Chapter 10
Chapter 10
ƙasanshi, ta wani ɓangaren kamar yanda Aunty ta faɗa, matattakala biyu na hau, sannan na zauna gefe ɗaya. "Sorry." Na faɗa cikin sanyin murya. Ya juyo da fuska ya kalleni,kunyarsa tasa na sunkuyar da kaina, ina jin motsawarsa ashe matsowa ya yi ya kama yatsun hannuna ɗaya. "Yasmin kin firgita ni sosai,kin tayar mini da hankali,kin saka mini rashin walwala a jikina." Ya sumbaci tafin hannuna na ɗan yi saurin janyewa nuna alamar kunya, na ɗan juya kansa jin a daidai nan yana magana. "Yunwa nake ji, ki taimaka mini da abinci." Na sa tafin hannuna na ɗan ture shi. "Ba ƙya so?" "Tashi mu je ka ci abincin." Na faɗa cikin muryar sassarƙewa. Ina jinsa ya koma da baya ya ƙwanta da ƙarfi tare da ajiyar zuciya, na juya na kalleshi yana mayar da numfashi a hankali, ya juyo muka haɗa ido na yi saurin miƙewa, sai na ga ya yi murmushin kunya ta kama shi, shi ma sai ya miƙe. Alkyabbar da ke jikinsa ya ƙara gyarawa, sannan muka nufi wajen cin abinci, sai da muka isa sannan ya cire alkyabbar ya miƙo mini,na karɓa sannan na tafi ga ɗan ƙarfen da ake ajiyewa na rataye ta, ina juyowa na gan shi tsaye sai kallona yake,muna haɗa ido muka yi murmushi gaba ɗayanmu. "Zan tafi idan kana yawan kallona." "Dole ne in kalle ki Yasmin,saboda kin canja mini rayuwata gaba ɗaya,kin mayar da ni tamkar ba ni da jini a jikina." "Ka gani...." "Ki yi haƙuri ba zan daina ba fa." Na juya alamar zan tafi. "Zo, na daina." Ya ɗauke fuska ya zauna sosai na iso na tsugunna a gabansa domin in zuba masa abinci. Tuwon niƙaƙƙiyar shinkafa ne,miyar dagwargwajajjan naman kaza, wacce aka yi ta da agushi, ya yi kalar kore-kore da gani ya sha kori (curry),shi kuwa tuwon ya sha naɗi a leda tamkar a hotel, na zuba masa, sannan na buɗe ɗaya ƙwanon, farfesun dagwargwajajjiyar hanta ne, shi kuwa ɗayan farfesun kifi ne, wanda hausawa kan ce masa ragon ruwa, ga shi ya sha albasa mai lawashi a cikinsa, da gani an saka shi a injin ɗin zare ƙayar kifi,ko kuwa in ce injin ɗin sa ƙaya ta yi laushi. "Ke fa?" "Ni naci a gidana." Ya yi murmushi. "Sam ban amince ba,ni dai na san kunyata ki ke ji, amma tsaya ki ga yanda za'ayi." Ya miƙe tsaye a inda ni kuma dama a tsayen nake ya isa makunnan fitila ya kashe ta, dawowar da zai yi sai ya rungume ni a jikinsa, ya yi ajiyar zuciya. "Sorry, ban lura da ke ba." Ya faɗa cikin raɗa, sannan ni kuma na zame na zauna. Zaunawar da na yi tayi daidai da kamawar wata ƴar fitila mai duhuwa wacce haskenta kawai za ka gani, amma ba zakaga mutum ba sosai, yanda nake zaune nan haka ya zo ya zauna kusa da ni a hankali ya dinga lalubo bakina yana saka mini tuwon nan, shi ma a haka ya ci nasa. Idan na girgiza kaina, shi ma sai ya ce ya ƙoshi,ni kuwa na san Yarima yana tare da yunwa sosai, saboda tashin hankalin da ya saka kansa, na ganin zai rasa ni. Cin abincin da ya kamata ayi shi cikin mintuna sha biyar, sai ga mu mun ƙwashi awa ɗaya. Na gane haka ne a lokacin da na iso kicin domin ajiye ƙwanukan abincin da muka ci,ni kuwa na yi tsaye a kicin ɗin na rasa me ke damun jikina, saboda wasu abubuwa da nake jin suna yi mini yawo tamkar kiyashi na bi mini jiki,shin ko son kenan? Shin ko na kamu da ciwon son Yarima