Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Kasaita Book 2 Complete Hausa Novel 1,240 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ragowar ƙannansa ba,ni kaina sai da na zauna gidan sannan na gane da kaina. Amma Mama ta ce mini, Yarima ba shi ne ɗan Sarki na farko ba,yana da yayyansa biyu mace ce babbar gidan ƙwata-ƙwata Hajiya Asabe, sai ƙannanta Abdul Rahman, amma tun kafin sarki ya hau sarauta ya auri uwarsu Hajiya Hadiza, sun rabu tun shekaru da dama. Yanda ta ba ni labari ba ta san abin da ya haɗa su ba, amma Sarki baya son ko sunan yaran a ambata, ba ma uwarsu ba, wannan dalili ne ma yasa jama'a da dama sun yi zaton Yarima ne babban ɗan Sarki Jafar. Uwarsu Abdul Rahman tafiya ta yi da su hannunta tun suna ƙanana, sai dai in sun ga dama suna zuwa gaishe shi, shi ma sai a yi shekaru basu zo ba, yanda ta bani labarin, yanzun haka Hajiya Asabe tana Ibadan tana auran wani mai kuɗi Alhaji Alabi. Shi kuwa Abdul Rahman yana Scotland zaune da matarsa baturiya (Vivian), yanda Mama take nuna mini kamar Sarki ya yafe su ƙwata-ƙwata, kenan ya barwa uwarsu su, sai dai ta ce ya kan aika masu da kuɗin makaranta da na abinci da suna yara, yanzun kuwa ko maganarsu ma baya son a tayar. Asalinsu Mama kuma iyayenta ƴan barikin Ladi ta nan Jahar Plateau,tun da daɗewa a garin Jos,ƴan ƙauyukan garin ke zuwa karatu, wato Makarantar ƙwana ta gaba da Primary,anan suka haɗe da Sarki a lokacin bai ma hau gadon sarauta ba, daga baya ne ma da ya hau mulki ya ƙara auran Hajiya Kilishi. Yanzun haka iyayen Mama suna nan da ransu a garin Aboko, da sauran danginta. Yarima kuwa shi ne ɗan ta na farko, sai Salimat, sannan Idris, daga su kuwa ba ta ƙara ba. Hajiya Kilishi kuwa anan Jos ya aure ta,ɗiyar hakimin Bukuro ce ta nan ƙaramar hukumar Plateau. Saboda rashin ganin hanya a ranar da muka zo gaishe da iyayen Yarima, shi yasa ban gane cikin gari suke zaune ba,a unguwar Dogon Agogo,wai wannan rukunin da nake gani har wajen baƙwai a gidan Yarima,wai na farko fada ce in Sarki ya zo kenan dai gidansa ne na hutawa,ko kawo baƙi na musamman. Sai masallaci a liƙe da shi, ragowar rukunin kuwa kamar namu ne,gidana da na Yarima, sai na su Idris da Ahmad,wai in sun yi aure, amma kowanne da kalar yanda aka tsara nasa ginin, amma tsananin kowanne gida zuwa wani gida, sai an shiga mota,in ba motsa jini za'a yi ba, saboda ko da Asuba ko ragowar sallolin nan an kai Yarima a mota. *** **** **** Tsugunne muke gaban Sarki ni da Yarima a ƙaton falonsa, na cikin gida,kawunanmu kuwa a sunkuye suke da gani ka san gaban manya muke. "Yau ne matarka za ta koma gidanta wacce ta samu tsayin ƙwanaki arba'in da biyu a hannunmu, dalilin da sakacin da ka yi da ita har ta faɗa haɗarin saran maciji. Bayani ya same ni na irin zaman da ka yi da ita a baya, zaman ko in kula da banzatar da ita. Wannan dalili ne ma ya janyo mata faɗawa rayuwa ƙuntatacciya, na gode,ka yi mini daidai ashe ni ina taƙama da ina da ɗa mai biyayya, ashe ban sani ba,ƙarya zuciyata ke gaya mini. Ka bani mamaki,a ce ita mace na je na nemo auranta ga iyayenta, suka amince suka ba ka ita, alhalin ba ta san ka ba, kuma suna da wanda ke jiransu su aura masa ƴarsu, ita ma tana da wanda zuciyarta ke