Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Kasaita Book 2 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yi dace da ke ƴa tagari. Ki yi haƙuri ki zauna da mijinki lafiya, duk abubuwan da suka faru a baya ya kamata a ce kun haƙura kun ajiye su gefe,kun mayar da su yarinta, wannan abu kuma da ya faru abu ne na al'adar sarautar gidan nan tun iyaye da kakanni. Hikimar yin shi kuwa shi ne hana rigima idan Allah ya ɗauki ran Sarki,a wancan zamanin,kin san kowacce masarauta a wancan zamanin da irin hikimar da ake amfani domin fitar da Magaji,wato wanda zai gaji sarauta. A zamanin da zaki ga wata masarautar su kan sa yaransu su yi tafiya mai nisa domin ɗauko wani abu ko samo wani abu. To su kuwa wannan masarautar ta haka suke ganewa. Ina son ki yi murna kuma ki godewa Allah da yasa ki ka samu kanki a wannan matsayi. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 10 Tsaya in baki wani labarin da ba wanda ya san shi daga ni sai Mai Martaba, sai kuwa ita wacce abin ya sama sai kuwa Allah. Kin ga wannan abin da ya faru da ke a yau, to shi ne ya haddasa tsana mai tsanani tsakanin Sarki da matarsa ta farko, Hajiya uwarsu Abdulrahman, da na taɓa ba ki labarinta. Mai martaba ya bani labari cewa, lokacin da aka kawo ta tana amarya ita ce ta dinga nuna masa ya zo gareta,kin san yanda auran sarauta yake da wuya a bar ka ka auri wacce ka ke so, sai dai a zaɓa maka. To wannan ne yasa ba so a tsakaninsu, lokacin wata ƴar barga yake so, wato irin ƴaƴan masu aikin gidansu, aka hana shi auranta aka aura masa Hajiya Asabe. Ranar da Allah yasa za su haɗu da ita a matsayin miji da mata, sai ga shi ya sameta ba yanda ake so ba, wato ta taɓa sanin wani bayan shi. Tun a daren ya kira jakadiya ya sanar da ita, jakadiya ita ta kawo shawarar a samo kaza a yanka ta,jininta a zuba shi a shinfiɗarsu, wannan dabara ita aka yi, balle a wancan lokacin jakadiyarsa mai himma ce da wayo, ita ta yi masa wannan dabarar har ya samu ya haye a matsayin zai gaji sarauta. Tun daga wannan lokacin ya tsani Hajiya Asabe, har ya zama yana zarginta da fita waje in ta fita unguwa. Ke a ƙarshe dai sai da suka rabu hankalinsa ya ƙwanta. Ke ki godewa Allah ko in ce mu godewa Allah, wallahi ni ma nan da ki ka gani sai da aka yi mini wannan taron,ki yi haƙuri ki zauna da mijinki lafiya. Mu dama tuni abin da muke son ji kenan, saboda duk wani masoyin Yarima zai so a ce ya ji wannan ranar, ta zo kuma yanda ake son ta. To ni zan koma sai kun zo mana sallama ko, Allah ya yi muku albarka, kira shi ki ce ni zan koma." Abin ka da falon sama muke dama sai kawai na shiga ɗaki, ina shiga ya ɗago kai ya kalleni daga inda yake ƙwance,bai tashi ba har na iso gabansa. "Mama na kira." Na samu na faɗa,a inda na juya na koma wajenta. Sallama kawai ta yi da mu ta yi tafiyarta,iyakata bakin ƙofar falo, Yarima kuwa shi ne ɗan doguwar rakiya. Kafin Yarima ya dawo ni kuwa har na saka rigar baccina na haye gadona, saboda ba zan iya cigaba da haɗa ido da Yarima ba. Ina kallon shigowarsa, ta ƙyallin idona ɗaya, ya zo ya tsaya a gabana kallona kawai ya dinga yi yana murmushi. Ya yi tsayin mintuna biyu a haka, sannan ya shige ciki, kenan ya