ne nima? Kamar yanda na ga duk ya yi laushi a kan ciwon da ya kama zuciyarsa da gangar jikinsa,wai shi ciwon so na. Motsin da naji yasa na yi saurin ci gaba da harhaɗa ƙwanuka tamkar dama aiki nake tun da na shigo. "Sannu da aiki." Na juyo na kalle shi ya jingina da gefen ƙofa, ya rungume hannayensa a ƙirjinsa, murmushi kawai na yi masa,a zuciyata na ce lallai Yarima yana son ƙananan kaya, saboda riga mai dogon hannu da take jikinsa wacce ya ɓallewa maɓallan gaba na rigar. "Ki bar shi, da akwai masu gyarawa." Na sunkuya wajen famfo na wanke hannuwana, sannan na iso inda yake tsaye ni ma na tsaya saboda ba hanyar wucewa, maimakon ya gafara in wuce sai na ga ya rakuɓe gefen ƙofa sosai, ma'ana in zo in wuce, wanda ya yi mini alamar da hannunsa ɗaya, duk da dama idanuwansa tsaye suke a kaina suna yi mini kallon kamun barewar damisa a jeji, ma'ana tamkar idanuwansa za su lumshe gaba ɗaya. A hankali na zo na raɓa zan wuce, sai da na shiga tsakiyarsa sai ya sa hannuwansa ya kare ni, wato ya saka ni tsakiya sai da ya lumshe ido ya buɗe ya ɗan girgiza kai alamar kana son faɗar wata magana, sannan ya yi magana. "Ina za ki?" "Kina da gidan da ya wuce nan?" "Eh." "Wanne kenan?" "Wanda iyayena suka saka ni a ciki." Ya ɗan juyar da kansa ya kai sau huɗu, sannan ya dawo da kallonsa gare ni. "Ina son da kiyi mini wani aiki." "Na me kuma?" "Mu je sama ki gan shi." "Dare fa ya yi, goma ta wuce." "Ƙuya kenan fa." Nayi murmushin kunya. "Na isa,mu je in yi maka ko na tafi kada inyi dare." "Matata na ce mini za tayi dare a wajena,Yasmin kenan." Ya faɗa a daidai lokacin da ya sauke hannuwansa na wuce. Sama na isa, wanda shi dama yana biye a bayana, kujerar da ke kusa da gado ita na zauna shi kuwa a zagayen gadon da ke tsakiyar ɗakinsa, ina kallo ya janyo durowar kusa da gadonsa ya ɗauko wata babbar ambulan mai fulawoyi ja, wanda ita kuma bulu ce mai haske (light blue), ya ɗago ya kalleni,ni kuwa dama shi nake kallo. "Zo ki gani." Na yi murmushin zuci na miƙe, saboda tunanin me Yarima ya mayar da ni,yarinya ko me? Na iso na zauna gefe ɗan nesa da shi ya miƙo mini na karɓa ina mai mayar da hankali a kan ambulan ɗin. "Buɗe mana." Ban ce komai ba na buɗe ta, litattafai ne guda biyu wanda yanayin hotan da ke jikinsu da sunansu ya nuna mini cewa su Nobel (Novel) ne, na ɗora su a cinyata, saboda jin da sauran wani a ciki,alawoyin chakuleti na ji a ciki (Chocolate), ina zarowa na ga an rubuta Bounty a jiki. Na ɗago na kalleshi wanda kallon yana nuna alamar tambaya. "Taimaka mini za ki yi ki karanta mini su, amma yau mu fara da ɗayan duk da na san da wuya mu yi ƙwata a yau, amma ƙila ma yi sati muna karantashi, chakulet kuwa matata na siyawa, saboda na san zata taya ta hira." Ya haye can ƙarshen gado ya ƙwanta irin ƙwanciyarsa da ya saba,wato rigingine, sannan ya yi filo da tafukan hannayensa, ya mayar da idanuwansa ya lumshe. Na girgiza kaina sannan nima na gyara sosai nasa fulalluka na tare bayana, sannan na soma karantawa. Ni kaina na san muryata ta yi daɗi a wajen karatun, na san kuma duk mai sauraren karatun zai ji daɗinsa, saboda dallah-dallah nake yinsa,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24