Chapter 21
Chapter 21
ya samu minti ɗaya da ƙwance mini,sannan na ji ya ce, "Open your eyes." Ina buɗewa sai na ga wasu abubuwa masu ƙyalli sun zubo da yawa, waɗanda suka hana ni kallon abin da ke gabana, can cikin mamakin da nake yi sai na ji tafi ya cika mini kunnuwana tare da kiran. "Happy birthday to you! Happy birthday to you Yasmin, Happy birthday to you." Can sai na ga kamar an yi sama da wani farin yanki sai kawai na ga hall (ɗakin taro), cike da mutane sun saka cake ɗin murna a gaba (Birthday cake) Na juyo na kalli Yarima irin kallon murna da mamaki, sannan na ce, "Thank you." A kunya ce. "Kin fi ƙarfin haka a gare ni." Sannan muka jero muka sauko ana ta tafin waƙar da suke yi tun farko. Kai tsaye wajen dogon cake mai hawa wajen shida muka tsaya a gabansa, sannan na ji waje ya yi shiru, can daga sama na ji ana cewa. "Muslim prayers." Sai na ji an karanta Fatiha, can kuma sai na ji an ce, "Christian prayers." Sai na ji suna yin addu'arsu da harshen Turanci, duk da ita kanta fatihar da harshen Turancin aka karanta ta. Ana shafawa ɗakin taron ya ɗauki ɗan ihun waƙar yanka cake ɗin murna, amma ta waƙar kiɗan Bature, sannan aka zo aka zagaye mu. Wani Bature ya tsaya gefenmu sai na ji ya ce, "Wannan ɗan Sarki ne a Nijeriya, wannan kuma matarsa ce." Haka na ji ya faɗa da harshen Turanci. Sai ya ɗauki wuƙa ya baiwa Yarima, sannan na ji ya ce, "Prince Faysal Jafar from Nigeria,zai yanka cake ya baiwa matarsa." Ya faɗa da harshen turanci, sai ya fara ƴar ƙirga, bayan Faysal ya saita wuƙar a jikin cake ɗin sai ya ce, "One, two, three." Yana faɗar muka fara hure wutar (Candle) ɗin da suke cin wuta a saman cake ɗin har izuwa biyu,yana cewa uku Yarima na Kamo hannuna muka datsa cake ɗin waje ya ɗauki tafi. Sannan Yarima ya yanko yasa mini a baki, a kunya ce na gutsura ni ma na yanko na sa masa shi ma ya gutsura sai ɗan tafi ihu ya tashi, shi kuwa Yarima har da saurin rungume ni. Kai rayuwar Turawa na bani sha'awa, amma iyakacinta kenan sha'awar, tunda ba Addini a tare da su,daga nan sai na ji kiɗa ya canja, cikin ƙanƙanin lokaci na ga suna kama junansu namiji da mace suna rawa suna bin kiɗan a hankali. Yarima ya miƙo min hannu ni dai na san ban iya ba, na girgiza kaina, "No,taho." Na ɗan maƙale ya janyo ni jikinsa. "Kalli ƙafafunsu." Ya raɗa mini a kunne na tsaya na kalla. "Ke ma haka za ki dinga yi." Ni dai na san kunya zan ba shi sai na ce kunya nake ji, ya dinga sani dole ni kuwa na ƙiya, ƙarshe wata Baturiya ta miƙo masa hannu sai ya sake ni ya kamata ya ci gaba da rawarsu. Ni kuwa ina tsaye ina kallonsu ganin ta ƙwanta a kafaɗarsa yasa na ji wani ɗan abu ya dakar mini zuciya,wai a take sai na ji nayi tunanin ko dai irin ƴan matan da yake tare da su ne a nan,nan take na ji raina ya ɓaci, idona kuwa ya kasa ɗaukewa daga wajensu. Can na ga ya ɗago yana ɗan waigen nema na, ya ɗago mini hannu sai kawai na ji na harare shi na juya, sai na ji na rasa inda zan nufa ina tunanin in tafi ɗaki sai na ji ya ruƙo hannuna ta baya ya rungume ni, tare da turo haɓarsa a jikin kafaɗata, sai na ji ya cigaba da rawa da ni tamkar