koma ta bayana,ni ga shi babu damar in juya in kalli me zai yi ba. Ina jin shi ya shigo cikin bargon da nake ƙudundune sannan ya hayo ta saman jikina ya ɗauki makunnin kashe fitilar ɗakin. Me ya manta? Na faɗa a zuciyata, saboda jin ya sauka daga saman gadona,ƙyallin idona ɗaya na ƙara buɗewa a nan ne na ga ya isa ga ƙofa yasa makullintaa ya kulle, cikin bargon ya koma tare da kashe fitilar ɗakin gaba ɗayanta, ina jin shi ya zare ɗan abun ɗane gashin da na sa na ɗaure gashina (band) cikin ruwan sanyi na saukar da ajiyar zuciya jin ya sumbaci bayana, tare da rungume ni jikinsa ta bayana. "Na san kina ji na ki kayi shiru, because you hate me Yasmin,har abada ba zan taɓa yaudarar ki ba,sona,ƙaunata, mulkina,ƘASAITA, duk naki ne,in har babu ke a tare da ni na san zan iya zama ba ko ɗaya a cikin abubuwan da na lissafa,ni na san ƘASAITa ta biya ni, tunda ta hana mata da yawa yi wa rayuwata katsalandan. Ki yi tunani, da ni mutum ne mai sakin fuska da mata nawa ne zasu dinga neman cin fuskarki, saboda suna kishi da ke. Ke kaɗai na fara sakarwa fuskata, da jikina baki ɗaya, kuma na yi imanin ke ce ƙarshe. Please Yasmin ki saki jiki da ni saboda ke special ce a gare ni, kamar yanda sunanki ya ke special a wajen jama'a. Ki so ni,zaki sameni mai sauƙin kai, komai ki kaga na yi na mulki a baya, saboda tsare mutuncin kaina ne." Ya kama ni ya juyo ni a jikinsa sosai kumatuna ne ya ƙwanta a ƙirjinsa ya yi ɗan saurin ɗago kaina na san dalilin ɗaga ni haka. "What? What? Yasmin, still you hate me." Na koma na ƙwanta a ƙirjinsa mai ni'imtaccen gashi, ina jinsa ya yi ajiyar zuciya ya ƙara rungume ni gam a jikinsa. Gashin kaina yasa hannu yana ɗan shafa shi a fuskata, ban iya buɗe idanuwana ba, amma nasa hannuna na riƙo gashin tare da yin murmushina. "Zan je sallah ne masallaci ki tashi ki yi taki sallar, saboda yau zamu ɗan fita zuwa wani ɗan lokaci, amma ƙasar Greece za mu fara zuwa,a can nayi karatuna, sai in nuna miki wuraren dana sani, ragowar ƙasashe uku ke ce za ki zaɓa." "Ni ba zan je ba." Ya sa haƙoranshi ya cije laɓɓana duk biyun, har sai da na ɗan yi ƙara kaɗan, na samu na ƙwace na cusa fuskata a ƙirjinsa. "Zane ki zan yi da tsintsiyar ƙwaƙwa na ga alama." Nasa yatsuna na ɗan ja gashin da ke ƙwance a ƙirjinsa, yasa ƙara kaɗan tare da ƴar kokawar ƙwace jikinsa ya mirgina ya tashi yana dariya ya sunkuyo ya sumbaci kumatuna. "Zan rama ne, gudu nake kada na makara da kin faɗa." Ni kuwa na ƙudundune kaina a filo, ina ƴar dariyar murmushi ina jin shi har ya kammala alwalla ya fito daga banɗaki, saboda jan faɗa har da buɗe ƙafata ya yayyafa mini ruwa. "Tashi." Na yi saurin jan ƙafata shi kuwa ina jin dariyarsa a hankali har ya fice daga ɗakin. Fitarsa zan iya cewa jinkirin minti ɗaya na yi na miƙe da tsallen murna, na sauka daga gadona, jin ƙuguna ya ɗan amsa, shi ya tuna mini ashe fa ba na jin daɗin jikina, na yi murmushi na shige banɗaki tare da tunanin na zama ta Yarima Faisal. **** **** ***** Ƙasar Greece,nan muka sauka FIVE STAR HOTEL,shi ne masaukinmu, wanda ɗakinmu shi ne ɗaki na ɗari da goma sha biyu (112) , ya kama kuma hawa na uku

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});