Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Kasaita Book 2 Complete Hausa Novel 1,220 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

in nufi ƙofar dakinta ba, har na zauna na ji ta ce, "Shiga ciki mana ki zauna man baƙi sun yi yawa, balle ma yau juma'a." Na ce to, tare da saurin tashina. Amma ina shiga sai na ga Yarima ya juyo da kansa ya kalleni ya mayar gefe ɗaya, na isa bakin gadon a daidai lokacin da nake zaro takardar da Aunty Salwa ta bayar in kawo masa. "Gashi in ji Aunty." Ya juyo ya kalleni ya lumshe idanuwansa kamar wanda ake ƙoƙarin ƙara masa ruwan ledar asibiti, domin ceto ransa daga ciwon amai da gudawa da ya yi masa mummunan kamu. To haka na ga Yarima na buɗe idanuwa da ƙyar. Ya zaro hannu tamkar hannun ya yi masa nauyin ɗagawa ni kuwa na ɗora masa takardar a kai, madadin in zauna sai na dawo falo na biyun Hajiya na zauna saboda ba zan iya zama a wajensa ba...... Maganar da Sarki ya fara ita ta katse mini tunanin da na tafi, wanda a cikin mintuna biyar kacal na yi shi. "Yau ne ranar da muka yi alƙawari da kai zaka zo mini da abin da na umarce ka, ina jiranka." Yanda na ji cikin naman jikina na rawa haka kuwa na tabbatar Yarima na cikin halin da ya fi nawa, da jin maganar da Yarima yake yi,ka san a tsorace,a firgice,a nadamance da kuma karfin hali irin na maza yake yin ta. Bayan ya miƙe da ƙyar ya koma can kusa da Sarki. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 5 "Baba ka yi mini afuwa a kan abin da na aikata maka na rashin ƙyautatawa,a baya na yi alƙawarin ba za ka ƙara kama ni da wani laifi ba na rashin ƙyautatawa ba." Sai na ji ya rage sautin maganar ta juya izuwa sanyi da rawar murya. "Ba..ba yan...zun ina son abin da ka ke so, zan iya zama na har abada da abin da ka ke so." Ya yi shiru. "Yanzun me ka ke son inyi maka kuma? Bacin ka kunyata ni ka tozarta ni a idon jama'a." Ina kallo ta wutsiyar idanuwana ya ja jikinsa ya matsa sosai kusa da ƙafafuwan Sarki. "Baba ka yi mini hukuncin duk da ka ga ya dace da ni, wallahi zan ɗauka matsawar dai yin hakan zai huce zuciyarka zai saka ka yafe mini. "Ka zaɓi ɗaya cikin abu biyun nan,auranka ko sarauta." "Baba duk wanda ka zaɓar mini ina so." "In zaɓa maka ka ƙara yi mini yanda ka ga dama." "Baba ka yi haƙuri, wallahi kuskure ne,ba zan ƙara ba har abada." "Koma ka zauna, zan yi tunani a kan ka, ke kuma ki gaya mini gaskiya zaki iya zama da shi ko kuwa?" "Duk hukuncin da ka yanke ya yi mini nima." "Tashi je ki ciki." "Na gode." Na miƙe a sanyaye na nufi ciki. Tsayin mintuna arba'in Yarima ya yi shi da Mai Martaba, amma ni ina ƙwance saman lanƙwasashshiyar kujerar Mama, na yi lamo alamar bacci nake yi, ina ji ya shigo suka shiga ƙuryar ɗaki da Mama sun ɗauki mintuna sun kai ashirin sannan suka fito, ina jin shi ya yi sallama ya fita. Bayan sallar la'asar ne,Mai Martaba Sarki yasa aka kira ni zuwa fadarsa ta cikin gida, zan iya kiran lokacin da huɗu da rabi na yamma,ni da Mama muka shiga fadar wacce ita ƴar rakiya ce, wani sanyin daɗi na ji ya sauka a zuciyata,a lokacin da Mai Martaba ya ce Mama ta zauna ita ma. Ba mu fi minti biyu da zama ba sai ga Hajiya Kilishi ta shigo. A nan