tarbar da suka samu kwarai, don ba'a kalamansu kaɗai ta fahimci hakan ba, har a fuskar Ma'aruf da kuma yanayin kallon da yake mata tun lokacin da taje ta sako wani dogon hijabi bayan shigowar su, wani abu da ita kanta taji ta kyauta da tayi hakan. Bayan sallar isha'i ne sannan suka yi musu sallama suka fita, kuma sun daɗe a waje suna magana don har bayan tafiyar Faruk ɗin shi da Ishaq suna nan, har su Munaya suka tafi ta ƙarasa wanke iya kwanukan da aka ɓata kasancewar basu tara wanke-wanken ko ɗaya ba dama a ɗazu. Kuma tana sallah lokacin da ta jiyo ƙarar fitar motar Ishaq ɗin, sai dai har ta idar ta gama addu'o'in ta da komai bata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73