Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Kasaita Book 2 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na zo na ƙara kama shi,a taƙaice dai ban ƙara sanin abubuwan da na dinga faɗa ba har aka kawo ɗan wani gado aka ɗora shi, sannan aka tambaye ni lambar ɗakinmu da ƙyar na iya faɗa,saman gado aka ƙwantar da shi na warware bargo na rufa masa, sannan na ga an yi masa wata allura a jijiya, cikin sakan biyu na ji ya yi wani tari, na ƙara riƙe hannunsa gam, cewa nake. "Tashi! Tashi!! Tashi!!! Yarima kada ka mutu." Sun gaya mini da harshen Turanci, zai tashi amma in dinga murza tafin hannunsa, da ƙyar na amsa da to. Sannan duk suka fita na kuwa dage goga hannuwansa duk biyun in na yi wa ɗaya in saki in kama ɗaya,kai sai gani har da busa bakinsa,ni sam na ma manta da wani haɗa baki muke yi da shi, wani ihu bayan hari zan ce, saboda wai sai a yanzun na ji ina mugun son Yarima, amma kuma ga shi a saman gado ya zame min ƙila wa ƙala. Na samu wajen minti talatin a haka, wanda hakan yasa na ji na karaya, sai kawai na ƙwanta saman ƙirjinsa na dinga kuka. Kuka mai tsananin gaske, amma ba wanda ake ihu ba, wanda gangar jikinka duka ke motsawa. Sama da mintuna ashirin ina haka wanda tuni har tunanina ya bani in bugawa Aunty waya in ce a zo a tafi da mu. Hannu na ji an sa an shafi gashin kaina ɗan motsi da numfashi su suka sa na yi saurin ɗaga kaina saboda in ga mai taɓa mini gashina. Yarima ne ke kallona yana murmushi, na yi wata sassanyar ajiyar zuciya na dinga murmushin daɗi don ma ina jin kunyarsa da tuni na yi tsalle. Na tashi da sauri na dawo saman gadon na faɗa jikinsa ya mayar da hannuwansa ya rungume ni ina jin shi yana ta shafa gashin kaina, alamar lallashi ina jinsa yana ƙoƙarin ya ɗago ni amma na rungume shi tamau, ina jinsa ya faɗi kalmomin nan da harshen Turanci. "Yasmin do you love me now? Zaki iya sakin jiki da ni?" Na ɗaga kaina wanda ke ƙwance a tsokar naman kafaɗarsa. Tabbas murnar Yarima ta fito fili,dana amsa masa ina son shi, ya ɗauke ni baki ɗaya ya ɗora ni a gadon da yake ƙwance, ya mayar da ni ya ƙwantar a ƙirjinsa ya janyo bargo ya lulluɓe mu a ciki, fuskokinmu kawai ke waje, na ɗago na ce masa. "Ka samu sauƙi?" Ya yi murmushin da yasa na ji sabuwar kunyarsa ta dirar mini sannan ya ɗaga kai alamar eh, wanda jin ɗaga kan kawai nayi saboda ni tuni na mayar da kaina a ƙirjinsa na ƙwantar. Lallai yanzu zuciyata da gangar jikina sun amince mini da ina son Yarima,su ma kansu son Yarima ya cika su dama. Na yi sauri na ɗan yi alamar zan tashi ya ruƙo gashina ta bayana, na juyo da sauri har da ƴar ƙara da ido da kai ya tambaye ni ina zani? Na sunkuyar da kaina ina murmushin da yake fita tare da ƴan ragowar hawayen idanuwana. "Magani zan ɗauko maka, likita ne ya ce da ka tashi na baka." Da kai ya nuna mini cewa inje na ɗauko, ina murmushin mamaki na cikin zuciya kenan bai fito fili ba, saboda mamakin yanda Yarima ya ƙware da maganar kai ko da yake ba mamaki idan na yi la'akari da farkon haɗuwata da shi yanda ya yi wa dogarawansa magana da gilashin hannunsa. Bayan na kama shi ya tashi zaune na taimaka masa na jingina shi jikin kan gado wanda nasa