Sarki ya umurce ta da ta zauna, wanda dama alamar da ta nuna Sarkin ne ya aika a kira ta. Maganganu, misalai,nasihun da suka yi mini yasa a take na ji zuciyata ta karaya a kan duk wani abu da na ƙudura a kan Yarima na game da wahalar da shi. Lallai Yarima ya samu yabo a wajen mahaifansa, da kishiyar Mama, Hajiya Kilishi, ta faɗi irin halayyarsa da suke ji, ita ma, sai na dinga jinsa a zuciyata a take kuma na tunano kalaman Aunty Salwa waɗanda ta karantar da ni tsantsar so kuma me ye shi da tafiyar da wanda ake so. Na dawo hayyacina lokacin da na ji Mai Martaba ya ce, "Ƴata ina fatan za ki gafartawa mijinkin abubuwan da ya yi miki a baya, na rashin ƙyautatawa, saboda ya yi nadama ya nuna ba zai sake ƙwatanta miki su ba, ya nuna mini yana son matarsa." Yabo, nasiha da maganganun da Mai Martaba da iyalansa suka yi mini shi ya sanyayar mini da jikina, sannan Sarki ya yi mini alƙawarin yi wa Yarima hukunci, matsawar bai gyara halayyarsa ba, ya tabbatar mini da sati ɗaya ya bani idan har na ga ba daidai ba,in sanar da shi. Irin maganganun mutane da suka yi mini sun sa na ji alamar ɗan ɗigon wani abu a zuciyata, wanda na tuno da Aunty ta ce wai shi ne alamomin so. Ƙarfe shida saura mintuna goma sha baƙwai motocin ayarina suka shiga get ɗin gidan Yarima,wai sai na ji na tsinci kaina cikin wani irin nishaɗin farin ciki. Mu ma muka sauka inda ake ajiye motocin gidana. Yarima na hango a tsaye ya jingina da ɗaya daga cikin ragowar motocin da ke ajiye a rumfar ajiye motocin. Dukkan hannayensa ya saka su a aljihunsa ƙafafuwansa kuwa ya harɗe su a waje ɗaya, tabbas sai na ga ya ƙara yi mini ƙyau,ko kuwa don baƙar T.Shirt ɗin da ke jikinsa ce ta ƙara haska shi dama abu ga farar fata. Amma yanayinsa ya nuna mini da ganinsa cikin ɗan ruɗani yake, saboda yana hango motocina sai na ga ya yi saurin miƙewa tsaye sosai. Murmushin da nake yi kuwa,ni na san ya shiga har zuciyata, motocin na tsayawa shi ma na ga ya ɗan taho alamar zai iso ga motata, ganin an buɗe mini na fito shi ya sa naga yayi tsaye cak, tare da mayar da ajiyar zuciyar da ta fito fili, wanda ya yi ta cikin lumshe idanuwansa duk biyu. A hankali na ga ya zaro hannu ɗaya daga cikin aljihunsa ya shafi gashin kansa da shi, sannan na ga ya buɗe idanuwansa ya ɗan ɗaga su kaɗan ya kallo ni. Ni kuwa tuni har na kusa zuwa inda yake a tsaye, saboda ita ce hanyar da zan bi in shiga cikin gidana,ni kaina na san na canja tafiya, amma wani abin ban mamakin da na yi shi ne ina isa inda yake tsaye sai na ji ba zan iya yi masa magana ba balle har ta kai ni ga tsayawa wajensa. Sai dai kawai na yi murmushi na raɓa ta gefensa na wuce. "Kin tayar mini da hankalina,kin daɗe sosai." Maganar da na ji ya yi daidai lokacin da na zo zan wuce ta kusa da shi, na ɗan juyo da kaina na ɗan kaɗa idanuwana tare da yin murmushin da na san ya ƙara bayyanar mini da ƙyan fuskata,ƴar lotsawar gefen kumatuna ta bayyana a fili (Dimple), wacce na tabbatar ita ce sirrin fuskata. Na juya na nufi gidana a inda ina shiga falo wayar hannuna na yin ƙara, Yarima na ga an rubuta tare da lambarsa na yi murmushi na kanga

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});