muna rawar tare. "Sorry my darling,kin san su al'adarsu ce." "Kai kuma Addininka ne.?" "Kai, to fa,ki yi haƙuri na yi kuskure babba,ƙato." Sai kawai muka ji kiɗa ya tsaya wajen ya ɗan ɗauki tafi. Daga nan sai na ga wannan dai Baturan ya ɗauki bututun magana (Macrophone) yana cewa duk su tsaya inda suke za'a gabatar da kowa, ɗaya bayan ɗaya ya dinga gaya mini sunayensu,su al'adarsu shi ne a gaisa ko a ɗan rungumi juna, amma mai jawabi ya gaya musu mu haramun ne tun farko ma saboda haka sai dai a ɗaga hannu in wuce. Sannan suka ƙara gabatar da ni,nima da bada ɗan guntun tarihina ga shi duk wanda na zo kanshi sai ya ba ni ƙyauta dama wata mace na biye a bayana da irin kayan ma'aikatan hotel ɗin in aka ba ni in miƙa mata. Wasu har da ƴar guntuwar fulawa wasu doguwar fulawa, wasu mai yawa, wacce take naɗe a cikin leda, wasu ƙwalaye nannaɗe da ledar naɗe ƙyauta (Wrapping sheet), daga nan kuma aka bayar da umarnin a tafi ɗakin cin abinci, gaba ɗaya muka nufi can. Waje ne shi ma ƙaton gaske, amma gaba ɗayansa wani tebiri ne zagaye da shi mai kamar an ajiye doguwar gwanda, wato ba zagaye yake ba kamar ƙarfen kuɗi zagaye yake amma kamar Oval shape. Kowa ya ja kujera ya zauna,mu kuwa muka zauna ƙarshen tsinin tebirin kenan kowa mu yake kallo, duk yawan mutanen nan kuwa kamar an ƙirga su kowa ya samu wajan zama,dama kafin mu isa an gama shirya komai kowa an ɗiga masa lemun ruwan nan nasu,rabin kofi,mukaɗai aka ajiyewa wata doguwar ƙwalba an rubuta concentrated sof drinks. Ana ci ana yiwa juna tsiya, daga wannan ya ce mini shi ya koyawa Yarima magana a ƙwashe da dariya, sai wancan ya ce shi ya koya masa cin abincinsu, suka dinga hirar makaranta, tsiya dai kala-kala sun yi wa juna,anan kuma suke yaba masa da iya zaɓen mata,wai har cewa suke aƙwai mata masu ƙyau a Nijeriya?. Nan na ga ashe idan aka yi Birthday yanka cake ɗin ake ashe a baiwa kowa, saboda na gan shi a ɗan faranti gaban kowa, da gani kuma yanka shi aka yi, tabbas na ga yanda turawa ke rayuwa, dole Yarima ya zama ɗan rayuwa,ni har kunya na dinga ji idan na hango wasu na tsotsar bakin juna,ko ƴar soyayyarsu, ga shi a gaban kowa ma yi suke ba wanda ya damu da wani, wani lokacin ma Yarima ke taɓo ni in gani sai in sha masa kunu. Ba mu tashi ba sai wajen ƙarfe uku na darensu wanda sai da muka zo ɗaki ma na ga dare ya yi, kafin a gama shigowa da kayan da aka ba ni ƙyaututtuka na cewa Yarima zan ɗan shiga ruwan ɗumi saboda na gaji da yawa, shi kuwa har da yi mini kashedin in na fito shi zai zaɓa mini kayan baccin da zan saka, na bishi da to. Ya koma falo saboda tsayawa ya ga masu aikin hotel ɗin sun gama shigo da kayan duka. Ban wani daɗe ba ganin dare ya yi, ga shi idanuwana cike suke da bacci, saboda haka ban fi mintuna biyar ba, ina fitowa tun daga ɗaki na ɗan ji tashin muryar Yarima kaɗan kaɗan, duk da dama shi ba mai sakin murya ba ne ba,ko waya yake yi za kaga kamar ba a jin abin da yake cewa, amma yau nayi mamakin jiyo muryarsa. Na buɗe durowa na ƙwaso rigunan bacci uku, na taho da su domin nuna masa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24