Chapter 9
Chapter 9
wayar a kunnena. "Hey!" Na faɗa. "Muryarki ta yi mini daɗi a zuciyata, ita kaɗai dama nake son ji ko hankalina ya daɗa ƙwanciya." "Wa ke magana ne ban gane ba?" "Yasmin mijinki ne." Na yi murmushi na kashe wayar. Ina aje wayar ƴan matan suka yi mini sannu da dawowa na amsa masu tare da ɗan ɓata mintuna biyar a wajensu, domin in basu nasu haƙƙin, na lura kuwa hakan na yi masu daɗi matuƙa. Ina hawa ban tsaya komai ba sai hidimar wanka, saboda ganin magriba ta kawo jiki sosai. Yau kam addu'ata ta sha bamban da ta kullum, tunda yau na yi ta ne a kan Allah yasa Yarima ya ci gaba da sona har abada,ni kuma Allah yasa inji ina son shi,in gane son in aikata shi nima, Allah yasa in dinga yi wa Yarima biyayya a kan duk abin da ya umurce ni da shi. Ƙarar wayata ita ta ɗan sa na waiga na kallo ta saman gadona, har na kawar da kaina manufata ba zan ɗauka ba, sai na yi tunanin ko Aunty ce, wannan tunanin ne yasa na miƙe cikin ɗan hanzarina na isa ga wayar tawa. Yarima na ga an ƙara rubutawa. Na yi murmushi na kanga a kunnena. "Don't say hello to me. Saboda muryarki na rikita ni, ina gayyatarki cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau." Kafin in yi magana har ya kashe. Na koma da baya na ƙwanta saman gadona na lumshe idanuwana haɗe da murmushin daɗi,nan take na tambayi kaina shin ko dai ina son Yarima ne? A take na ji ƙwayar idanuwana na karanto mini fuskarshi,shin ko wannan shi ne son? Na yi saurin tashi ina girgiza kaina,kai a'a,ni na san ba na son Yarima. Na yi tsaki na miƙe na nufi ƙasa wajen ƴan matan gidana. A hankali suka dinga ba ni labari,a nan har na dinga zolayarsu da cewa ko wacce sai ta gaya mini sunan saurayinta. Muna cikin haka wayar da ke falo ta ɗauki ƙara, tana nuna mana alamun an bugo waya kenan. Mansura ce ta yi saurin zuwa ta ɗauka, cikin sakan ɗaya da kanga kan wayar a kunnenta na ga ta yi saurin durƙushewa ƙasa, sannan na ji tana gaishe da mai maganar. Yanda take yi tamkar tsaye take a gabansa, sai dai na ji ta ce, "To." Da sauri da sauri na ga ta iso gabana bayan ta ajiye kan wayar ta tsugunna tamkar tana neman in gafarta mata daga wani laifin da ta yi mini sannan ta yi magana. "Allah ya taimaki Gimbiya, Yarima ne ya ce ki ɗauki wayar hannunki." A take na ji gabana ya faɗi, wanda ya yi daidai da kallon agogon da ke manne a kusurwar falon. Ƙarfe tara saura mintuna sha takwas,nan na tunano gayyatar da aka yi mini ta zuwa cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau. Cikin ɗan gaggawa na nufi sama tun kafin na isa falon sama na ji wayar tana ta kukan kirana, na yi saurin gudu na isa, tare da saurin kanga wayar a kunnena. "Hey." Na faɗa cikin muryar da tafi kama da ta marar lafiya. "Na san kin gane na samu kaina cikin son ganin ki,shi yasa ki ke wahalar da ni." Shi ma tamkar ba shi da lafiya yake mayar mini da amsa. "Sorry." "Ina jiran ki." Bai jira na mayar da amsa ba na ji ya kashe. Na ƙurawa kan wayar ido, tamkar zan ga hoton Yarima a ciki, na yi murmushin da ya ratsa jijiyoyin jikina, sannan na miƙe. Ƙarfe tara daidai ina gaban madubina ina kallon jikina, riga da siket ne na atamfar Super Holland, ɗinkin wanda ya bi jikina ne, shi ne mai (shape) babu wani ƙwalliya a gaban ɗinkin sai dai buɗaɗɗan wuya ne mai zagaye. Sai kawai dogon zib tun daga saman wuya har izuwa bakin ƙugu, wanda makamin zuge shi,zamu iya cewa ya yi kama da ɗan ƙaramin zobe, shi kuwa siket ɗin irin ɗinkin nan wanda ƙarshensa buɗaɗɗe ne sosai. Takalman dana saka, basu da wani tsini sosai, mayafin jikina kuwa kalar takalman ne, wanda suka yi shige da ɗaya daga cikin ƙwalliyar atamfar wato ja, turaren (Glorious Lonkoom) shi na feshe jikina da shi, wanda wayar G.S.M ce mai kalar ja a hannuna. Na yi murmushi sannan na tambayi kaina, shin me yasa nake jin farin ciki a zuciyata? Na lumshe idanuwana haɗe da tunanin wai ga Yarima nan zai rungume ni ta bayana. Na buɗe ido da ɗan saurina har da ƴar ƙara haɗe da ɗan tsallena, tamkar da gaske, na yi dariyar da na ji tamkar yau ne ranar da aka yi mini wahayi da farin ciki, sannan na nufi gidan Yarima. Falon ƙasa na yi sallama na shiga, kafin in rufe baki mutane sun kai baƙwai suka zube a gabana suna kirari da gaisuwa a gare ni, na amsa masu cikin nuna nima fa ƴar mulki ce, kafin in ƙarasa wajensa,tuni an malala mini wata lallausar darduma a wata kujerar da ke kusa da shi da alama ta mulkinsa ce. Yarima kuwa yana ƙwance a gadon mulkinsa mai kama da katifa,ko in ce kujera mai hannuwa, amma mai faɗin gaske, ban da fitilu da ke zagaye da ita, ita kanta katifar mulkin sai ka tattaka hawa biyu sannan ka same shi ana uku ƙwance,ke nan kamar kana hawan matattakalar bene. Yanda yake a ƙwanciyar rigingine nan wayoyin hannu da na gida sun zagaye shi sun kai baƙwai, amma kai da ganinsa ka san hankalinsa ba ya a wajen mutanen da ke zagaye da shi, suna ta fadancinsu,su ma za su kai taƙwas, daga ƙwancen da yake kawai ya waigo da kansa ya kalleni. Hararar lumshe idanuwa ya yi mini,wacce zan iya cewa ta bayar da ma'anoni da dama, gaisuwa,kin mini laifi,ƙauna,son ganin ki nake,na ji daɗin zuwan ki. Cikin nuna ban fahimci mai yake ciki ba na ɗan ɓata fuska alamar na ji haushi,nan take na ga yana girgiza kansa, sannan ya juyo ya kalli mutanen da suka kasu gida biyu. Wasu a wajensa suna yi masa firfita da gyara shi, ban da kirari da suke yi masa. Wasu kuwa suna a kaina ni ma ana yi mini nawa,kallonsu kawai ya yi sai na ji suna cewa. "Mun bar ku lafiya, ƴaƴan mulki, waɗanda suka gaje shi, godiya muke." Kafin su ce sun yi gaisuwar nan da suke,ko in ce sallama,tuni wani dogari ya iso gabana da faranti a hannunsa lulluɓe da farin yanki,a take na fahimci komai wai in ina so inyi musu ƙyauta. Na ɗan sunkuyo kaɗan na ɗauki bandir uku na miƙawa na kusa da ni da hannu na yi masu inkiya da su raba. Ai kuwa na sha godiya da kirari irin na ƙwararrun dogarawa. Cikin mintuna uku falon ya koma shiru, daga ni sai Yarima da ke ƙwance, kamar mai jiran motar asibiti (Ambulance),ta zo ɗaukar shi. Mun samu mintuna biyu a haka, sannan na yi murmushi na ce a zuciyata, mulki sai mai shi, sai kuwa ɗan da ya gaje shi. ƘASAITA, sai Sarki, sai kuwa jinin da ya fito ta sarauta. Na girgiza kaina sannan na yi murmushi na miƙe tsaye na nufi inda yake ƙwance. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 6 Dole,in zamo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24