filo a bayansa sannan na zauna kusa da shi na miƙa masa maganin da ruwa a kofi, maganin ƙwaya ɗaya ne ɗan ƙarami, sannan na ƙara janyo kujerar da na ɗora ɗan farantin da kofin maganin na ajiye kofin sannan na miƙa masa kofin ruwan madara ya shanye. Saboda magriba ta kawo jiki,in na yi la'akari kamar a ce ƙarfe shida na Nigeriya kenan, wannan yasa na ce ya yi ƙoƙari ya je ya shiga ruwan ɗumi a banɗaki ko ya samu ƙarfin jikinsa sosai,bai yi mini gardama ba ya miƙe abinka ga namiji sai na ga baya ko irin ɗan tangaɗin nan na marasa lafiya. Ina zaune ni kuwa na rabka uban tagumi a gefen gado ina jiran ya fito, wanda tuni na tafi duniyar tunanina, na da Yarima ya mutu da ya zan yi? Ba don komai ba sai don yanda zuciyata ta fara nutsuwa wajen son zama da shi a matsayin mijin aurena,wai don shirme sai na ji hawaye sun taho na samu na lumshe idanuwana su kuwa suka ci gaba da gangarowa. Ban ji fitowarsa ba, saboda idanuwana a lumshe suke, kuma linzamin tunanina ya canja salo ya koma tunanin abubuwan son da Yarima ya nuna min a fili, na tuna ranar da ya mallake ni a matsayin matarsa irin nuna so da ƙaunar da ya yi mini a wannan daren ƙwaya ɗaya cal. Jin an sumbaci laɓɓan bakina shi yasa na dawo daga duniyar tunanin da na tafi, na buɗe lumsassun idanuwana sai na ga Yarima tsaye a kaina, na yi saurin ƙwantar da kaina a cinyata na ce, "Kai Yarima." Cikin kunnena ya ce, "Ke Yasmin me ye.?" Na ɗaga ɗanyatsa na nuna shi, "Me ye,tawul, Yasmin sai in ƙi ɗauro tawul ni da matata ni ne fa kawai a ɗakin" Da jin yanda sautin maganar ke fita ka san Yarima bai saba da yawan magana ba, saboda cikin nutsuwa yake yin ta. "Ki ɗago Yasmin na zama naki fa." Na girgiza kaina. "Sai kasa riga." Ina jin sa ya zauna dab da ni tabbas na ji sunkuyowarsa daidai da kunnena, saboda jin hucin numfashinsa, madadin ya yi magana sai dai kawai na ji ya hura kunnena,tsigar naman jikina na ji ta yamutsa, na rasa ya zan yi sai dai kawai na koma gado na ƙwanta a ƙudundune. Haɗani ya yi ya rungume a ƙirjinsa, amma ta bayana, kalaman da suke fita daga bakinsa su suka sakani na ji ɗakin na juyawa da gadon da nake ƙwance, jin ya ƙara hura mini saitin ƙofar kunnena yasa na mirgina ɗaya kusa da shi na samu na miƙe na gudu, na shiga banɗaki, saboda na san nan kaɗai ne in na shiga na tsira, shi ma idan na kulle saboda ƙaton falo ne da ɗaki ɗaya kawai su ne ɗakunan hotel ɗin. Na kulle ƙofar, amma sai na ji na jingina da ita tare da sulalewa ƙasa na zauna, kai sai na ji ina jin kunya ni kaɗai a banɗaki, na ƙudundune kaina jikin cinyata, na dinga murmushin da zan iya kiranshi na daɗi,wai don tsananin shirme irin nawa da na ɗaga fuskata sai in mayar wai kunya nake ji. Sai da na ƙwashi wajen mintuna sha uku a haka, sannan na yi sauri na miƙe tsaye saboda tunanin da na ji ya faɗo mini a take,shi ne sallah na san bai fi sauran mintuna a kira sallah ba,ko kuwa in ce lokacin sallah ya yi tun da garin arnaku muke balle mu samu kunnuwanmu da jin kiran Sallah. Na saɓule kayan dukkansu a gaban ƙaton madubinsu na banɗaki na kalli kaina tas na yi murmushi ganin ba ni da ko

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});