so, amma ta haƙura ta yi biyayya ga iyayenta, kai kuwa ban isa ba." "Baba...." Yarima ya faɗa cikin sanyin murya. "Kada ka ce mini komai, kai ne da bakin ka ka gaya mini da ka amince in zaɓa maka wacce na ga ta dace da kai, tun daga ranar na baza mutane a kan su gano mini matar da ta dace da ɗana wanda nake mugun ƙauna a zuciyata, Allah ya ba ni ya kuma ba da sa'ar aka samu ƴar gidan manyan mutane masu mutunci. Ka tuna,bakina da naka muka yi wannan maganar ba fa aike na yi maka ba,ka tuna,kiranka na yi ka faɗa mini wacce yarinya ka gani ta ƙwanta maka a yi maganar auranku,ka tuna, kai da bakinka ka ce mini babu. Yanzun na yanke hukunci zan raba auranku, amma na baka tsayin ƙwanaki biyar ka zo mini da rubutacciyar takardar sakinta...." "Baba...." "Bana son jin komai daga gare ka,ka bani haushi,ka ɓata mini raina matuƙa." Ya miƙe tsaye, "Ɗiyata ina ƙaunarki da ɗana, amma ki je kiyi haƙuri, sannan ki yafe ni da na sa aka raba ki da wanda ke son ki,saboda son kai irin nawa. Zan aiko a yi kiranki." Ya juya ya tafi. Yana ƙulewa a inda har ya ƙule, Yarima na Baba,Baba cikin girmamawa, amma bai ko juyo ba,ni kuwa na waigo a sanyaye na kalli Yarima inda ya koma ya ƙarasa zama a ƙasa. "Tashi mu tafi." Na faɗa cikin muryar da zata ƙara karyar da zuciya. "Kin ji abin da Sarki ya ce fa Yasmin." Na ɗan yi murmushin da ƙago shi kawai na yi. "Kana da magani?" Ya girgiza kai. Na miƙe na bar shi a wajen zaune,gudun kada ya karyar mini da zuciyata. Ina jiyo su daga falo,suna cikin ɗakin Mama yana gaya mata, amsar da ta bashi ce nima ta ɗan firgita ni. "Gara haka,ai ni har naji daɗi, tun da baka son ƴar mutane a dinga ajiyarta a gidanka,ƙwanaki nawa kuka ɗauka da ita ba ka ji kana son ta ba,sai yanzu....?" "Mama zan iya yi miki rantsuwa da Alƙur'ani akan ina son ta, Mama duk laifinta ne...." "Laifintan wa? Kusan kullum sai mun yi waya in har baka zo ba,in dinga ƙwatanta maka cewa don tana mace,kai ya kamata ka dinga shishshige mata,yau da gobe za ta saki jiki da kai." "Wallahi Mama, ina yi mata, ita da wanda take so,wai shi ANWAR." "Shi kenan ka ga yanzu ka yi wa kanka, ita kuwa tana da wani." "Mama yanzu ya zan yi? Wallahi ina son Yasmin,ni dama can ina son ta." "Ƙarya ka ke yi, da kana son ta da baka tsaya yi mata mulki da kuma ƘASAITA ba, haka ka ga muna zaune da mahaifinka? Mulkinsa da ƙasaitarsa a waje suke, sai kuwa idan ya shigo gida ya ga barorinsa, wannan dole ya yi,kana kallo wata rana da kansa zai leƙo ya kira wacce yake son yin magana da ita a cikinmu. Ko an ce maka jakadiyar da aka sa a tsakaninku, Addini ne ya shinfiɗa ta?" "Mama matsalar, Mama, Yasmin ba ta sona ƙwata-ƙwata,ni kawai ke sonta." "A yanzu ko kai ma?" "Mama ki tuna ranar da na fara ganinta daga can sai nan fa nazo na gaya miki na ga yarinyar da nake so,amma ban san ko ƴar waye ba, har ki ka ce sai in je in ta nema, wallahi Mama ita ce nake gaya miki, don dai haɗuwarmu ta zo ne da saɓani shi ya sanya...." "Saɓani ko dai ka nuna mata kai ka isa, dole ne ta ji tsoron zama da kai yanzun." "Mama duk ki bar wannan maganar,a yanzu na ajiye duk wata ƘASAITA in dai ina tare da Yasmin kamar yanda nake miki Mama." "Yanzun

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});